MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

A tare duk suka amsa da Amin.
Gyara zama Kaka yayi yace,”To alhamdulillah duk kan godiya su tabbata ga Allah mahaliccin kowa da komai daya bamu aron wannan lokacin dan kuwa da yardar sa muke gudanar da komai namu, tsira da aminci Allah su kara tabbata ga annabi Muhammad (S A W) .”tabbas ba zance faruwar wannan abu yana da dangantaka da rashin kulawa ta addini ba, dan kuwa na ganta atattare da ku ,a tattare da ku na hango kamala irin na mutane masu riƙo da addini dan kuwa ma’abota addini suna ɗauke da wata irin natsuwa da cikar kamala wanda ba ko wani mutum ke ɗauke dashi ba, nayi imani wannan yana ɗaya daga cikin jarabta na rayuwa”.
“To alhamdullahi tunda komai ya zo karshe Allah ya daɗa kare mu daga sharri mahassada”.
Atare duk suka amsa da amin.
Daga nan kuma aka shiga hirar Duniya, gabaki ɗaya *Mussadam* kasa ɗauke idanuwansa daga kanta yayi sosai yake jinjina wa ƙoƙarin ta akan sa, “wannan mace ce kuwa”.? “Tabbas ta cancanci kyauta irin ta girmamawa daga guna amma me zanyi mata na biya ta wahalhalun da tayi dani.? “Kai gaskiya babu”,. Haka dai yayi ta saka da warwara kuma duk idanuwan sa akanta yake.
Ita kuwa sam kasa sakin jiki tayi gani take kamar kallon kaskanci yake mata duk da kuwa ta shaida karamcin sa akan mutanan da yake mu’amala dasu.
Koda ya koma ɗaki sa gabaki ɗaya kasa bacci yayi dan kuwa duk inda ya juya fuskarta yake gani tsaki yayi yace,” *Ummi* ki barni nayi bacci man kin tsaya min a ido”.
“Wace *Ummi* kuma”?
“Malam bana son gulma haba kayi bacci ka kawai mutum sai sa ido”.
“Hhhhhh, Allah ya baka haƙuri amma dai kace mata ta barka kayi bacci dan kuwa gobe zaka kama hanya”.
Duka ya kai masa da pillow dake hannun sa, dariya Faruq yayi yace,”menene laifi na? Abakin ka fa naji”.
Ganin nema yake ya dagula masa lilsafi yasa yayi kwanciyar sa kamar yana bacci saidai shi kansa yayi mamakin yanda akayi har zancan zuci ya fito waje”.
Faruq kuwa ajiyar zuciya yayi yace,”Allah ka amshi addu’a ta”.
Da haka duk sukayi bacci.
Yau ma kamar kullum mafarkin ta yake zaune take fuskanta luluɓe da farin mayafi amma da alama tana cikin farin ciki.
“Sahiba yau kuma kinyi shiru babu magana ne”.?
“Hmmm yau babu abinda zance ne ai”.
“Ki min magana ko zanji daɗi dan Allah”.
“Abu ɗaya na sani shine ina matukar so da ƙaunar ka Yaya na”.
“Nima haka amma dai yaushe zaki zo gare ni”.?
“Ai ni kullum ina tare da kai kane kawai baka jina a kusa da kai”.
“Ban fahimta ba”.?
“Lokaci zai nuna maka Ya’ya na”.
“Ke kuwa meyasa zaki miƙe bamu gama magana ba fa”.
“Ina tare da kai ai na faɗa maka, kawai ka kwantar da hankalin ka kaji masoyi”
“Naji amma ki buɗe min fuskar ki na gani dan Allah”
“Shine kawai abinda kake so?”
“Eh”.
Hannu tasa ta yaye gelan fuskar ta juyawar da zatayi, aka fara kiran sunan sa da karfi, ” *Mussadam* *Mussadam* a firgice ya farka yana goge idanuwansa, wani irin mugun harara ya watsa masa haɗe da jan tsaki yace,
“Kai wallàhi idan ba dan kai aboki na bane da sai nace kafi kowa baƙin ciki dani yasin”.
Dariya faruq yake sosai yace,”Nashiga uku ni Umar daga warkewa kuma sai masifa”.?
Ɗaka masa duka yayi yace,”menene ka wani zo kana ta yar da ni”.?
“Mummy ce tace na tayar da kai muje masallaci”.
“Kaji gulma a ina kaga Mummy ɗin? Zaka wani haɗa karya da ita”
Magana yake yana zura kafar sa cikin takalmin sa.
koda suka idar da sallar asuba zama yayi a masallaci ya gabatar da azkar Sannan yayi addu’a sosai akan alkairan dake tsakanin sa da wannan yarinyar ta cikin mafarki.
