HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Kuka take sosai gashi kuma bakin layi ne duk mutane sai kallon su suke, hakan yasa ta jata suka koma gefe,kallon ta tayi tace”Yanzu ba kamata yayi ki gode min ba? Shin asanadin shawara ta baki fahimci inda ya dosa ba? Wannan bawan Allah bai taɓa furta kalmar so a gare ki ba, meyasa kika ganin laifin sa yanzu dai bai nuna kishi akan ki ba,? Kalla *Ummi* na kamata yayi ki godewa Allah da kika gane hakan tun yanzu, amma dai ki koma ki zauna ki yi tunanin akan abinda na faɗa miki kinji ki kwantar da hankalin ki.”

Share hawayan ta tayi tace”Shikenan amma ki sani bani da wani miji a duniyar nan face shi.

Da haka tayi gaba abinda.

_Safnah Aliyu jawabi_✍️✍️✍️
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga marubuci Musaddam Idiriss Musa_

4️⃣5️⃣

“_*You need to quit worrying about what people think. Honestly, it doesn’t matter. They’re entitled to their thoughts. At the end of your life, you’re not going to stand before people and give an account of what you’ve done. You’re going to stand before the Almighty.*_

 

 

_______Washa gari kuwa tunda sanyin safiya ƙannan Mummy suka nufin gidan su *Ummi* zaune take Kasancewa ranar asabar ne   haka yasa ta shimfiɗa tabarma ta kwanta a tsakar gidan, “Abin mamaki sai kaiwa da komo wa Abba da ya faruq suke cikin gidan nan ko dai Aunty ta haihu ne?” “Kai a’a da haihuwa zatayi da babu shakka za’a faɗa min ai”.

Haka dai ta cigaba da wasa da wayar hannu ta, can sai ga kiran Safyan da kamar ba zata ɗaga ba sai kuma wani zuciya yace”ta ɗaga dan taji abinda zai faɗa mata, da sallama a bakin ta ta amsa, kwantar da murya yayi jin tayi shiru yace”Fatan kina lafiya?”
“Lafiya”.

“Dama magana nake so muyi”.

“Magana kuma wani irin magana kenan da sanyin safiyar nan?”
“Dama gani nayi tunda mun daidaita kanmu ai Kinga babu amfanin tsayawa wani ɓata lokaci shiyasa na faɗawa iyaye na dan haka daga nan zuwa ko wani lokaci zaki iya ganin su.”

Aikuwa nan fa *Ummi* ta shiga masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba ,a ƙarshe ma buga wayar tayi da kasa tana dafe kanta sabida sara mata da yake.

Umma kuwa tashima tayi ta shige daki dan kuwa tana zaune a kusa da ita tana jin duk abinda ke faruwa,tana shiga ɗaki ta tintsire da dariya, “Kai wannan yarinyar da wawta take ko shi kuma wayar laifin me yayi mata oho”.

Sosai wannan sauyi na iyayan ta yake mattukar razana ta.

Zama tayi ta haɗa kanta da guiwar ƙafa sai jin sallamar Abba tayi  Muryar sa ɗaukar da tsantsar farin ciki ,da murmushi ya kalle ta yace” *Ummi* ƴar albarka zo nan ki zauna a kusa da ni,ko kuma kafin nan ki kira min Umman ki, kai ma faruq samu guri ka zauna kaji,?”

Saida kowa ya hallara sannan Abba ya gyara zama  ya matso da goron dake gaban Faruq yace”Maza ɗauki ɗaya ki ci kuma kiyi bismilla kafin ci,sannan kafin ki haɗeye kiyi alhamdullah ma’ana godiya ga Allah mahaliccin kowa da komai Kuma mai tsara duk kan abinda yasa babu mai hana shi.”..

Gabaki ɗaya *Ummi* jitayi gabaki ɗaya jikin ta ya ɗauki rawa,banda zufa babu abinda take ganin yanda ya Faruq yake kallon ta hakan yasa tayi saurin ɗaukar karami daga ciki ta saka a baki.

Saida Abba ya tabbatar ta haɗe sannan yace”Madalla mama na, kafin na fara magana ina so na tambaye ki wata alfarma shin zaki min?”

Murya na rawa tace”Abba babu niman alfarma ko shawara Abba na umarni kawai zaka bani ni kuma nayi alƙawarin zanyi maka duk kan abinda ka umarce ni dashi”.

“Yawwa mama na Allah yayi miki albarka”.

A tare duk suka amsa da Amin sannan yace”Wannan goro da kika gani ba goron kowa bane ba face naki wato goron auran ki.”

