HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Jinjina kansa kawai *Musaddam* yayi dan kuwa duk abinda Kaka ya faɗa gaskiya ne, kawai sai dai Fatan Allah ya gyara mana al’amuran mu.

“Hmmm ka fahimci abinda nake faɗa kenan”?

“Na fahimta Kaka, amma idan muna son gyarawa ta wace hanya zamu bi”.?

“Duk abinda suke faruwa a yanzu yana daga cikin alamomin tashin alkiyama  kuma babu wanda ya isa ya hana su faruwa dan kuwa haka Allah ya shirya al’amarin sa, amma duk da haka ba’a rasa hanyar gyarawa ba, hanya mafi sauki shine komawa ga Allah mahaliccin kowa da komai dan Kuwa  lokaci baya jira, idan har al’umma zasu fahimci cewar ko yatsar ƙafarka baka isa motsawa ba saida izinin Allah tofa komai zai dawo daidai, ina ma jama’a zasu fahimci duk kan mu akan mizanin kardarar mu muke tafiya da al’fahari da ɗagawa sun gushe daga zuciyar mutane, ina ma jama’a zasu fahimci baka isa sawa ko hanawa ba da babu shakka hassada da ƙyashi sun gushe daga zuciyar mutane, ina ma zamu fahimci akwai wata rayuwa bayan nan da son duniya da abinda ke cikin ta yayi gaggawar rabuwa da zuƙatan mu, ina ma iyaye zasu fahimci ƴaƴan su amana ne agurin su kuma abin tambaya a gurin su ranar tashin alkiyama da sunyi musu tarbiya ta hanyar nuna musu Allah da Manzon sa..ina ma ƴaƴan zasu fahimci iyayan su dole ne akan su da sun yi musu biyayya koda kuwa bayan ran sune,  dan kuwa hakkin mahaifi akan ɗansa yana nan koda kuwa bayan rai ne, ina ma mata zata fahimci cewa yin biyayya ga mijinta shine kawai samun tsara agare ta ranar gobe kiyama, data mishi biyayya gwargwadon iyawar ta.ina ma miji zai fahimci matar sa amana ce wacce Allah ya damƙa masa amanar ta kuma zai tambaye shi akan ta ranar gobe kiyama wallàhi da yayi mata riƙo kwatance yanda zai yi wa kansa”.

“ina ma maci amana zai fahimta kuma ya gane kuskuran sa ya kuma ni mi yafiya agun wanda yaci amanar da tofa da babu shakka ya samawa kansa Sallama, ina ma zamu fahimta mu daina ɗaukar alƙawari alhalin ba mu ke da iko akan kan mu ba da rai da gangar jiki sun samu sallama,  Allah yasa mu dace.”

Sauke ajiyar zuciya *Mussadam* yayi hawaye na gangara yace,” Innalillahi wa inna ilaihi raju’un”.

“Wannan kaɗan ne daga cikin abubuwan da suke gaban mu fatan mu kawai Allah yasa muyi ƙarshe mai kyau”.

“Amin amin”.

Sallamar da suka ji ne yasa *Musaddam* miƙewa cikin sauri ya nufi ƙofar ɗakin , daskarewa yayi agurin wasu irin hawaye masu ɗumi suna zubuwa daga kan fuskar sa, ita kanta ji tayi kamar tayi Shekara bata ga gudan jinin ta ba, ji take kamar bashi bane saboda rama da haske da yayi ita kanta hawaye take sosai, riko hannun sa tayi tace,”Yau sai nake ganin ka kamar mahaifin ka, ban taɓa ganin kamanin ku ba irin na yau, sai nake ganin kamar shine ya dawo, ina ma ina ma.. kukan da yaci ƙarfin tane yasa ta kasa ƙarasa zancan ta.

Ganin haka yasa ya durƙusa a gabanta, riƙo ƙafar ta yayi yace,”Mummy ki agaji rayuwa ta,ki taimaka ki min sutura, ki tausaya ki luluɓe ni da wannan inuwar mai saukar da sallama , ki taimaka ki agaji rayuwa ta ta hanyar yafiya a gare ni duk da kuwa a halin rashin lafiya ne ke”.

Gabaki ɗaya gurin kuka suke harda Kaka saida ya share ƙwallar da suka cika idanuwan sa, dan kuwa an ɗauki dogon lokacin baiga irin wannan soyayyar ba bayan wanda shi kansa yake wa Umma mahaifiyar *Ummi*.