Lafiyayyan kunu da kosai aka musu suka karya dashi, sosai mummy taji daɗin wannan tarbar da suka samu lailai Ummi ta fito daga gidan mutunci da karamci, wannan tayi daidai da irin matar da nake wa ɗana gudan jinina, addu’ar samu”.
Cikin zuciyar ta duk take aiyana wannan,fuskar ta ɗauke da murmushi, saida suka gama karyawa sannan yayi gyarar murya yace,
“mummy sai zuwa yaushe zamu tafi”.?
Ɗaka masa duka Kaka yayi yace,’kuji min ja’irin yaro to babu inda zaka tafi anan zaka zauna kaji na faɗa maka”.
Gabaki ɗaya dariya suke jin diramar kaka da *Mussadam*.
Saida suka gama shirin su tsaf sannan kaka ya sake tunasar dasu akan kiyaye dokokin Allah, sannan riko da addu’o’i wanda tabbas idan bawa yayi riko dasu babu makawa ya kuɓutar da kansa daga sharrin mai sharri.
Addu’a yayi musu cikin babban gora mai ciki da ruwa ya basu suka tafi dashi, *Musaddam* harda yar kwallan sa sosai yake jin ƙaunar wannan tsohon a ciki rainnsa.
Tunda suka kama hanya hira kawai suke amma banda mutum biyu , *Mussadam* tunanin wannan yarinyar kawai yake, inama yanzu ya ganta koda kuwa sau ɗaya ne”.
“*Ummi* kuwa gabaki ɗaya jikinta ne yayi sanyi saboda tasan daga yau ba kullum zata rinka ganin shi ba, ji take kamar wahalar ta, ta dawo sabuwa ne” dawa zanyi wannan maganar? Waye zai kawo min agaji? Allah ka taimake ni, ina masa so wanda bansan adadin ta ba.
“Kanwa ta lafiya kalau kike kuwa?”
Daga sama ta jiyo Muryar sa, afirgice tace,”lafiya kalau Yaya na”.
Wani irin bugu kirjinsa yayi jin suna da kuma muryar yarinyar cikin mafarkin sa sak innalillahi wa inna ilaihi raju’un kawai yake ambata da ƙarfi, a ruɗe Faruq ya tsayar da motar yana tambayar sa lafiyar sa kalau kuwa”.?
08036746004 safnah Aliyu jawabi
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idriss Musa*
_Jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idriss Musa_
3️⃣8️⃣
*Don’t jump to conclusions. Things aren’t always what they seem. Our conclusions may be logical but they may not be true. By refraining from making the wrong assumptions, we can avoid unnecessary pain & conflict. So don’t be too quick to judge & condemn. Instead do be discerning!*.
_________Ganin yadda hankalin su ya tashi yasa ya sauke ajiyar zuciya, “babu komai kawai dai haka na ji gabana yana faɗuwa”.
“Haka kawai?”.
“Eh wallàhi, Mummy”.
“To ka rinƙa addu’a, insha Allahu babu abinda zai faru ka ji?”.
“To…Allah yasa Mummy”.
Tafiya suke amma zuciyar sa wani irin bugawa take da ƙarfin gaske, so yake ko da uhmm ne ta sake furtawa amma shiru har suka isa, a gida aka sauke *Ummi* da iyayenta, kallonta yake har ta shige cikin gida Mummy kuwa har cikin gidan ta raka su ban da godiya babu abinda bakinta ke furtawa, ganin abin yayi yawa yasa Umma tace,” Don Allah Hajiya wannan godiyar tayi yawa don Allah ki daina dukkan mu mun zama abu ɗaya yanzu wallàhi babu damuwa ai Musaddam kamar ɗana ne nima ko?”.
Ajiyar zuciya Mummy ta sauƙe kafin ta iya samun damar buɗe bakinta, “tabbas na daɗe ban ji ko da labarin mutane masu karamci irin naku ba. Allah ya saka muku da mafificin alkairi, mun gode sosai”.
Da haka suka yi sallama har gurin mota Ummi ta sake raka Mummy, har za ta tafi yace, “ni kuma wa na kashe miki?”.
Da mamaki take kallon sa sai dai ta kasa furta ko da kalma ɗaya ganin haka yasa Mummy tace, “don Allah kar ka saka min ƴa a gaba…haba dai. Kalli nan…kar ki damu da shi kin ji…yawwa yaushe zaki zo min?”.