HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

“Kina ganin wannan shawarar shine daidai?”

“Eh a yanzu gaskiya shine kawai mafita ki daina damuwa kinji ƙawata?”

“In sha Allah amma ki sani ina mattukar son sa kuma kema shaida ne akan haka”.

_SAFNAH ALIYU JAWABI_✍️✍️✍️✍️
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Marubuci Musaddam Idiriss Musa_

4️⃣4️⃣

*It might not be obvious to you now, but greater things are being planned for you. You’re always given the test before the reward. You’re always given the struggle before the strength. Hardships always come before the ease. Keep trusting the Almighty. The blessings will follow.*

 

 

_______Ganin yanda abubuwa suke tafiya yasa *Ummi* da  iyayan ta suka koma ɗaya daga cikin gidajan mahaifin  Maimuna kafin a gama nasu, duk da kuwa sam ba haka *Musaddam* yaso ba haka ya hakura suka koma can.

Bayan ta dawo daga makaranta agajiye take dan tafiya ma da kyar take yin sa daidai kofar gidan su taga motar sa alamar dai yana ciki dan haka yake yi kullum sai ya zo ya duba yanda aikin ke tafiya.

Ciro wayar daya saya mata tayi ta kira Safyan kira ɗaya aka daga saida ta gama kiran sa sannan ne kuma jikin ta yayi sanyi gashi babu halin sake kira tace”masa kar ya zo, haka dai ta haƙura ta shige gidan.

Can bayan an gama magrib suna zaune da Abba a kofar gidan suna hira yanda kasan abokan juna, dan kuwa Abba mutum ne mai saukin kai, shi kuma *Musaddam* akwai saurin sabo haka yasa suke jin kamar sun yi Shekaru masu yawa da juna.

Tashi *Musaddam* yayi da niyyar ɗauko wayar sa,haka kawai yaji ƙirjinsa na bugawa da ƙarfin gaske,dafe gurin yayi a hankali yana murzawa,abin mamaki maimakon yayi sauki kuma sai ƙara tsanan ta yake hakan yasa ya zauna a motar dan ya ɗan samu sauƙin abinda yake ji.

Kamar ance ya ɗago kai sai ganin mutum yayi azaune a dakalin ƙofar gidan da fari ya ɗauka Maimuna ce dan kuwa har an saka ranar aura ta, wucewar wani ɗan acaɓa yasa ya hango wacce take tsaye tana murmushi.

Innalillahi wa inna ilaihi raju’un kawai yake maimaitawa tsabar ruɗani daya tsanci kansa a ciki wani irin ciwon kai ne yaji yayi masa dirar miƙiya, har wani jiri yake gani,dafe kansa yayi yace”Me hakan ke nufi *Ummi* ce waccan ko dai gizo take min kamar yanda ta saba min wasu lokutan?”

Fita daga motar yayi ya dawo inda Abba yake zaune yana jiran sa yace”Abba na muje na rakaka zan tafi gida na mance akwai sakon da Mummy ta bani na kai kuma shaf na mance”.

“Ashhhha yaran zamani kenan ko me kuke tunani sai Allah shikenan muje”.

Haka kuwa akayi har ƙofar gidan ya raka shi,sanda ya tabbatar da cewar *Ummi* ce wani irin farin haske ya gani ya gifta ta gaban idanuwan sa,cikin dakiya ya raka Abba har zauran gidan Sannan ya fito, miƙa masa hannu Safyan yayi yace”Barka da wannan lokaci babban yaya”.

“Yawwa barka fatan kana lafiya?”.
“Lafiya kalau alhamdullahi gaskiya na gode babban yaya daka bani shawarar zuwa gida gashi cikin yardar Allah mun daidaita Allah ya kara girma”.

“A a ai babu damuwa nagode saida safe”.

Ko kafin *Musaddam* su gama magana da Safyan tuni.
gaban hijabin ta ya jiƙe da ruwan hawaye, kuka take sosai har da sauke ajiyar zuciya motar sa na barin Kofar gidan ta shige gida da gudu faɗawa jikin Umma tayi tana kuka kamar ranta zai fita, fitowa daga ɗaki Abba yayi yace”Dama aikawa zanyi yanzu a kira ki waye na ganki tsaye dashi a Kofar gida *Ummi* na kuma kin shigo gida kina kuka.

