HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Daburcewa tayi tace,”A a kai dai bari yaro na kuna tafiya na samu ganyan magarya da sabara na shafa a ƙafar shine cikin ikon Allah harna samu na ɗan sauki”.

“Hmmm inna kinci narasar tarwatsa rayuwar ƴaƴan ki gudu biyu wanda su kenan Allah ya Mallaka miki shin wani amsa zaki bawa Ubangijin ki yayin daya tambayi ki amanar daya baki”.? “Inna ina da tabbacin baki da amsa da zaki bashi, gefe guda kuma mu ma ba zamu taɓa yafe miki ba, domin kuwa kece abu na farko da nake takaici da kuwa Allah wadar dana fito ta tsatsonki Inna”. Nayi kuka wanda babu amfani yau, nayi dana sanin kasancewa abu na farko da kika fara fitar wa ta ƙarƙashin ƙafar ki, Inna menene makomar mu? Inna menene makomar mutumin da aka haɗa hannu dashi gurin kashe mahaifinsa da kuma ɗan’uwan sa”.?

Wallàhi inna ba zan taɓa yafe maki ba, tabbas nasan bani da sauran wani rahama dan kuwa nine nayi jagora aka kashe mahaifina”innalillahi wa inna ilaihi raju’un Allah na tuba Allah ka yafe min Kasancewar ka mai rahama da jinƙai”.

Kuka Sale yake sosai kamar ransa zai fita.

Cikin kakkausar murya tace,”Dalla rufa min baki dan banza shege ka wani zo da ƙazamar bakin ka kana wani faɗa min zancan banza zancan wufe,dama tunda kazo duniya wani abin arzikin kake bani”? Shin ka taɓa yin abinda naji daɗi kuma na saka maka albarka ne”.? ‘ to bara kaji wallàhi wallàhi baka isa ka tsayar min da cikar buri na ba kaji na rantse maka wai ina Suwaiba take”.?

Matsawa gefe yayi yace,”Gata kamar yanda kike da muradin ganin ta”.

Wani irin ƙara Inna Salma ta kwalla tana mai dafe bangwo wani irin ashariya ta sake tana wani yatsina baki ala dole ranta a ɓace yake tace,”Haka suka mayar dake Suwaiba”? ” Tab lallai kuwa Ni’ima da ahalinta sun taɓo jinin wanda ina da tabbacin ba zasu taɓa sha ba, lallai sunyi kuskure mafi muni dan kuwa mahaifin ku babu abinda yake so da ƙauna sama da ƴaƴan sa wato ku kenan faruwan wannan abu lallai na san zai mattukar fusata shi”.

Da mattukar mamaki Sale ya nufi gunta jijiyoyin kan sa sunyi wani irin mimmiƙe wa akan fuskar sa, idanuwansa kuwa sunyi ja jazir wani irin abu ne ya tsaya masa a maƙogoro murya na rawa yace,”Wanene Mahaifin mu”.?

Kame kame ta fara yi dan kuwa maganar suɓucewa yayi daga bakin ta ,ganin bata da niyyar faɗa masa yasa ya shaƙe mata wuya murya cike da ɓacin rai yace,”Tabbas idan baki faɗa min ba babu shakka zan kashe ki kuma na tabbata ko a gurin Allah Bani da laifi”.

Ganin da gaske zai kashe ta yasa tace,”Zan faɗa maka”.
“Faɗa min cikin lokaci yana nufin tsira da ranki cikin sauƙi dan kuwa babu abinda nafi tsana sama da ke a cikin duniyar nan”.

“Baba mai shaye shine asalin mahaifinka kuma shi ɗin ya kasance matsafi tun kafin ni kaina a haifi ni, garin niman maganin yanda za’ayi na auri Aliyu yasa na fara zuwa gurin sa amsar magani dan in samu na mallake shi ,shine ya bukaci dana bashi haɗin kai, babu musu na aminci masa muka aikata alfasha, tun daga wannan rana ban sake zuwa gunsa ba tunda dai buri na ya cika, abin mamaki wata rana bayan na cika wata biyu gidan Aliyu aka aiko kira na koda na fita shina tarar a kofar gida”.

“sosai tsoro da fargaban kar Aliyu ko matar sa su ganni yasa nace masa ya tafi zanzo, koda na tafi abinda ya faɗa min saida naji duniya tana juya min.

“Salma akwai ajiya ta acikin ki kuma daga nan zuwa wata tara ina buƙatar jini na,”.

A firgice nace,”Wani jinin ka kuma”.?

“Tabbas kina da ciki a jikin ki kuma wannan cikin dai nawa ne”.