Innalillahi wa inna ilaihi raju’un girgiza kunnuwan ta *Ummi*  ta shiga yi sabida lokaci ɗaya jin ta ya ɗauke kamar an buga mata abu haka taji, wasu irin zazafafan hawaye ke zuba a idanuwan ta,kallon ta Abba yayi yace”Karki mance yanzu kika ɗauke alƙawari dan haka cikawa kuma ya rage gare ki.”

Tashi yayi ya shige cikin ɗakin yana kunshe dariyar sa.

Kallon Umma tayi da idanuwan ta wanda tuni suka koma ja tace”A a Umma na ki zauna karki tafi dan kuwa tafiyar ki daidai yake da bugawar zuciya ta,in dai wannan ɗin yayi muku kuma kun tabbatar shine zaɓin ku a gare ni?”

“Eh wannan ɗin shine zaɓin mu *Ummi* na ki daure kinji wannan ma ki ɗauka jarabawa ne daga Allah kinji?”

“In sha Allah Umma na zan yi muku koda kuwa hakan yana nufi..rufe mata baki tayi cikin sauri tace”karki yarda mahaifin ki yaji wannan batu dan kuwa ba zai ji daɗi ba mun gode da kika kasance ɗiya ɗaya tal wacce take tamkar goma a gare mu Allah yayi miki albarka”.

Gyara zama ya Faruq yayi yace”In sha Allah ba zaki taɓa yin dana sanin amincewa da wannan zaɓin ba shalele na”.

Wannan rana tashin hankalin da *Ummi* ta shiga mai karatu na bar muku kuyi hasashan sa a zuciyar ku.

Koda garin Allah ya waye bata fito ba kuma iyayan ma basu matsa mata ba.

Tana kwance ta fara jiyo Sallamar jama’a a gidan kuma da alamu dai mata ne, leƙowa tayi dan ganin ko su waye kuma me ke faruwa.

Wanin irin sara mata taji kanta yayi kamar zata fashe ganin matan ɗauka da akwatunan aure da yawa kamar za’a buɗe shago dasu.

Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara zarya a kuncin ta” kenan sabida kuɗi suka bada ni ba tare da amincewa ta ba kuma bayan sun san wanda nake so?” Kome ta tuna kuma tace”ina dole dai akwai abinda suka gani wanda suke saka ran shine daidai a rayuwa ta Iyaye na ba makwaɗaita bane ba sam”.

Haka ta kwanta tana ta sauke ajiyar zuciya har barci ɓarawo yayi awan gaba da ita.

********
Bangaran *Musaddam* kuwa  Mummy tana dawowa yace”Na farka banganki ba?”

“Eh zuwa nayi dan na cika alkawarin dana ɗaukar maka tun a wancan lokacin alhamdullahi kuma yanzu komai ya kankama zuwa gobe za’a|kai kuɗi gidan jibi kuma a kai kayan aure dan suma sunce basa so auran ya wuce sati ɗaya”.

Zamewa yayi daga saman kujerar yayi zaman dirshi a ƙasa kallon ta yake da mamaki yace”Mummy ban fahimci abinda kike faɗa ba”.

“Cewa nayi auran da nayi maka alƙawarin tun wancan lokacin Allah yayi nayi magana da iyayan yarinyar kuma daga nan zuwa sati in Sha Allah za’a ɗaura muku aure idan kuma ban isa da kai bane ba to”.

“A a Mummy na kin isa har kinfi karfin haka, ke uwa ce ni kuma ɗanki ne babu ta yanda za’ayi ki min zaɓin da bashi da nagarta kawai dama magana nake akan…”Akan me kuma son bayan ka gama magana yanzu idan har ka aminta dani kuma ka tabbatar ba zanyi maka zaɓin banza ba kawai kace dani”Allah yasa hakan shine mafi alkairi”.

“Allah yasa hakan shine mafi alkairi”.
“Amin yauwa ka kira Faruq zuwa gobe sai a buga kati a a faɗawa ƴan jarida da gidajan talabijin “.

“Mummy sunan yarinyar fa”?

“Babu ruwan ka duk Faruq ne zai yi wannan aikin ba kai ba”.

Tashi tayi ta shige ciki ɗaki abin ta .

Wani irin tari *Mussadam* ya fara tun yana yi a hankali har abin yayi tsanani tashi yayi ya shiga cikin ɗakin sa.maganin da Dr abokin sa ya rubuta masa ya ɗauka yasha…a hankali tarin ya soma lafawa har ya lafa gabaki ɗaya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button