MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_
3️⃣3️⃣
*_Sometimes Allah afflicts us with_*
_*tribulations because our hearts have been come too attached to this life*_ _*It is these hardship that break this attachments and refocused our*_ _*attention to the purpose of our existence. ALLAH didn’t creates us for this life. Duniya is not our home*_
_______Duk yanda Faruq yaso kaucewa motar nan ina,rintsa idanuwansa kawai yayi dan kuwa tuni ya daɗe da miƙawa Allah lamuran sa, wani irin huci ne ya bige fuskar su mai tsananin zafi har Saida suka kare fuskar su da tafukan hannayan su, buɗe idanuwansa Faruq yayi jin shiru babu alamar hatsari ko wani abu, abin mamaki babu wannan motar babu labarin ta saidai mutane da yawan gaske ga motoci sun haɗu sosai a gurin, sake kallon gefan sa yayi ya ganta kwance idanuwanta a kunshe ganin yanda numfashinta ke fita da sauri sauri yasa ya fahimci suma tayi.
Fitowa daga motar yayi yana bin jama’ar gurin da kallon mamaki kamar yanda suma suke binshi da kallon mamaki ,Sallama yayi musu yana cewa,”Dan Allah ku taimaka min da ruwa”.
Sai a sannan aka samu mutum ɗaya cikin su yace,”Yaro fatan dai babu abinda ya same ku ko”.?
Girgiza masa kai yayi daidai nan wanda ya tafi nimo ruwan ya ƙaraso gurin, amsar ruwan yayi ya shafa mata a fuska,da salati a bakin ta ta farfaɗo tana kallon sa da tsantsar mamaki tace,”Yaya Faruq ta ya ka kaucewa wannan motar”?
“Ni kaina abinda nake niman amsar sa kenan, amma nasan babu abinda Allah bayayi ga bayin sa”.
Wannan dattijon daya tambayi shi ɗazu shine ya kuma matsowa kusa dasu yace,”Yaro tabbas yau naga mu’ujiza ta Ubangijin taliƙai, tabbas naga amfanin saka yarda da yaƙini akan Allah buwayi gagara misali.
“Wato a lokacin da wannan babbar mota ta nufo kanku gadan gadan babu wanda yaga zuwan ta saidai kawai isarta jikin motar ku, wani irin ƙara na ban al’ajabi ne ya gaurayi ilahin garin nan baki ɗaya,abin mamaki ta jikin motar ku wannan babbar mota tabi ta wuce, bayan fitar ta daga jikin motar ku kuma ta ɓace bat”.
Sosai wannan abu ya bamu mamaki gabaki ɗaya,wani abin mamakin kuma shine ganin yanda motar ku da kanta take tafiya harta samu guri mai kyau ta tsaya, sai a wannan lokacin ne muka samu damar tsallakowa dan ganin abinda ke faruwa,abin burgewa shine kira’a ke tashi cikin motar ku kuma cikin Suratul baƙara lallai Allah yayi gaskiya kuma tabbas babu abin bautawa da gaskiya sai shi ɗaya buwayi gagara misali”.
Tunda wannan dattijo ya fara zantukan sa *Ummi* da faruq suke kallon sa kallo irin na al’ajabi, murmushi yayi yace,”Karkuyi mamaki domin kuwa Allah da kansa yace “yana tare da wa’anda sukayi imani kuma suka miƙa wuya saboda haka wannan yana daga cikin kariyar Ubangiji”.
Jinjina maganar sa sukayi sannan suka musu godiya..saida suka gabatar da Sallar azahar sannan suka kama hanya, har suka isa bakin su bai dana ambatar sunan Allah ba Allah cikin ikon sa kuwa suka isa gida lafiya, saida suka fara zuwa gidan su *Ummi* suka sanar dasu abinda ke faruwa Sannan suka nufi gidan su *Musaddam* zuwan su yayi daidai da zuwan Sale da Suwaiba, sosai *Ummi* take kallon su sam jikin ta bai bata ba.
Har mai gadi ya buɗe musu get *Ummi* tana leƙen su, cikin sauri Suwaiba ta isa ga Faruq tana cewa”Yallaɓai dan Allah dan tsaya”.
Tsayawa Faruq yayi yana kallon ta kamar ya santa sai kuma ya basar gaishe ta yayi yace,”Wa kike nima”.?
