MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Murmushi kawai Kaka yayi yace, “komai na ta irin na mahaifiyar ta Allah ya albarkaci rayuwar ku baki ɗaya”……
*_SAFNAH ALIYU JAWABI_* 08136476004
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_
3️⃣1️⃣
_*Do yourself a favour. Surround yourself with those who speak of visions, ideas, goals, growth. Not those who sit and gossip about others. And if you do find yourself in that situation, excuse yourself and walk away. The game ends when you choose to leave such a gathering.*_
________Murmushi kawai Ka’ka Yayi shima ya shige ɗakin sa, tun daga wannan rana shaƙuwa mai ƙarfi ya shiga tsakanin su, a koda yaushe burin ta bai wuce ganin ta zaune kusa dashi suna hiran su ba, hira irin ta zuciya da zuciya, sosai yake jin babu daɗi idan har bata kusa da shi, saidai kuma hankalin sa yaƙi kwanciya dan kuwa daidai da minti ɗaya bai taɓa dai na addu’ar baiyanar wacce yake mafarki da ita ba, duk da kuwa yana samun kwanciyar hankali da sallama a duk lokacin da *Ummi* take kusa dashi.
Yau ma kamar kullum mafarkin ta yake ciki yanayi na jin daɗi da annashuwa take masa magana”Sahibi na shin baka jin yanda bugun zuciya ta take ƙaruwa a duk lokacin da kake tare dani? ” Murmushi yayi yana cewa,”Tabbas ina ji ina jin yanayi mai daɗi ta yanda sam ba zan iya misaltuwa ba, dake kawai nake so na ƙarasa rayuwa ta”.
“Shin ka ɗauki alƙawarin zama dani babu gudu babu ja da baya”.?
“Nayi alƙawari zanyi rayuwa dake a cikin daɗi ko akasanin hakan, dake kaɗai zan rayuwa ina mai tabbatar miki rayuwa ta bata da wani amfani idan babu ke acikin ta, ina mattukar ƙaunar ki nayi kukan zuci nayi ciwo naji kuncin rashin bai yanar hhhhki a gare ni,shin sai yaushe zaki zo gare ni”?
Murmushi tayi tace”Nan bada jimawa ba zanzo zanzo gare ka muradin rai na”.
“Yanzu tafiya zakiyi ki barni?” Dan Allah karki tafi karki tafi ki tsaya kece rayuwa ta”.
Cikin wani irin ƙunci da ɓacin rai ta kira sunan sa cikin kakkausar murya mai nuni da tsantsar ɓacin rai da baƙin ciki, “Yaya *Musaddam* a firgice ya farka yana share gumin fuskar sa kallon ta yayi yana mamakin lokacin da bacci yayi masa wannan shimmatar haka. ita kuwa *Ummi* suman tsaye tayi tsabar shiga ruɗani shin farin ciki zatayi ganin ya samu lafiya kuma yau maganar sa raɗau kamar yanda yake ada? Ko kuwa baƙin cikin jin kalaman sa akan wannan budurwar tasa za tayi”.
Share hawanyan ta tayi yace,”Alhamdullah Yaya *Musaddam* ka samu lafiya cikin yardar Allah “.
Sauke ajiyar zuciya yayi dan gabaki ɗaya ya kasa fahimtar yanayin ta, buɗe baki yayi da kalmar “Allahu Akbar alhamdullahi Allah”.
Murmushi mai tsada ya sakar mata wanda zai da taji tsigar jikinta ya bada yarrrrr, da gudu ta shige gida tana kuka sam ji tayi ba zata iya riƙe kukan ta ba, “innalillahi wa inna ilaihi raju’un ashe Yaya*Musaddam* yana da budurwar da yake so”.?
” Nashiga uku na shikenan buri na ba zai cika ba? Allah ka dubi wannan baiwar take wacce bata san komai ba sai bauta agare ka, Allah nafi kowa sanin cewa kusancin ka dani yafi kusancin dake tsakanin wuya na da maƙoshi na, saboda haka babu wanda yafi dacewa na kai sa kuka na sai kai Allah, kana ji na kuma kana gani na ka zaɓa min abinda yafi zama alkairi a cikin rayuwa ta. kuka take mai tsoma zuciya, jin sallamar Ka’kar ta yasa tayi saurin goge hawayan ta tana tsokala hannu a ido alamar ƙoƙarin cire abinda ya faɗa mata, murmushi kawai tayi tace,”Halan kin daina ganin gari ne tun yanzu mu san abin yi”.?