Kallon Abba tayi ta sauke kai dan kuwa ba zata taɓa iya faɗa masa dalilin zuwan Safyan kofar gidan su ba, haka ta zauna tayi ta kuka ganin haka yasa Abba ya shige ciki abin sa dan kuwa rigimar ta ta fara yawa haba dai.

Ganin ya shige ciki yasa ta jawo ta jikin ya tace”Faɗa min*Ummi* na menene?”

“Umma ba sona yake ba wallahi babu so na ko na minti ɗaya cikin zuciyar sa Umma mutuwa zanyi na faɗa miki idan har ba shina aura ba babu wanda zan aura a cikin duniyar nan”.

“Yanzu dakata faɗa min abinda ya faru Kinji”.

Nanfa ta zaiyana wa Umma duk yanda akayi, banda salati babu abinda Umma take jin salatin da Umma take yasa Abba fitowa da sauri nan dai shima ta faɗa masa abinda ke faruwa, jinjina kai kawai yayi ya shige ɗakin da suke abin shi.

Ganin haka yasa Umma ma ta shige dakin abin ta aka barta ita ɗaya a tsakiyar gidan.

Haka ta zauna tayi ta kuka kusan awanni ganin dare ya fara yi ne yasa ta tashi itama ta shige ɗakin.

Yanda taga rana haka taga dare.

Tsabar kuka har idanuwan ta sun kumbura.

Wani tashin hankali kuma daga Abba har Umma babu wanda ya sake bi ta kanta.

******
Allah ne kaɗai ya kai shi gidan dan kuwa gabaki ɗaya ba a cikin haiyacin sa yake ba ,zaune ya samu Mummy a falo tana waya ganin yanda ya shigo gida a galabaice yasa ta miƙe cikin sauri ta tare shi ,abin mamaki hawaye ne sosai a fuskar sa bakin sa kuwa banda kiran suna *ummi* babu abinda yake sosai mummy ta shiga ruɗu ganin halin da yake ciki hakan yasa ta kira Umma take tambayar ta abinda ke faruwa daidai lokacin ne Umma ta shige ɗaki, sanda ta gama zai yana mata abinda ke faruwa hamdala tayi sannan suma ta shaida masu halin da shima ya dawo gida a ciki, sosai duk zuciyoyon su suka cika da tsantsar farin cikin faruwar wannan al’amari, shawarar da mummy ta bayar na kin sanar dasu komai yasa basu faɗawa *Ummi* abinda ke faruwa ba.

Washa gari kuwa bayan *Ummi* ta tafi makaranta Mummy ta zo gidan suka tsara abin su ,daga nan mummy bata tsaya ko ina ba sai gidan su wato gidan iyayen ta faɗa musu abinda ke faruwa tayi sannan ta hane su da karsu faɗawa ɗaya daga cikin yaran gidan abinda ke faruwa gudun kar su faɗawa shi Musaddam ɗin.

Nan take ta fito da A T M ɗinta ta damƙa a hannun ƙanin ta tace” zuwa gobe zaku tafi gidan su dan nima wa ɗanku  Auran ta duk abinda ake ciki sai a sanar dani, dan Allah karku bar gidan har sai kun tsayar da lokaci”.

“In sha Allah, Allah dai ya tabbatar da alkairi”.

A tare duk suka amsa da amin.

Unin wannan rana haka zuciyoyi biyu suka kasance cikin fargaba da tunanin juna, a nashi ɓangaran tuni ya yanke shawarar ba zai sake yarda shi da ita su haɗa ko da hanya bane ba, zai tsaya har zuwa lokacin da zai haɗu da ita asalin budurwar tasa na cikin mafarki wanda dama can kama take da ita ba ita bace ba,”dan kuwa da itace ba zata taɓa tsayuwa da wanin sa  ba duk da kuwa yayi mata gargaɗi”.

Ita kuwa tunanin wance yake so take,”Kenan bani yake so ba, shi sam baya jin abinda nake ji kenan? Wacce yake so ɗin dame ta fini to? A hanya ita ɗaya take maganar ta, kiran sunan ta da Maimuna tayi ne yasa taja burki ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya, ƙarasowar ta keda wuya tace”Karki ce min komai domin kuwa kin cuce ni kin gama da rayuwa ta, asanadin ki nayi rashin wanda nake so da ƙauna, asadanin shawarar ki ,kalli inda na tsanci kai na, Na gane *Musaddam* bani ce yake so ba dan kuwa sake jinjinawa Safyan yayi maimakon yaji haushin sa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button