HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Murya ƙasa ƙasa tace,”Zan zo jibi in sha Allah”.

“A’a haba ke kuwa ai jibi yayi yawa, ina ma laifin gobe”.

“Duk yadda kike so haka za’a yi Mummy na”.

“Yawwa ‘yar albarka”.

Har sai da suke ɓace wa ganin ta sannan ta shige gida.

Koda suka isa gida wanka yayi ya sauko ya ci abinci, sai da suka ɗan taɓa hira sannan kowa ya nufi ɓangaren sa. Wayar sa ya buɗe kallon ƙyaƙyyawar fuskarta yake babu ko ƙiftawa…murmushi kuwa yaƙi gushewa bisa fuskar sa yana shafa sajen fuskarsa yace, “tabbas ina jin yadda bugun zuciyata ke fitowa da sauri a duk lokacin da na kalle ki, shin wace ce ke? Me yasa nake jin farin ciki a duk sanda na ji ni daf da ke? Me yasa muryaki ke kama da ta sahiba ta? Da irin wannan sambatu bacci yayi awun gaba da shi.

Ko da ya tashi da asuba sosai yayi mamaki ganin yau sam ba ta zo cikin mafarki sa ba, “To ko dai fushi tayi da ni ne?, me yasa ba ki zo ba?”. Share tambayar kawai yayi ya nufi masallaci, ko da aka idar da salla zama yayi a masallaci har sai da gari ya gama wayewa, da sallamar sa ya shiga gida zaune a falo ya iske Mummy, kallon sa tayi cikin so da ƙauna tace,”Abin alfahari na”.

Murmushi yayi sai dai kuma hawaye ne cike fal a  idanuwan sa, ƙarasowa gurin yayi yace, “Mummy na ina ƙwana”.

“‘lafiya kalau ɗan albarka ya ƙarfin jikin na ka?”.

“Alhamdullah sai dai har yanzu ina ji a jikina kamar akwai sauran tabon ciwon abinda na aikata a gare ki cikin rai na, Mummy don Allah ki gafarta min”.

Share hawaye tayi tace,”Na yafe maka ɗana babu abinda ka min don kuwa ni shaida ce akan cewa ba a cikin haiya cin ka kake ba *Son* ka daina damuwa ka ji”.?

“In sha Allah Mummy na”.

Tashi suka yi suka nufi Dinning Table sai da Mummy ta tabbatar ya ci ya ƙoshi sannan ta sarara masa. So yake ya tambayi Mummy lokacin da za ta zo amma gabaki ɗaya kunya ta hana shi, kallon sa tayi tace, “Son ko dai akwai abinda kake so ne? “.

Cikin sauri yace, “bacci dai nake ji Mummy na”.
“To maza tashi ka tafi kayi bacci lafiya kuma ka tabbatar kayi addu’a kafin ka kwanta”.

“In sha Allah Mummy na”. Da haka ya shige ɗakin sa zuciyarsa cike da son ganinta.

Mummy kuwa murmushi tayi tace,”Allah ka cika min buri na akan yaran nan idan shi ne mafi alkhairi”.

*******

Suwaiba kuwa hauka tuburan ce ta kama ta ga ta a ƙwance ba ta iya motsa ko da yatsar hanun ta, idanuwanta kuma ga su dai a buɗe, amma babu abinda take gani da su, ban da faɗe-faɗe babu abinda take.

Sosai abin duniya yayi wa wa Inna Salma yawa ga shi Sale tunda ya fita ya bar gidan har yanzu babu shi babu labarin sa, tana zaune ta fara jiyo sallama jiki na rawa ta mike don kuwa sarai tasan mai wannan muryar, baki na rawa tace, “dama yanzu nake son leƙowa gurin ka na sanar…

Wani irin tsawa ya daka mata sai da ta kusa sakin fitsari a tsaye, gabaki ɗaya idanuwansa sunyi ja, kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar yana cikin matsanancin fushi yace, “Su waye suka aikata min wannan mumunar abin su waye su? tabbas sai na ciyar da su azaba, kuma na shayar da su da ruwan uƙuba wannan alƙawari na ne”. Yana kai wa nan ya fice daga gidan.

Sauke ajiyar zuciya tayi,”Shikenan ai ni a daɗi na tunda za su gane kuren su”.

