HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

“Son zata tafi ka kai ta gida kaji.?”

“Mummy ni fa bana jin daɗi gaskiya”.

“Shikenan bara na kira drive sai ya kai ta Allah ya ƙara sauƙi”.

Cikin sauri yace”A a bara na kai ta”.

Kunshe dariyar ta Mummy tayi har suka fita sannan tace,”Ja’irin yaro ni zaka mayar sakarya ko?” Zaka dawo ka same Ni”.

Cikin mota ma wani irin tafiyar taƙama yake kamar bazai tafi ba, gashi ya saka ɓakar tabarau baka ganin ko kwayar idanuwansa.

Ita kuwa raɓewa tayi da jikin motar saboda wani irin kwarjini da yayi mata,Alla alla kawai take su isa ta fita daga motar a takure take sosai.

Shikuwa juya kan motar yayi zuwa cikin gari, kallon sa take da mamaki saidai kuma sam ba zata iya tambayar sa ba ganin yanda ya haɗa girar sama da ƙasa, sunkuyar da kai tayi tana wasa da yatsun hannun ta amma gabaki ɗaya jikinta banda rawa babu abinda yake.

Sosai yake lura da yanayin ta Murmushi yayi kawai, har suka isa wani babban moll kanta a sunkuye yake , buɗe motar yayi yace,”To ƴar kauye fito an samu A c an wani manne min barauniya kawai”.

Sosai kinjinta ke dukan uku uku so take ta karanci yanayin sa dan kuwa tasan yanda yake da barkwanci saidai kuma tuni ya rigada ya shige ciki, murmushi kawai tayi tace,”Idan ana niman ɓarawan gaske ai kaine dan kuwa gabaki ɗaya ka gama sace ni.”

Bangaran kayan ƙwalliya suka fara shiga saida yasa matar dake shagon ta cika mata mekUp kit sannan suka nufin shagon kaya, nan ma yar kallo kawai ta zama dan kuwa ya hanata magana ta hanyar tsare ta da dara daran idanuwan sa.

Jallabiya masu mattukar kyau da atamfofi aka cika mata akwati dasu haka bangaran takalma.

Ita kuwa banda kallon sa babu abinda take har suka kammala suka dawo cikin mota.

Har ya saka key suka ji ana sallama cikin sauri *Ummi* ta buɗe motar ta fito tsabar murna harda tsalle tace”La Sir Safyan kai ne?”

Murmushi yayi mai nuni da tsantsar farin cikin da yake ciki yace”Haba Maryam yanzu dan Allah kin kyauta kenan kin san halin da nake ciki akan ki amma kuma kika basar da zancen na yanzu hakan daidai ne?”

Sunkuyar da kanta kasa tayi tuni hawaye sun gama cika mata ido ɗago kai tayi da niyyar bashi amsa sai ganin mutum tayi a tsaye ya kafe ta da dara_daran idanuwan sa masu mattukar kyau da kwarjini, gabaki ɗaya ji tayi sam ba zata iya jure kallon tsakiyar idanuwan sa ba wanda tsabar ɓacin rai suka koma ruwan zaiba, ganin ta sunkuyar da kai yasa ya juya ga Safyan yace”Yallaɓai idan magana kake son yi da ita kamata yayi ka same ta a gida sai ku daidai, amma ba’a ana ba”.

Daga hakan ya shige motar sa, *Ummi* kuwa jiki a sanyaye ta buɗe motar, sosai take jin yanda bugun kirjinta ke ƙaruwa”kenan ba so na yake ba? Innalillahi wa inna ilaihi raju’un.”

*Musaddam* kuwa wani irin abu ne yaji ya tukare masa maƙoshi cikin sauri ya parking ɗin motar goran ruwan dake gefan sa ya ɗauka ya kafa a baki saida ya shanye tas sannan ya shiga sauke ajiyar zuciya, gabaki ɗaya launin idanuwan sa sun koma ja, sai fitar da gumi yake duk da karfin Ac dake cikin motar.

Buɗe baki tayi da niyyar magana cikin kakkausar murya ya daka mata tsawa yana cewa”Idan kika kuskuran kika buɗe wannan kazamin bakin naki sai na fasa miki su”.

Sosai ta firgita da ganin yanayin sa shiru tayi tana share hawaye da haka har suka isa gida, buɗe motar tayi da niyyar fita taji ƙofofin motar a ƙulle komawa tayi ta zauna hawaye kuwa kamar an buɗe fanfo.

Saida suka kusa rabin awa a haka tsakiyar kanta taji Muryar sa yana cewa”Yanzu ke dama abinda kike yi kenan tsayuwa da maza a titi ko?”

