HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Tunda sanyin safe ta tashi tayi duk aikin da tasan itace ke yi ,sannan tayi wanka  ta shirya tsaf abinta cikin riga da zani na atamfa, sosai kayan  suka mata ɗas a jiki gwanin sha’awa, koda zata tafi saida Umma tayi mata nasiha sannan ta ɗauko hijabinta har ƙasa ta sanya, tafiya take cike da natsuwa fuskarta kuwa cike da annashuwa, Allah Allah kawai take ta kai gida saboda yanda jama’a suke kallon ta haka kawai taji ta tsargu.

Sallama tayi mai gadin ya buɗe mata ganin ta yasa ya washa baki, cikin sauri ta rusuna har ƙasa ta gaidashi dan kuwa akalla zasu zo sa’a da Abba.

Sosai Baba mai gadi yaji daɗin wannan girmamawa da *Ummi* tayi masa, harta shiga ciki yana shi mata albarka.

Zaune yake gabaki ɗaya komai jin shi yake babu daɗi,gashi waccan bata zo ba ,ita kuma na cikin mafarki bata sake zuwa ba, Allah ka kawo min mafita cikin gaggawa.

Sallamar tane yasa ya ɗago cikin sauri haɗe da miƙewa tsaya, wani irin ƙayattacan murmushi ya sakar mata wanda saida ta sunkuyar da kanta ƙasa jin yanda tsigar jikinta suka bada yarrrrrrrr

Kome ya tuna kuma cikin sauri ya kuma ya zauna yana wani cin magani kamar ba yanzu ya gama murmushi ba.

Murya a daƙile yace,”Idan ba shigowa zakiyi ba Malama ki koma.”

Jiki a sanyaye ta shigo falon har ƙasa ta duƙa ta gaisheshi, “Ina ƙwana Yaya.”
“Lafiya kalau ya su Umma.?”
“Lafiya kalau suke sunce a gaishe ku”.

“Madalla bara na kira miki Mummy”.

“Zauna abinka ai daga ɗaki na jiyo Muryar ta gani”.

Miƙewa tayi cikin sauri ta rungume Mummy”.

Shafar bayan ta tayi tace,”nayi kewar ki sosai ƴar albarka”.

Janye jikinta tayi ta rusuna har ƙasa itama ta gaishe ta, murmushi mai nuni da tsantsar jin daɗi tayi tana cewa,”Ya su Umman na ku.?”

“Lafiya kawai suke Mummy”.
“To madalla,”.

Kallon ta yake da wani irin shaukin so wanda shi sam bai san yanayin sa ba, gabaki ɗaya yarinyar ta tafi da imanin sa, shanyayyun idanuwan ta suna rikitar dani, labban bakin ta a hankali take sarrafa su yayin magana, murmushin ta kuwa ji nake kamar zan sume, kalar fatar ta a yanzu itace kala mafi tsada dan kuwa kai tsaya ba zaka kirata da ɓaka wuliƙ ba ,kuma ba fara bace ba, meyasa sai yanzu kika shigo rayuwa ta, tsayin lokaci nayi zaman jiran yarinyar cikin mafarki na , abin mamaki kuma zuwan ki kaɗai yasa na fara mancewa da zuwan ta cikin mafarki na muddin zan rinka ganin ki, shin me hakan yake nufi?”.

Duk abinda yake Mummy tana lura dashi saidai har yanzu ta kasa tantance soyayya ce ko kuma dai kawai ɗinbin alkairan ta a gare shi yake jinjina wa.?”

“Ƴa ta tashi mu shiga kitchen mu dafa abinda zamu ci ko?”

“To Mummy na”.

Sosai nake  jin so da ƙaunar irin rayuwar da wa”anan bayin Allah suke dan kuwa babu girman kai ko kuma ɗagawa a tattare dasu,  kalli Mummy ashe da kanta take girki duk tarin dukiyar da Allah ya mallaka mata, saɓanin wasu masu kuɗi wanda ko rabin su ma basu yi ba ,hatta wankin baya yi musu ake, hmm Allah kasa mu  dace, koda suka shiga kitchen sosai lamarin Mummy ya kara bata mamaki,sam matar bata da son jiki da ganda aikin ta take cike da jarumta.

Miƙo min wancan ɗauko min wancan shine kawai a tsakin su,sai kuma idan kika saka wannan zai bada kaza, har suka kammala aikin su babu alamar gajiya a tattara da ita, lemo mai daɗin gaske suka haɗa suka zuba ƙanƙara a ciki, saida suka kammala tsaf sannan Mummy ta ja hannun ta basu tsaya ko ina ba sai ɗakin Safnah, nuna mata toilet tayi tace,”Maza shiga ki yi wanka,ga kaya nan ki duba duk wanda yayi miki ki ɗauka ki saka, babu wanda aka taɓa sawa a cikin su kinji ƴar albarka?”

