MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
*_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga marubuci Musaddam Idiriss Musa_*
4️⃣3️⃣
_*You don’t have to discredit someone to feel good about yourself. Be the one who fixes something that’s not right in others without telling the whole world about it. Do things quietly away from the limelight. Let your heart smile at your deed! And the Almighty knows!*_
_____ Washa gari shirin sa yayi tsaf dan kuwa tunda wuri yake so su fara aikin sam baya so aikin ya ɗauki lokaci mai tsayi.. bayan sun gaisa da Mummy yake tambayar ta yaushe ne lil Sis ɗin sa zata dawo,? a nan ne take shaida masa ai zuwa nan da karshin wata zata dawo, sosai yayi farin ciki sannan yace”Mummy zamu fita addu’ar ki kawai nake buƙata mummy na”.
“Addu’a kullum cikin yin sa muke kuma muna da yaƙinin Allah zai amsa mana muddun aka guji aikata abu huɗu ,na farko saɓa alƙawari, cin amana,zamba cikin aminci, karya a inda ake saka ran jin gaskiya daga bakin ka. Idan har ka gujewa wannan babu shakka addu’a ta bata da shamaki a gunka kamar yanda Allah ya sanar damu, Allah ya kiyaye hanya kaji ɗana”.
“Amin Amin Mummy amma mesaya cikin wa’ancan sharuɗan baki sanya shirka da zina ba?”
“Hmmm ban saka su bane sabida da yawan mutane sun san hukuncin su kuma suna ƙoƙarin ganin sun nisanta kansu dashi. wannan kuma ganin sa suke kamar aikata shi ba komai bane ba alhalin wannan ma yana ɗaya daga cikin manyan laifuka wanda kai katsaye zasu shigar da bawa cikin halaka amma sam hankalin mu baya gushewa daga aikata su.”
“Allah Nagode maka daka min kyauta mafi girma a rayuwa ta sai na dawo.”
“Allah ya bada sa’a.”
( “`shin menene zai tabbatar da soyayyar uwa ga ƴaƴan ta?
shin ta yaya ake gane uwa tana mattuƙar son ƴaƴan ta?
da yawa sun ɗauka sayawa yaro kaya ko kuma abin more rayuwa shine Soyayya, ana fahimtar soyayyar uwa ne ta hanyar jajircewa akan ƴaƴan ta dan ganin sun tarbiyayyan tu, ta hanyar sanin haƙin Allah akan su da kuma hanyar da zasu bi dan ƙarsu ƙyetare hakkokin Allah, uwa ta gare itace mai keyayye sallar ɗanta, uwa ta gare itace ke lura da shigewa da ficewar ɗanta, uwa ta gare Itace ke ƙiyaye duk wani abinda zai saka ɗanta ya kaucewa hanyar Allah, uwa ta gare itace ke kama hannun ɗanta tayi masa alwala sannan tayi nata a gaban shi ta yanda zai rinka lura da yanda take yi har shima ya kai lokacin da zai iya da kansa, uwa ta gare itace mai zaunar da ɗan ta ta kwaɗai ta masa daɗin Aljana da kuma abubuwan dake ciki ,uwa ta gare itace ke zaunar da ɗan ta ta nuna masa yanda take cike da tsoron saɓawa Allah sabida tana tsoron shiga wuta..uwa ta gari itace ke zama ta nuna wa ɗan ta falalar dake cikin azumi da kuma asarar dake cikin rashin yin sa.
Shin ba zakiyi farin cikin ba a ranar da kiyama ta tsayu ganin yaron ki a kusa dake yana mai alfaharin kasancewar ki uwa a gare shi ba?
Shin yaya zakiyi lokacin da kiyama ta tsayu ɗanki yana mai jin bakin ciki da takaicin kasancewar ki uwa a gare shi?
Shin ina wannan kayan wasan da kike saya masa a lokacin da yake duniya? Shin ina wannan motar wacce ake yayi wanda kika saya masa saboda kar yaji kunyar shiga cikin abokan sa?
Allah yasa mu dace duniya da lahira.“` ????????????
Koda ya fita bai tsaya ko ina ba sai shagon Abba wato mahaifin *Ummi* cikin girmamawa ya gaishe shi,sosai Abba yayi farin cikin ganin sa, gabaki ɗaya ma rasa abin da zai bashi yayi tsabar farin cikin da yayi na ganin sa ko babu komai mutum mai karamci mai taimakon al’umma ai abin girmamawa ne bare kuma wannan wanda ya zama kamar ɗan uwa a gare su yanzu.
