MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idiriss Musa_
4️⃣2️⃣
*A delay is not a denial, it is only a sign that you need to have peace, patience & trust that in perfect timing what you want will come to you. Sometimes you are delayed where you are because Allah knows there’s a storm where you’re headed. Be grateful. Trust Him.*
_____Ita kuwa koda ta shiga gida ɗakin ta ta shiga cikin sauri tana zuwa ta kwanta banda murmushi babu abinda take, hannun ta riƙe da pillow sai juyi take tana lumshe shanyayyun idanuwan ta.
Koda ta idar da sallar magrib bata tashi a gurin ba saida aka kira sallar isha’i tana idarwa sai ga yaron maƙotan su ya shigo bakin sa ɗauke da sallama amsawa tayi tace”Mai ƙaton kai lafiya dai?”
“Wallahi ki daina ce min mai ƙaton kai dan kuwa kai na iri ɗaya ne da taki”.
Dariya take sosai tace”Anji yanzu faɗa min menene?”
“Wani ne a waje wai Safyan yana kira k….da wanin irin gudu ta shige ɗaki harda banko kofar haɗa da saka saƙata tana cewa”Yanzu Sir Safyan duk kallon mai hankali da nake maka ashe alkasin haka ne? Yanzu saboda Allah duk gargaɗi da aka min baka ji ba? So kake a karya min ƙafafu na kenan? Aikuwa ba zan fita ba koda kuwa zaka kwana a gurin yasin haba dai yanzu ɗan kafar da nake dashi ma sai an min hassadar sa, kai jama’a.”
Sauke ajiyar zuciya tayi tace”kai amma nima dai ina da shiririta da yawa ai ba agaban shi akayi maganar ba, amma kuma duk da haka ni ba zan fita ko ina ba”.
Umma kuwa da mamaki take kallon Kofar ganin yanda ta banko ƙofar da karfi yasa tace”Kai Mubarak lafiya kuwa?”
“Umma nima dai bansani ba saƙo kawai aka bani cewar ta zo ana kiran ta shine kuma naga ta ruga ɗaki da gudu”.
“Saƙo kuma injiwa kenan?”
“Wani wai nace mata Safyan”.
“Safyan kuma? Jeka kawai kace masa tayi bacci kaji?”
“To Amma Umma saida shafi”.
“Ƴawwa saida safi Mubarak”.
“Kofar dakin take bugawa tana kiran sunan ta”Ke *Ummi* na menene haka wai ki buɗe kofa”.
“Umma wallàhi ba zan fita ba idan na fita Yaya *Musaddam* yace”Zai karya min ƙafa ta kuma ni bana so na zama gurguwa,kuma ai kema na san zakiyi kuka idan na zama gurguwa ko Umma na?”
Tintsirewa da dariya Umma tayi saida tayi mai isarta tace”Aikuwa gara da yayi miki haka kuma ko ni kike fita ko kuma tsayawa da wani sai na faɗa masa”.
“Ayyah mana Umma na ai gashi nan babu inda na tafi ko?”
“Ƴawwa to ki kwanta kiyi bacci sai da safi kinji ƴar albarka?”
“To Umma na”.
Ko da Abba ya dawo Umma ta faɗa masa dariya yayi sosai shima dan kuwa shiriritan *Ummi* yana nima wuce gona da iri.
*************
*Musaddam* kuwa yana komawa gida ɗakin sa ya nufa yayi wanka ya sanya ƙananan kaya sosai kayan suka amshi jikin sa, babu abinda fuskar sa ke fitarwa sai tsantsar farin ciki da annashuwa, koda Mummy ta kalle shi hamdala kawai tayi a zuciyar ta dan kuwa babu shakka wannan farin cikin nasa yana da nasaba da kasancewar sa a tare da *Ummi*.
Zuba masa abinci tayi amma ina kamar ma hankalin sa baya ga abincin da yake ci, kiran sunan sa tayi tace”Ina ta yaka farin ciki ɗana”.
“Murmushi yayi yace”Nagode Mummy na ai lafiya yayi fatan mu Allah yayi mana rowan cuta”.
Ganin bai fahimci abinda take nufi ba yasa ta basar dan kuwa tasan babu inda wannan ɓoye_ɓoyan nasa zai tafi dole dai ita zai fara sama da zancan *Ummi*.
Da haka har suka gama cin abincin koda ya dawo daga sallar magrib gabaki ɗaya ji yayi sam bai gamsu da cewar idan Safyan yazo ba zata fito ba ,hakan yasa ya shirya tsaf ya nufi gidan su, saida kuma ya tafi ya rasa ta ina ma zai fara”Kai ai da kunya na aika kiran ta cikin daran nan”.