Cike da shagwaɓa ta fara bubbuga kafar ta a ƙasa tana cewa,”Ni dai wallàhi tafiya ta zanyi ma na bar garin nan tunda mugun alkaba’i kuke min ke da wannan tsohon mijin na ki”.
” A a rufa min asiri bani na kar zomon ba rataya aka bani,wasa wasa *Ummi* kuka take sosai harda ajiyar zuciya haka yasa ta karasa gun ta janyo ta jikinta tayi tana bubbuga bayan ta cewa take,”Ka’ka komai ya kare bani da wani sauran farin ciki, bani da sauran kuzari naji ina ma ina ma..cikin sauri ta sa hannu ta rufe mata baki tana cewa,”duk da kin ɓoye min abinda ke damun ki sam ba zan matsa ba amma zanyi miki fatan alkairi Aduk abinda kika saka gaba, ki kaiwa Allah kukan ki ina da tabbacin zai magance miki komai cikin sauki kinji”?
Share hawayan ta tayi tace,”in sha Allah komai zai wuce na haƙura da koma menene, amma dan Allah Ka’ka ina so in tafi gida ɗumin jikin Umma shine kawai zai sanyaya ruhi na”.
Daƙuwa tayi mata cikin wasa tana cewa,”Au shine kuma kika zo kika wani rungume ni bayan kin san kina da uwa, kuji min ja’irar yarinya”.
“To to ai dama bani bace na jawo ki kece kika jawo ni kawai dan kina so kiji laushin fatar jikina wanda babu ko ɗigon tabo, ba irin na mijin ki ba wanda tuni ya jame ya yanƙwane”.
Gorar dake hannun ta ta jefe ta dashi tana cewa,”kai wannan yariya gara ma ki tafi mu huta da wannan jarabar ta ki”.
********
Kukan da take sosai yaji babu daɗi duk da kuwa yau kamata yayi ya zama ranar farin ciki a gare shi ,amma ganin ta cikin wannan hali sosai ya saka shi a damuwa, “to Menene kuma na kuka bayan itace mutum na farko daya dace ace tayi farin cikin gani na cikin wannan halin na samun lafiya”?
Ganin babu mai bashi wannan amsar yasa yayi shiru yana jiran dawowar faruq dan kuwa tun da ya fita Masallaci bai dawo ba,Ka’ka kuma yana bacci .
Koda Ka’ka ya farka sosai yayi farin cikin ganin *Musaddam* yana magana bakin sa raɗau suna hira da Faruq saidai kallo ɗaya zaka masa ka fahimci ba acikin natsuwar sa yake ba.
“Alhamdullahi Alhamdullahi Alhamdullahi Ka’ka yayi Sannan ya samu guri ya zauna hannun sa riƙe da gora cike da ruwa,kallon sa yayi yace,”yanzu ya kake jin ƙarfin jikin na ka”?
Da murmushi akan fuskar sa yace”alhamdullahi babu abinda zance ga Allah sai godiya”.
“Shin ina zaka iya tuna abinda ya faru dakai a wannan rana da har yayi sanadiyar shigan ka cikin wannan hali”.?
Sunkuyar da kansa yayi yana nazari can ya miƙe a razane yane cewa,”Wallàhi itace itace na gani da ido na tana saka abubuwa a cikin toilet ɗi na, itace take fesa abubuwa a cikin kaya na wallàhi bazan barki ba sai na kashe ki, da kyar aka samu Faruq ya zaunar dashi Ka’ka ya watse masa wanna ruwan goron,kan ka ce me tuni har ya bingere, hamdala Kaka yayi yana cewa,”Tom alhamdullah mun samo bakin zaran alamu sun nuna akwai abubuwa da aka binne cikin wannan gida kuma aka saka cikin ɗakin sa, har ma kuma da kayan sa, idan kuwa haka ne dole akwai buƙatar komawa wannan gida a haka lungu da sako na gidan Sannan a firfitar da komai na cikin ɗakin idan da hali wannan makewayar da yake magana a yashe ta”.
Sauke ajiyar zuciya Faruq yayi yace,”In sha Allah haka za’ayi Ka’ka tunda akwai sauran lokaci har yanzu zan iya tafiya ai,caraf sai ganin ta kawai sukayi a gaban su tana cewa,”nima zan tafi Yaya Faruq akwai abinda nake so nayi a gidan nima,”.