Ɗago shi tayi tace,”Ni kuwa me zance da Allah sai godiya daya bani ɗa ɗaya tamkar dubu, a gare su ka kasance ɗaya a gare ni ka kasance tamkar dubu *Musaddam* kwantar da hankalin ka tuni na daɗe da yafe maka dan kuwa nasan Wanene ɗa na, babu abinda zai fito daga baki na akan ka har ƙarshan rayuwa sai albarka da fatan Allah ya kare ka daga sharrin zamani”.

“Mummy mu shiga ki zauna kin gaji fa.”

Wani irin waigawa *Musaddam* yayi cikin sauri dan ganin ma mallakiyar wannan murya, maƙale take bayan Umma tana wani cin no baki ala dole ta gaji da zaman mota, kallon ta yake babu ko ƙiftawa ita kuwa ganin haka yasa ta ƙara shigewa jikin Umma tana sun ne kai.

Murmushi Mummy tayi tace,”Zo kusa dani yar lele ta , zo ki gaisa da Ya’yan ki”.

Matsowa Ummi tayi daf da Mummy tace,”Gani Mummy na”.

“Baku gaisa ba”.

“Ina yi ni ya jiki”.?

“Lafiya”.

Kallon sa Mummy tayi jin yanda ya amsa a daƙile tace,”ko dai jikin ne”.?

“A a mummy mu shiga ciki ki huta”.

“Ai kai a ɗakin ka zaka zauna ni da ita mu shiga ciki,”.

Gabaki ɗaya dariya suke jin wannan furuci na *Ummi*.

*Musaddam* kuwa ji yayi ina ma zata kwana tana magana ba tare da ta tsaya ba da babu abinda zai kai haka daɗi a gun sa, “Wacece ita kuma daga ina take”.?

“Muryar ta babu bambanci da muryar sahiba ta”.

Kallon sa Mummy tayi tace,”Wannan itace ta zama tsanin kasancewar ka cikin ƙoshin lafiya yanzu.”wannan itace mafi godiya da soyuwa cikin abubuwan dana samu acikin wannan lokacin…nanfa ta fara zai ya no masa duk abubuwan da suka faru wanda ita a bakin faruq take samun labarin su, rungume faruq yayi yace,”Lallai na shaida kai aboki na gari ne fata na Allah ya biya ka da mafificin alkairi”.

Koda ya kalli *Ummi* murmushi kawai yayi dan yama kasa furta koda kalma ɗaya, ganin haka yasa Umma tayi musu izini da su shiga ciki dan su huta, haka kuwa akayi *Mussadam* kuwa sai satan kallon ta yake.
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_

3️⃣7️⃣

*_”Maturity is not by age I’m still a small girl but I’m mature enough to control myself I don’t engaged myself in matters that doesn’t concerns me. Is not a beef or pride I’m just minding my own business”*_

 

 

______ Saida suka ci abinci sannan aka sake sabon zama, dan kuwa *Musaddam* ji yake kamar mafarki yake ba gaske ba, wai duk abubuwan nan da akan lilsafa shi yayi su”? “Innalillahi wa inna ilaihi raju’un, gabaki ɗaya idanuwan sa sunyi ja sun canza kala, jijiyoyin kansa sun tashi sunyi ruɗu ruɗu. Ganin haka yasa ta miƙe ta nufi randar ruwa mai sanyi ta ɗibo ta miƙa masa tana wani kawar da kai kamar bashi take miƙawa ruwan ba, ƙarba yayi yace,”Nagode ƙanwa ta”.

Komawa tayi ta zauna tana karantar yanayin sa sosai ya bata tausayi duba da yanda yake ta sauke ajiyar zuciya.

“Son karka damu haka lamarin Ubangiji yake fatan mu Allah yasa mu cinye jarabawar mu”.

“Mummy ba zan iya taɓa mancewa da wannan iftila’in ba dan kuwa wannan shine abu mafi girma daya taɓa faruwa dani tsawan rayuwa ta kema kuma kin san haka”.

“Shi yasa nace Karka damu wannan kaɗan ne daga cikin jarabawar da Allah yayi alƙawarin jarabtar bayin sa wanda suke iƙrarin sunyi imani, tabbas imanin ka ba zai cika ba sai an jirabe ka da abubuwa masu yawan gaske, saboda haka ka daina damuwa”.

“In sha Allah”.

“Baba na gode sosai da sosai babu abinda zan iya cewa saidai kawai nayi maka addu’ar gamawa da duniya lafiya, Allah ya jibanci lamuran ka dana iyalan ka, Allah ya jiƙan ka ya jiƙan iyalan ka koda bayan rai ne, Allah yayi maka sakamako da gidan aljannar sa maɗaukakiya, ina maka Fatan alkairi a tsawan rayuwar da za kayi nan gaba, tabbas ba zan mance da alkairin ka ba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button