HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Abba wanda shigowarsa kenan yana tsaye daga bayanta yace, “Amin”. Waigowa ta yi tare da murmushi ta nufi inda yake tsaye.

*MUSADDAM NE ZAƁINA*????????????????

______________________________________________________________________

*Reviewed by: Musaddam Idriss Musa*

????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

 

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

_Jama’a ku shaida na sadaukarwa da wannan littafin ga*Musaddam Idriss Musa_

*Reviewed by: Musaddam Idriss Musa*

4️⃣

 

*Don’t pay heed to people who talk behind your back. You can’t stop them. What everyone else has to say, think, or feel about how you live your life does not and should not affect your happiness or state of mind. It’s really about them, not you. Realize this before it’s too late.‬*

 

______shafa kanta Abba ya yi yace, “kar ki damu insha ALLAH komai zai yi daidai”.

Murmushi Umma tayi tace, “babu komai ai, na san jarrabawa ce daga Rabbil izzati…wata rana komai zai daidaita”.

“Ina alfahari dake”.

Kallon sa tayi tana murmushi tare da sunkuyar da kai tace,”ni ma haka”.

Washe gari tun da asuba *Ummi* ta sa rigima ita fa wallahi ba za ta zauna a wannan asibitin ba kawai a sallame ta tunda ta warke. Daƙyar umma ta samu ta rarrashe ta akan ta bari gari ya ɗan ƙara wayewa.

Ba don taso ba tayi yanda Umma tace. Barci mai nauyi ne ya ƙwashe ta ba ita ta farka ba sai kusan 11:00am.

A firgice ta farka tana faɗin shikenan Umma ya tafi aiki wallahi, kun sa yau ma na yi rashin ganinsa da safe”.

Kuka take sosai sai da Abba da kansa ya rarrashe ta sannan aka samu ta nutsu.

Kallon ta Abba ya yi yace, “kar ki ɗaga hankalinki kin ji *Ummi* na?”

Ita ma kallonsa take hawaye na zuba tace, “Abba da yau ina da ikon buɗe maka zuciya ta da na buɗe maka ko don ka ga yadda ta rabu gida biyu”.

Bin ta da kallon mamaki yake yace, “bangane abin da kike nufi ba *Ummi* ta yaya aka yi zuciyar ki ta rabu gida biyu? Kuma ke da baki da ikon ganinta ta yaya kika san cewa ta rabu?”

Murmushi mai ciwo *Ummi* ta yi tace, “Abba zuciyata ta rabu gida biyu ne sakamakon rashin ganin *MUSADDAM* da nake fatan hakan a kullum…gida ɗaya cike yake da so da ƙaunar sa, ɗaya ɓangaren kuma…” tsagaitawa da zancan ta ɗan yi tana cewa, “ashhh! Abba ɗaya ɓangaren yayi ciwo a karshe kuma ya zamo min gyambo ta yadda duk ranar da ban ga *Musaddam* ba yake min ciwo mai raɗaɗi da ƙuna”.

Abba dafe kansa yayi a bango jin irin furucin dake fitowa a bakin ƴarsa gudan jinin sa, yarinyar da a da can baya ko magana za tayi ma sa sunkuyar da kanta take amma yanzu duba yadda soyayya ta mayar da ita”.

Kallon Abba *Ummi* tayi tace,”Abba mu tafi gida don ALLAH”.

Hakan nan ba don sun gamsu da samuwar lafiyar ta ba suka sa hannu aka sallame su.

Fitowar ta daga ɗakin da aka ƙwantar da ita yayi daidai da fitowar mummy daga ɗakin da *MUSADDAM* yake ciki. Bangaje ta mummy tayi ba tare da sanin ta ba domin kuwa lokacin share hawayen da suke zuba mata take. Sosai lamarin *MUSADDAM* yake ba ta mamaki.

Cikin sauri mummy ta riƙe *Ummi* wace tayi baya kamar za ta faɗi tana faɗin, “ki yi haƙuri kin ji baiwar ALLAH”.

Kallon ta *Ummi* tayi sosai ganin da gaske mummyn *MUSADDAM* ce yasa ta gyara tsayuwar ta. Yayin da a cikin zuciyar ta kuwa cewa take,” me kuma ya kawo surukata asibiti? Waye ba shi da lafiya?”

Kiran sunanta da Umma ta yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shilla, murmushi ta yi tare da sunkuyar da kai kasa.
Mummy tace, “ke kuwa a wannan ƙarancin shekarun naki tunanin me kike haka, ai sai ki jefa kanki a wata damuwar?”