“To Mummy na”.

Ko da mummy ta fita saida ta tsaya na tsayin lokaci tana ƙarewa ɗakin kallo daga bisani kuma ta shige toilet ɗin…nan ma saida ta ƙarewa toilet ɗin kallo sannan tayi wankan ta duk da dai dama tsaf take abin ta.

Ko da ta fito rasa kayan da zata ɗauka tayi dan kuwa gabaki ɗaya cikin wannan abin babu kayan da suke kasa da dubu ashirin…ganin shiru shiru bata fito ba yasa mummy ta shigo ɗakin bakin ta ɗauke da sallama ganin ta zaune tayi tagumi yasa tayi murmushi tace,Au samun guri kikayi kika zauna?”

Marairaice fuska tayi tace,”Ni..ni..ni dai Mummy wallàhi bansan kayan da zan saka ba”.

Saida ta gama maganar kuma ta tuna cewa bafa Umma bace ba wannan, cikin sauri ta rufe fuskar ta da tafukan hannun ta tana ji ina ma ƙasa ta buɗe ta shige ciki abinta…

Wani jallabiya mai masifar kyau Mummy ta miƙa mata tace,”Maza sanya ki fito yanzu ina jiran ki, wancan shine takalmin da zaki saka , sannan ga ɗan kunne can da gyalan kayan wanda akai zaki ɗaura shi”

“To Mummy na”.

Bayan fitar ta kuwa kallon kayan take tana murmushi dan kuwa sosai rigar tayi kyau.

Saida ta gama shirin ta staf sannan ta ɗauka wannan gyalan ta ɗaura saman kanta..

Fitowa tayi daga ɗakin da sauri jin Mummy tana ƙwalla mata kira yasa ko tsayawa kallon madubi ba tai ba.

Tafiya take cike da izza wanda ita kanta bata san tana yi ba dan kuwa haka Allah yayi ta, shiyasa da yawa suke cewa tana da girman kai da izza, wanda ita kuma sam bata san da zaman hakan ba.

Tunda *Musaddam* ya hango ta ya sake cukalin da yake cin abinci dashi a ƙasa, kallon ta kawai yake babu ƙiftawa tsarki ya tabbata ga Allah mahaliccin kowa da komai,tsara da aminci su tabbata ga Annabi Muhammadu (S A W)”.

Saurin gintse bakin ta Mummy tayi ganin dariya na niman kufce mata dan kuwa magana yake a fili ba tare da sanin sa ba……

SAFNAH ALIYU JAWABI
08136746004
09055560552
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

4️⃣1️⃣

*Don’t jump in to conclusions. Things aren’t always what they seem. Our conclusions may be logical but they may not be true. By refraining from making the wrong assumptions, we can avoid unnecessary pain & conflict. So don’t be too quick to judge & condemn. Instead, be discerning*

_*Allah ya jiƙan ki Umma na*_????????

 

_____Ita kuwa *Ummi* ko lura da yanayin sa ba tai ba gabaki ɗaya hankalin ta yana ga Mummy.

Kujerar dake fuskantar Mummy taja ta zauna.”Sorry Mummy na”.

“Babu komai ƴa ta zauna ga abinci nan ke muke jira”.

“Tom”.

Shi kuwa sun kuyar da kansa ƙasa yayi yana jin yanda zuciyar sa take bugawa da ƙarfin gaske,dafe ƙirjinsa yayi, sannan ya fara cin abinci sa cikin natsuwa.

Da haka har suka gama cin abincin,kallon ta Mummy tayi tace,”Yawwa ƴata wai ya zancan karatun ki?”.

“Mummy yanzu dai nake son farawa”.

“Allah ya taimaka yaushe zaki fara zuwa?”

“Ranar monday nake sa rai in sha Allah”.

“Me zaki karanta?”

Sunkuyar da kanta tayi dan kuwa sam ba zata iya ɗaga ido ta kalli shi ba.

“Kasuwanci”.

“Allah ya bada sa’a”.
“Amin amin”.

Da haka suka canza hira..

Abin mamaki yi nin wannan rana babu inda *Mussadam* ya tafi daga masallaci sai ɗakin sa.

Duk abinda yake Mummy tana kallon sa kuma tana lura da yanayin sa, ita kuwa gabaki ɗaya a tsarge take saboda wani irin kallo da yake mata.

Saida akayi sallar la’asar sannan tayi haramar tafiya, sosai Mummy ta haɗa mata abubuwa kama daga turare man shafawa da kayan kwalliya, sosai tayi godiya ganin irin abubuwan dake cikin wannan leda.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button