Kuka na fashe dashi ina roƙon sa daya rufa min asiri,tsawa ya daka min yace,”Alfarma guda ɗaya zan yi miki shine ba zan taɓa faɗawa kowa wannan sirin ba, amma zaki rinƙa bani haɗin kai a duk lokacin dana buƙata”.

Da wannan yarjejeniyar na samu na zauna a wannan gida cikin salama harna haife ka, bayan haihuwar ka da shekara biyu na sake samun wani cikin wanda shima dai nashi ne, kuma duk shi yake faɗan sunan da yake so a saka muku”.

 

Wani irin hajijiya ne ya ƙwashi Sale sai ƙasa, da rarrafe Inna Salma ta isa gare shi tana cewa,”Tabbas wannan shine asalin ku sam bakwa da wata halaƙa da jikin Aliyu, Muhammad shine asalin gudan jinin sa,wanda aciki sa aka samar da *Musaddam*.

********

Gari na waye wa Mummy suka ɗauki hanyar garin Suleja cike da ɗokin ganin gudan jinin ta, wannan karon harda Umma da Abba dan kuwa wannan ba ƙaramin lamari bane ba,lallai Allah shine yake jarabtar bayin sa da abubuwa daban daban dan nuna ikon sa da buwayan sa akan su.

 

*Musaddam* kuwa koda garin Allah ya waye kasa zama yayi dan kuwa bashi da sauran wani buri face ganin mahaifiyar sa abin so da ƙaunar sa, ganin halin da yake ciki yasa Kaka tasowa zuwa inda yake yace,”Kai kuwa kayi hakuri sunanan tafe da yardar Allah kaji”.?

“Kaka so nake naga Mummy na ,Kaka itace abu na farko dake sanyaya ruhi da gangar jiki na,Kaka itace ruwan dake kawar da ƙishin ruwa na, Kaka itace sanyin idaniya ta, Kaka itace take saukar da inuwa sassanya a duk lokacin da zafin rana ya firgitar da ruhi na, Kaka itace ta shayar dani, Mummy itace komai nawa, Kaka faɗa min shin idan kai ne a matsayi na yaya zakayi,”.?

“Zanyi abinda yafi Wanda kake yi yanzu”.?

 

………

08036746004 *SAFNAH ALIYU JAWABI*
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idiriss Musa_

3️⃣6️⃣

_*The company you keep will have a great impact on how you live your life. Make sure you do it with the right people. Choose them wisely.True. No one is perfect and this is why it is important for us to be with good company who will remind us to get closer to Allah.*_

 

________Murmushi yayi yace,”Kenan nawa kaɗan ne Kaka”.?

“Tabbas dan kuwa Uwa tafi gaban wasa”.

“Ji nake kamar na tafi mu haɗu a hanya”
“Ƙwanta kayi bacci in Sha Allah kafin ka farka sun iso”.

“Cikin wannan yanayin sam ba zan iya barci ba”.

“Allah ya kyauta masu rigimar yawa gare su”.

“Ni fa ba rigima nake ba”.

“Kana nufin wannan kadan ne”.?

“Kai Kaka kaima akwai rikitar da mutum”.
“A tunanin ku kune kaɗai kuke da basira”.?

“Amma ai ta mu tafi ta ku”.

“Tun da lokacin mu ba’a yankan kai ba? “Kuma ba’a satan mutane ayi cinikin su kamar ana cinikin kayan sawa, kuma alokacin mu babu yawan mabuƙata dan kuwa komai ƙanƙantar abincin gidan ka zaka fitar dashi zaure kuci kai da abokan ka, alokacin mu babu cin amana kamar na yanzu , alokacin mu babu ɓaraka kamar ta ku lokacin, a lokacin mu fyade da cin zarafin mata abune wanda sam bamu sanda wanzuwar ta ba, alokacin mu iyaye sukan boye son da suke wa ƴaƴan su kawai dan suga sun zama ƴaƴa na gari abin kwatance, lokacin mu mun nuna wa ƴaƴan mu niman halas  komai ƙanƙantar ta, alokacin mu mun nunawa wa ƴaƴan mu mata cewa idan suka ga maza suna zuwa su tsaya tukunna har sai sun huce kafin suma su tafi, alokacin mu  mace tana da daraja da ƙima, alokacin mu maza suna da mutunci da girma a idanuwan matan su, idan na tsaya jera maka abubuwan da wannan zamanin tayi rashi tabbas zaka zubda  hawaye, duk da kuwa akwai na kwarai har yanzu cikin duniyar nan saidai kafin ka gansu shine abu mai mattukar wahala”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button