MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Da kamar ya hana ta kome ya tuna kuma yace,”shikenan ki shirya dan babu ɓata lokaci zamu tafi”.
Cikin sauri ta koma ta ɗauko hijabin ta tana sakin ajiyar zuciya kallon ta kawai Ka’ka yayi cikin zuciyar sa kuwa cewa yake,”Allah kai ne kawai kasan ajiyar da kayi da kuma baiwar daka aje a jikinta wanda ka barwa kanka sa ni game da wannan yarinya, tunawa yayi da mafarkin da yayi jiya wai ta zo masa cikin wani irin suffa mai kyawun gani take faɗa masa cewa tabbas akwai abinda aka binne cikin wannan gida wanda dole akwai bukatar a cire shi hakan ne kawai mafita a gare su”.
Suna tafiya ya tashi ya shige ɗakin sa yana tunanin wannan al’amari………
_Page na gaba yana zuwa nan da awa ɗaya in sha Allah_
08136746004 Safnah Aliyu jawabi
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga marubuci Musaddam Idiriss Musa_
_*Be careful how you treat people. The tables always turn. The Almighty will see to it. Be careful who you ignore when you’re at the top. Some choose to treat people any which way that pleases them. Don’t! It will come back to you. You’ll be made to eat humble pie sooner or later!*_
___________Zaune take tayi shirin ta tsaf cikin wani leshi ja duk ya ƙoɗe hijabin jikinta kuwa a ya motse yake, cikin nuna ƙosawa tace,”Gaskiya ni fa tafiya zanyi in barka haba ace tun ɗazu mutum sai wani gyara gyara yake kamar mace.?” To ko ni da nake mace banyi wannan abin ba, kuma sanin kanka ne daga nan sai mun tafi gun boka ɗan kande kafin mu tafi can ko?”.
Daga wani ɗan akurkin ɗaki muryar take fitowa”Ke dai wallàhi akwai ki akwai tsangwama haba gani fitowa ai, kamar fa gani kike kin fini son kuɗin nan ko? “To Allah bara ki ji nafi ki buƙatar kuɗin nan dan ki sa ni”.
Murguɗa baki tayi murya ƙasa kasa tace,”Wawa kawai sakarai ƙanin bayan ka yayi aiki tukuru ya samu kuɗi amma kai kuma kana can kana ta shashanci gashi yanzu har ɗan sa yana nima ya hana mu rawar gaban hantsi banza kawai”.
Da haka Sale ya fito ya same ta,sallama suka wa inna Salma Sannan suka fita daga gidan ita kuma tana musu fatan samun nasara.
Fitar su ke da wuya ta janyo gyalan ta tana ɗingisawa. magana take cikin annashuwa da farin ciki tana cewa,”Hhhhh yara manyan gobe ku tafi ku gama faɗi tashi dan ganin dukiyar ɗan uwan ku ya dawo hannun ku, ni kuma ina daga gefe na sa hannun na karba sai yanda nayi daku da dukiyar baki daya”.
Da wannan tunanin take tafiya har ta isa wani kurmin daji, duƙawa tayi gaban wani bishiya mai duhuwar gaske…
“` duƙawa irin wacece mahaliccin sammai da ƙasai kawai ya dace bawa yayi masa tayi, innalillahi wa inna ilaihi raju’un duniya ina zaki tafi da mu? Mata mata mata wallàhi muji tsoron Allah mu gujewa aikin shaiɗan da son zuciya, shin ko kin mance cewa ko wani mintina naki a ƙi daye yake? “Shin kin mance cewa Allah yana kallon ki kuma sai ya tambaye ki akan duk abinda kika aikata? “Innalillahi wa Inna ilaihi raju’un, saboda kishi ki saka rayuwar ki cikin nadama da dana sa ni mara amfani, shin ɗan Kishiya ba ɗa bane ba? Kina nufin Allah da yace ayi mata hudu kin fi shi sanin abinda ya dace kenan? Menene aibun riƙe ɗan kishiya? Wallàhi babu komai a cikin bin boka face asara wanda babu girman asara daya fita, Allah yasa mu dace tunasarwa ne kawai????????????????““
Wasu irin surƙulle take wanda ita kaɗai tasan abinda take faɗa,can sai ga wani iska mai karfin gaske ya taso tsagaitawa tayi da surƙullan na ta tana kallon guguwar har ta lafa wani irin mumunar halilta na gani wanda ko kaɗan bazan iya misalta rashin daɗi gani da yake dashi ado ba.