Gyara ɗaurin zanin ta tayi tace,”Nan gidan muka zo kuma kai ma naga kamar gidan zaka shiga dan Allah mutanan gidan suna ciki”.?
” Fatan dai lafiya”.?
“Lafiya ƙalau yaro”.
Shiru yayi can kuma yace,”Gaskiya basa nan amma kina iya shigowa matar gidan tana zuwa”.
Daga haka yayi shigewar sa cikin gidan ,samu guri yayi parking a tare suke fita daga motar ita dai *Ummi* sam jikinta bai bata da wa’anan mutanan ba saidai tunawa da tayi addini ya haramta zargi yasa tayi istigifari Sannan ta kawar da zancan a ranta.
Koda Suwaiba da Sale suke shigo cikin gidan Sale rikicewa yayi dan kuwa gidan ya sake zama sabo a gunsa har yana ai ya na yands zai baje kolin sa cikin gidan yana wani murmushin mugunta, kamar ance *Ummi* ta miƙe kawai sai ganin Suwaiba tayi tana cusa abu cikin kujerar da take zaune kallon ta take da mamaki har zatayi magana suka ji sallamar Mummy da murmushi akan fuskanta. saidai ganin Suwaiba da Sale yasa ta murtuƙe fuska kamar bata taɓa dariya a gidan duniyan nan ba, “Me kuma ya kawo ki gida na.?” Shin kin zo ki ƙarasa abinda kina so ma ne”.? “Ko kuma zuwa kikeyi dan ki duba shuƙar da kikayi ko tayi tsiro? “To albishirin ki babu ɗaya cikin shirin ki wanda yayi tasiri akai na da ƴaƴa na, domin kuwa Allah muka mayar abin ji da ganin mu, Kinga kuwa wallàhi ba dai mutum ba , Suwaiba ki kwana da sanin duk gidan da Allah yayi wa katanga wallàhi komai karfin iska saidai ta wuci ta gabanta saboda haka fice min daga gida bana fatan sake ganin ki a cikin gidan nan dama rayuwar mu gabaki ɗaya”.
Magana Mummy take tana kuka, sosai Suwaiba da Sale suka cika da tsananin mamaki dan kuwa tsawon shekaru talatin babu kalma ɗaya da ta taɓa furta musu a matsayin martani amma gashi yau harda kora, gyara zani Suwaiba tayi tace,”Zamu tafi kamar yanda kika buƙata Allah ya bamu alkairi”.
Da mamaki Sale yaka kallon ta har zai buɗe baki tace,”Yaya mu tafi kawai babu matsala ai rayuwa ce”.
Har ta kai bakin ƙofa,cikin ɗaga Muryar *Ummi* tace” kin mance da ajiyar ki kuma zaki tafi”.
Cike da tsoro da fargaba Suwaiba ta juya tace,”Ni babu abinda na mance dashi”.
“Au haba dai to bara na nuna miki”.
Janyo hannun ta *Ummi* tayi har bakin kujerar tace,”Tabbas akwai abinda kika aje anan domin kuwa na ganki da ido na saboda haka saka hannu ki fitar dashi”.
Sosai Suwaiba ke gumi domin kuwa idan bata mance ba boka Ɗan Kande cewa yayi,”Da zarar kin saka musu ƙasan kujera ko kuma gado ,tofa duk wanda ya ƙwanta a kai ko kuma ya zauna shikenan an gama da babin sa dan kuwa cikin abu uku tofa guda ɗaya ne zai faru, ko ya makance makanta na har abadan ko kuma yayi hauka ko kuma shanyewar ɓarin jiki, idan kuwa akayi rashin sa’a ma wanda ya zauna ko kuma ya kwanta bashi da tsarki tofa akwai yuwar duk ukun ma zasu hau kansa ba tare da ɓata lokaci ba”.
Wani irin zufa mai kaurin gaske ne ya fara feso mata, kallon *Ummi* take tana aiyana nisan ta da wannan kujerar dan kuwa yanzu hanya ɗaya ce kawai mafita a gare ta , shine tura wannan hatsabibiyar yarinyar saman wannan kujerar, komawa da baya tayi ta ingiza *Ummi* kan wannan kujera………
Yawan comments yawan page ????????????????????????????
SAFNAH ALIYU JAWABI
081367460004
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/