Bayan komai ya lafa yake sanar dashi abinda ya kawo shi.,”Wato Abba wata alfarma nake nima ko kuma nace abune daya rataya a wuya na wanda idan har kuna min kallon ɗa wanda ya kasance naku kamar yanda nima nake kallon ku matsayin iyaye na tofa babu shakka wannan kamar hakki ne akai na kamata yayi kawai na fara aiwatar da abinda ke rai na,amma na zaɓi niman izinin kane saboda wani dalili nawa, Abba so nake ku tashi daga wannan gida ku koma kusa da gidan mu ga makullan gidan a cikin mota, idan kuma nan anguwar da kuke, kuke so saboda hali na sabo shima babu damuwa za’a rushe shi ayi muku irin wannan wanda ke kusa da namu, baya ga haka an buɗe maka shago a cikin babbar kasuwa acan zaka fara kasuwanci da yardar Allah, Abba kin amincewa da buƙatata yana nufin baku ɗauke ni ɗa gare ku bane kuma sam hakan ba zai min daɗi ba babu godiya a tsakin mu addu’a kawai muke buƙata Abba na.”
Gabaki ɗaya Abba ji yayi ƙafafuwan sa sunyi sanyi wani irin Fargaba haɗe da farin ciki na suka masa dirar miƙiya lokaci ɗaya dan sam bai taɓa zaton wannan kyauta ko kuma alkiri zai zo gare shi ba,duk da kuwa daidai da rana ɗaya bai taɓa cire rai daga rahamar Allah ba.
Sauke ajiyar zuciya yayi yace,”duk da kace babu godiya amma zanyi maka addu’a daga nan har karshan rayuwa ta wannan alƙawari nane, saidai game da zancan zaɓin daka bani zan samu ita Umman ku sai muyi shawara in sha Allah zaka ji duk yanda ake ciki in Sha Allah”.
Sosai Musaddam ya jinjina karamci irin na wannan tsoho mai tarin natsuwa da kamala.
Abba kuwa kasa tabuka komai yayi tsayin ranar gabaki.
Haka dai ya tafi gida ya shaidawa Umma abinda kenan,itama dai tsakanin farin ciki da kuma akasin sa take dan kuwa mutanan duniya sam ba’a iya musu yanzu sai gari ya ɗauka da sunyi kwaɗanyi ko kuma roko,kin amincewa kuma yana nufin mayar da hannun kyauta baya wanda Allah kansa baya son haka, a karshe sai suka yanke shawarar yin tsayuwar dare da miƙawa Allah zaɓi duk wanda zuciyar su tafi amince dashi zuwa safe tofa shine zaɓin Allah.
Haka kuwa akayi tsayin dare babu wanda ya rintse abin mamaki duk sun lamunta da batun karɓar gida da safe saidai kuma a rusa wannan a gina musu wani shine yafi tsayuwa musu a rai.
Kusan yamma Abba ya kira shi ya shaida masa hukuncin da suka yanke, sosai *Musaddam* yayi murna da jin wannan zance,sai a lokacin yake sanar da Mummy,itama sosai tayi murna kuma a nan ne take sanar dashi kudirin ta na buɗewa Umma shago wanda zata rinka sayar da kaya irin su zanin gado atamfa da lace haka kaya dai ma mata, tsabar murna *Musaddam* jiyaye kamar ya rungume ta, sai addu’a yake mata yana ƙarawa.
*Ummi* kuwa jin wannan batu yasa ta shiga tashin hankali gani take kamar da gaske ba sonta yake ba tunda gashi suna niman biyan su taimakon da suka musu ta hanyar canza musu gida da buɗewa iyayan ta sabbin shaguna, cikin kwana uku kacal ta rame tayi baki.
Maimuna kawai ta faɗawa damuwar ta, “Haba ƙawa karki ce haka ni har cikin rai na ina jin cewa duk abinda *Musaddam* yake saboda son da yake miki ne wannan babu tantama akai”.
“Ban yarda ba dan kuwa yanzu ko ta kaina baya bi ko gaishe shi nayi amsawa yake a dake baki gani ba ke dai.”
“Ki daina kuka to yanzu menene shawara?”
“Shawarar da zan baki shine ina wannan Safyan ɗin kawai ki kira shi kice masa ya zo gidan ku, karki kira shi sai kin tabbatar *Musaddam* idan yazo sai muga yanda zai yi idan har bai nuna damuwar sa irin na wancan lokacin ba tofa saidai kawai muyi haƙuri”.