*******

*Ummi* kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare saƙe saƙe kawai take, gari ne waye wa ta fita ta taya Umma aikin gida, sai dai tana aikin ma tana gyangyaɗi, kallon ta Umma tayi tace, “tashi ki tafi ki ƙwanta kin ji *Ummi* na.” Babu musu kuwa ta tashi ta nufi ɗakin ta, tana kwanciya kuwa bacci yayi awun gaba da ita, ba ita ta farka ba sai dai aka kira sallah la’asar tsabar yadda bacci ya riƙe ta duk yadda Umma taso tayar da ita don tayi sallar azahar ƙin tashi ta yi, ganin haka yasa ta bar ta don kuwa abu ne wanda ba ta taɓa yi ba.

Miƙewa tayi ta fita daga ɗakin cike da mamaki take kallon yanayin garin da alama yamma tayi, murmushi Umma tayi tace,”Ummi na kin tashi lafiya?”.

“Ni…ni…ni dai Umma shi ne ba ki tayar da ni ba?”.

“To kin dawo da wannan rigimar taki ko? kwana biyu da baki nan har na ji sakayau”.

“Umma har kin fara gajiya da ni kike so ki ce ko?”.

“A’a bance ba wasa kawai nake miki Shalelen Faruq”.

“Waiyyo Umma ban kirashi na yi masa bangajiya ba”.

“Kai wannan yarinya to kwantar da hankalin ki shi da kansa ya kira lokacin kina bacci, ba shi kaɗai ba harda Mummyn ku wai ta ji ki shiru kuma kin ce mata za ki zo”.

Sulalewa kawai *Ummi* tayi a gurin tana salati, “Na shiga uku na wallàhi na karya alƙawari Umma na, don Allah lokacin da ta kira me kika ce mata? “.

“Nace da ita kina bacci ai”.

“Hmmm shikenan wallahi ji nayi dama ban yi baccin nan ba”.

Da gudu ta shigo gidan tana ƙwalla kiran sunan ta, ita ma da gudu ta nufi zauren gidan nasu a hanya suka haɗu rungume juna suka yi ko wacce tana sauke ajiyar zuciya kallon ta *Ummi* tayi tace nayi kewar ki”.

“Daina faɗa don kuwa abu ne wanda baki ba zai iya furtawa ba “.

sai da suka gaisa da Umma sannan suka nufi ɗakin ta.
……….
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_

3️⃣9️⃣

 

_*Life has a way of unfolding when you least expect it. You’ll be betrayed by those you trusted. You’ll fall out with so-called friends. Don’t despair. The Almighty is in full control. He knows who should go & who should stay. He will pave a way out for you. Keep going. Trust Him!*_

 

_____Kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yana cikin damuwa saukowa yayi zuwan sashin Mummy, kallon sa tayi tace,”Son ka shirya su Nusaiba suna nan zuwa su duba ka”.

“Kai amma naji daɗi Allah ya kawo su wallàhi nayi kewar little Mummy.”

“Idan mummy kace da gaske kawai ka cire mata little ɗin mana mara kunya kawai.”
“Shikenan zan cire Mummy amma dai kinsan cewa sa’ar Safnah ce ko.?”

“Eh kuma kai ma kasan cewa itace autar gidan mu ba.”?

Dariya kawai yayi yace,”Allah ya kawo su sosai nake son ganin ta sarauniyar son girma, har zai wuce kuma ya dawo yana cewa,”Mummy babu wani baƙo daya zo gidan nan ne yau.?”

“A a babu kana saka ran zuwan wani ne?”

“A a kawai dai na tambaya ne.”

“Dama *Ummi* ce kawai tace zata zo kuma bata samu zuwa ba.. da alama dai gajiya ce dan Umman ku cewa tayi tana bacci.”

Boyayyan ajiyar zuciya ya sauke yace,”Allah yasa dai baccin lafiya ne?”

“Nima na tambaye ta tace”lafiya kalau take”.

Daga nan bai kuma cewa kumai ba ya ɗauke wayar sa ya fita.

Kiran Faruq yayi ya shaida masa gashi nan zuwa gidan shi.

Sosai kuwa yayi farin cikin ganin sa cikin ƙoshin lafiya kamar da, matar sama tayi masa jaje kan abinda ya faru, godiya yayi mata itama sannan suka fita.

Shafe kansa yayi yace,”Da motata zamu fita ko da taka.?”

“Kalli wani gulma kawai mu fita da taka yanda ka dauki ni ka dawo ka ije mata mijinta.”

“Au haka ma zaka ce ko?”

“A a sorry abokina mu fita da taka ɗin dai.”

Saida sukayi tafiya mai nisa sannan yace,”Wai ina zamu tafi ne aboki naga sai sharara gudu kake?.”

“Sayar da kai zan yi na saya tsare da kuɗin.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button