Idanuwansa sunyi ja gefan fuskarsa sa yayi kamar an kona da rushin wuta a fusace yake kallo ta yace,”Menene kuma ya kawo ki a wannan lokacin bayan ina kan hanya ta ta zuwa daukar fansar ko na ni da tayi”?
Baki na rawa tace,’Allah ya….
Wani irin tsawa daya daka mata saida ta ni mi faɗuwa tsabar ruɗewa.
“Kullum ƙara tsayin laifin ki kike yi kuma tabbas zaki girbi abinda kika shuƙa, abinda yasa nake raga miki shine jinin mijin ki da kika shayar da masu mana hidima tabbas sun yaba da daɗin wannan jini haka yasa kullum suke miki uzuri, amma naga alamar baki san da haka ba, menene Matsalar ki? Ki gaggauta faɗa min dan kuwa bani da lokaci”.
Cikin ladabi tace”yanzi haka ƴaƴa na duk su biyu sun nufi birni dan amsar duk abinda ɗan Muhammad da matar sa suka mallaka kuma ina da tabbacin idan sun karɓa rabawa zasu yi a tsakanin su, shine nake so idan suka ƙarbo su rasa tunanin su har sai sun damƙa komai a hannun na”.
“Shikenan bukatar ki”.?
“Eh”.
“Lallai kin cika makira wacce tayi wa duniya zuwan asara, zanyi miki abinda kike buƙata saidai kuma ke ma zaki bamu jini”.
“Zan bayar idan har aka min wannan”.
“Shikenan tashi ki tafi”.
Da murna ta Inna Salma ta bar cikin wannan jejin tana jan kafar ta da ƙyar saboda ciwo da yake mata.
*********
Suwaiba da Sale kuwa gurin boka ɗan kande suka nufa kai tsaye, koda suka isa a zaune a ciki bokkan sa suka sama shi, ganin su yasa ya haɗe fuska yana cewa,”,Kunga zuwan matsiyata tabbas zuwan matsiyata babu al’fanu da zuwan ku gwara babu”.
Danne baƙin ciki su sukayi gudun kar ya ki taimaka musu, murmushi Suwaiba tayi tace,kar ka damu duk zamu biya ka kuɗin ka da zarar wannan aikin ya kammala,”.
Dariya boka ɗan Kande yake kamar sakarai can kuma ya murtuƙe fuskar sa yana cewa ku faɗi buƙatun ku duk da kasancewar nasan ba lallai ku biya ni kamar yanda kuka ɗauki alkawari ba, saidai kuma ku sa ni wannan aiki ba kuɗi kawai yake da buƙata ba tabbas muna bukatar jini, jini irin na tsohuwa, idan kuka sama mana babu shakka kun biye ni duk wani bashi da nake bin ku a baya”.
Kallon juna Suwaiba da Sale sukayi suna tunanin yanda zasu ɓullowa wannan al’amari, a tare suka furta zamu bayar da mahaifiyar mu”.
Dariya suka fashi dashi jin abinda zuciyar su yake saƙawa iri ɗaya, nan dai suka masa alƙawarin bayar da mahaifiyar su idan har burin su ya cika da haka suka bar gurin boka Ɗan Kande…
***************
Faruq da *Ummi* kuwa ko a cikin mota kira’a ne kawai yake tashi cikin motar kowa ka gani hankalin sa a tashe yake kuma kuwa da abinda yake tunani, a bangaran *Ummi* kalaman *Musaddam* ne kawai yake dawo mata Kamar yanzu yake faɗa,sosai kanta yake sara mata.
Ganin yanda jijiyoyin kanta suka mimmiƙe yasa Faruq fahimtar akwai matsala,kiran sunan ta yayi.
Gabaki ɗaya idanuwanta sunyi ja girgiza kan sa yayi yace,”Kinyi ƙoƙari kuma ina alfahari dake shalele Allah ya baki lada, akwai bukatar idan muka tafi ki zauna a gida ki ta ya Umma aikace-aikace sannan kema ki samu ki huta”.
Buɗe baki ta yi da niyyar bashi amsa wani irin salati ta gwalla ganin wani babbar mota ta yu kansu gadan gadan……..
Wash kuyi haƙuri sai kuma gobe in sha Allah
SAFNAH ALIYU JAWABI 08136746004
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????