Can kuma wata dara ta faɗa masa, kiran ɗaya daga cikin yarin dake wasa yayi yace “Sannu ko yaro”
“Ƴawwa”
“Dan Allah dan shiga cikin gidan nan ka kira min *Ummi* kace mata Safyan yana kiran ta”.
“Au kace gun mai ƙaton kai kazo?”
“Mai ƙaton kai kuma?”.
“Eh mana haka take kira na shiyasa nima nake kiran ta haka”.
“To ita kace mata Safyan ne tayi maza ta zo”.
Koda yaron ya shiga ciki kuma sai gabaki ɗaya yaji wani iri dan kuwa idan aka samu akasi ta fito bayan duk gargaɗi da yayi mata tofa ran sa ne zai ɓaci.
Haka dai ya tsaya, ganin yaron ya fito yana dariya yasa yayi saurin riƙo hannun sa yana cewa”Kai mai ƙaton kai tana ina?”
Dariya sosai yaron yake kafin daga baya gace”Kai ma mai ƙaton kai kake kira na kenan to na fasa baki saƙon”
“A a yi hakuri kaji wasa kawai nake maka”.
Koda yaron ya bashi labarin abinda ya faru tun daga shigewar ta daki har maganar da take faɗawa Umma duk saida yaron ya faɗa masa,sosai yake Dariya harda riƙe ciki,komawa yayi cikin mota ya dauko kuɗi ya bawa yaron da kyar yaron ya ƙarɓa yayi masa godiya.
A cikin mota kuwa tamkar zararre haka ya koma banda dariya babu abinda yake ganin hakan bai masa ba yasa ya faka motar ya cigaba da dariyar sa Sannan ya nufi gida.
********
Inna Salma kuwa abin duniya yayi mata yawa ga ciwon Suwaiba sai gaba gaba yake kana shigowa gidan ba zaka iya koda jan numfashi ba saboda wari dake tashi a gidan,ga mafarkai mara daɗi da take yawan yi kullum cikin bata tsoro ake .duk yanda mahaifin su yaso warkar da ita ta hanyar amfani da siddabaru abu yaki aiki,haka yana ji yana gani ya barta saidai kuma babu komai a zuciyar sa sai muradin ɗaukar fansa wanda gani yake idan ba ya kawar da wanda sukayi sanadiyyar jefa ƴaƴan sa cikin wannan halin bane ba sam ba zai huta ba.
Yau ma kamar kullum zaune yake cikin ɗakin tsafin sa,wasu irin maganganu yake yana tofawa jikin wannan madubin, kamar kullum yau ma tsawa madubin yayi ya tarwatse ba tare da hoton ko da mutum ɗaya ya baiyana ba.
Cikin takaici ya miƙe yana wani irin gurnani kamar zaki yace”Zanyi tafiya wanda nisan tafiyar ta yakai shekara ɗaya wanda a cikin ta sai na yi tsayin wata babu ci babu sha kafin na samu damar gane wa idona ahalin da suka haɗu suka min wannan mumunar aiki, amma kafin nan bara na sake zuwa ga wancan sakaryar ko yau zata samu damar faɗa min”.
Koda ya tafi hannu yasa ya rufe hancin sa sannan yace”Bantaɓa ganin asararriya kamar ki ba Salma yanzu ace mutanan da suka aikatawa ƴar ki wannan mumunar aikin ace ki kasa koda tuni sunan mutum ɗaya daga ciki?”
Gyara zama tayi wanda yanzu da ƙyar take iya mikewa ma tace”Ka yarda dani ni kaina bansan abinda ke damu na ba kafin ka shigo cikin gidan nan sai naji na tuna da komai harda gidan da suke zaune, abin mamaki kuma da zarar ka shigo sai naji na mance komai abin yana damu na sosai”.
Tsaki kawai yayi ya fice daga gidan yana ɗura mata ashar.
********
Sale kuwa cikin gari ya nufa bashi da abin yi a koda yaushe sai niman yafiyar Allah sosai yake dana sanin abinda ya aikata har zuwa yau wanda babu na kirki acikin ta, cikin ikon Allah kuwa ya samu Masallaci wanda yake kwana a ciki Allah cikin ikon sa suka aminci ya rinka kwana a ciki bayan ya faɗa musu labarin sa, a cikin masallacin ana koyar da karatun Alkur’ani nan da Sale ya dukufa niman ilimin Addini ba ji ba gani.
Babu comment ina ga kamar daga nan zan dakata.
Love you all
S A JAWABI
08136746004
09055560552
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????