Sunkuyar da kai *Ummi* ta sake yi kasa haɗe da turo baki gaba alamar shagwaɓa cikin ranta kuwa cewa take, “ba ɗanki ba ne ya hana ni sukuni”

Dafa ta mummy tayi cikin nuna kulawa tace, “yata ki daina yawan sa wa kanki damuwa kin ji?”

Murmushi umma tayi tace,”ai kuwa dai tana fa ma da shi sai dai kawai mu ce ALLAH ya kyauta”

Da amin mummy ta amsa tana cewa, “wallàhi nima haka nake fama da nawa ɗan, abu ƙaɗan wanda sam ɓai kai matsayin damuwa ba sai su ɗauka su ratayawa kan su”.

Share hawayen da ya gangaro mata mummy za tayi kawai sai jin saukar hannun *Ummi*  saman fuskarta ta yi tana goge mata hawaye.

Murmushi tayi tace,”ALLAH yayi miki albarka ‘yan nan.”

“Amin” Umma ta amsa mata, yayin da ita ma Ummi ta amsa daga can kasan zuciyarta saboda kunya.
Kallon su mummy tayi tace, “na tsayar daku ko?”

Girgiza kai umma tayi tace, “ai haka lamarin ALLAH yake mu ma tafiya gida za mu yi yanzu insha ALLAH”.

“Ayya kuma kuna da marar lafiya ne a nan cewar mummy?

Murmushi umma ta yi tace ita ce ba ta da lafiya amma yanzu Alhamdullahi ta samu sauƙi har an sallame mu yanzu haka gida muka nufa”.

Kallon ta mummy tayi tace,”Ayya ki ce na so ƙarasawa Doctor marar lafiya?”

Gabaki ɗayan su murmushi su kayi saɓanin *Ummi* wace cikin zuciyar ta cewa take, “ai tuni ɗanki ya gama ƙarasa ni…kuma shi ne kawai maganin damuwa ta, amma sanin cewar wutsiyar raƙumi yayi nesa da ƙasa yasa na miƙa duk lamura na ga Rabbil izzati”.

*Ummi* ba ta ta shi dawowa hankalin ta ba sai da ta ji umma ta fisgeta zuwa harabar asibitin. Cike da mamaki take bin Umma da kallo don kuwa sam bata ga wucewar mummy ba.

Kunkuni take har suka isa gidan su wanda ban samu damar karewa gidan kallo a wancan lokaci ba.

Gida ne matsakaici wanda kai tsaye zan iya kiran sa da gidan masu ƙaramin ƙarfi domin kuwa ɗaki biyu ne cikin gidan irin wanda suke jere ɗin nan, ɗayan ɗakin umma da Abba suke ɗayan kuma *Ummi* ce a ciki.

Farfajiyar gidan yana da ɗan girma sosai dan kuwa a cikin ta akwai toilet da kitchen madaidaita.

Ɓangare guda kuma inda umma take kiwon ƙajin ta.

Ko’ina na gidan tsaf yake kasancewar umma mace mai matukar son tsafta hakan yasa da yawa suke son zuwa gidan ta, kullum gidan cikin ƙamshi mai daɗi yake.

*Wace ce Ummi* ?

*UMMI* ta kasance ɗiya ga malam Lawal kuma ita ce ƴa guda ɗaya wacce suka mallaka tun daga ita ba su sake samun wata haihuwar ba, sam ba su wani damu ba kasancewar sun yi imani ALLAH shi ne yake bayarwa ga wanda yaso kuma ya hana ga wanda yaso, imani da hakan yasa duk suka rayu cikin salama ba tare da wani tashin hankali ba.

 

Malam Lawal ya kasance ɗan kasuwa mai ƙaramin ƙarfi domin kuwa ƙaramin shago gare shi wanda yake sayar da kayan masarufi irin su biscuits, madara da dai sauran su. Kallo ɗaya za kayi wa shagon ka fahimci kawai maleji ake.

Kasancewar sa mai wadatar zuci hakan yasa kullum cikin hamdala da godewa ALLAH yake.

Asalin sunanta *Maryam* sunan Maryam sunan maman sa ne haka ita ma umma sunan mahaifiyar ta ne, ga shi kuma ita ɗaya suka mallaka hakan yasa ta zama ‘yar gata gaba da baya.

Sai dai kuma sam hakan bai sa sun sakar mata linzamin rayuwa ta yi yadda take so da shi ba, sosai idanuwansu yake kanta wajen ganin sun ba ta tarbiyya wacce za tayi alfahari da su ko da bayan ran su ne.

*Ummi* ta yi karatunta tun daga matakin primary school har zuwa yanzu da take gab da da kammmala secondary ɗinta.

Izuwa yanzu *Ummi* tana da shekaru ashirin cif a Duniya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button