Shiru tayi dan kuwa gabaki ɗaya tama rasa abin faɗa hakan yasa ya sake jin haushi da takaici dan kuwa yana ɗaya daga cikin abinda ke mattukar ɓata masa rai yayi magana ayi banza dashi.

“Shikenan tunda haka kike so zaki iya tafiya”.

Sai asannan ta ɗago kai “Yaya *Musaddam* sam wannan ba hali na bane ba wannan ɗin Safyan ne kuma malamin makarantar mu ne Tp aka aka turo shi a makarantar mu babu wani halaƙa bayan wannan ka yarda dani”.

“Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sake yace”Tafi gida ina zuwa”.

Jiki a sanyaye ta fita daga motar ta shige gida zuciyar ta cike da ɗin bin tambayoyi wanda take ganin babu inda zata samu amsar su sai gun shi kuma babu damar tambaya, “idan kuwa haka ne dole na nime Maimuna cikin gaggawa”.

Tana shiga ta rungume Umma tana cewa”Nayi kewan ki Umma na”.

“Nima ai ya Mummyn naku take?”
“Lafiya kau tace” A gaishe ki Umma na”.

“Ina amsawa ina shi *Musaddam* ɗin yake?”..

Har zata buɗe baki suka ji sallamar sa,cikin sauri ta shiga daki ta ɗauko mata hijabi ta sanya mata fuskar ta ɗauke da murmushi tace”Umma na wannan hijabin yana miki kyau sosai Allah”.

“To uwar surutu sallah ake kije ki shigo dashi.”

Cikin natsuwa take tafiya,shi kuwa gabaki ɗaya ji yayi ba zai iya ɗauke ido daga kanta ba har ta iso gurin yana binta da kallo,kallo mai cike da tsantsar so da ƙauna, kallon mai cike da girmamawa dan kuwa yarinyar ta cancanci girmamawa saboda jarumtar ta da jajircewa, ita kuwa ganin yayi shiru yasa ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsar hannun ta, sallamar da almajiran da ya saka su kwashi masa kaya ne ya dawo dashi daga duniyar tunani daya shalla.

Da haka suka shiga ciki tana gaba yana binta a baya, cikin girmamawa ya gaisa da Umma sannan ya sake jaddada godiyar sa akan hidimar da suka yi dashi.

“Ai babu komai domin kuwa alkhairi da sharri duk abin bibiya ne muddun kayi su tofa babu shakka sai sun dawo gare ka fatan mu kawai Allah ya bamu ikon aikata alkairi”.

“Amin Umma na”.

Da mamaki *Ummi* ta ɗaga kai tana kallon sa daidai lokacin shima ya ɗago kansa kallon juna suke ido cikin ido gabaki ɗaya yau ji tayi kamar ya saka mayan ƙarfe ya sarƙafe mata idanuwan ta a cikin nashi so take ta janye idanuwan ta amma ina sai ma wani lumshe idanuwan ta take.

Janye idanuwan sa yayi ganin Umma a wajan amma kam sosai yake jin daɗin kallon ta, ita ɗin ta daban ce komai nata mai kyau ne, idanuwan ta masu mattukar kyau da sheƙi,hancin ta madaidaiciya bakin ta dan ƙarami .

Komai na ta abin burgewa ne.

Saida ya sha ruwan da suka kawo masa sannan yayi haramar tafiya, sallama yayi wa Umma da alƙawarin gobe zai tafi har shago ya duba Abba.

Rakashi tayi zuwa bakin ƙofar gidan su, nan ma tsayawa yayi yana kallon ta can kuma yace,”Zan tafi kuma saura idan wannan sakaran malamin naku ya zo ki fita, Wallàhi sai na karya miki wannan kafafuwan naki kinji na faɗa miki kenan”.

“Ni..ni..dai dama ai ba cewa nayi zan fita ba bare a min albishir na mayar dani gurguwa na rasa mijin aure”.

Ɗago kai yayi cikin sauri dan kuwa maganar tazo masa a bazata, ganin yanda ya waigo a firgice yasa tayi saurin shigewa gida harda haɗawa da gudu.

Murmushi kawai yayi ya shige motar sa, har ya isa gida tunanin maganar ta yake banda dariya babu abinda yake,”Wannan yarinyar akwai shiririta amma zan gyara miki zama ne nan bada daɗewa ba……

Mu haɗu a page na gaba dan ganin yanda al’amarin Suwaiba Inna Salma..Sale da kuma mahaifin su zai kasance..

Love you all
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button