HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Kwanciya yayi yana aiyana surar jikin *Ummi* da kuma kyawawan ɗabi’un ta wani irin hawaye ne masu zafin gaske suka shiga zarya a kuncin sa haka yayi wannan dare ba tare daya rintsa ba.

Wani tashin hankali bayan gari ya waye ya fito dan gaisawa da Mummy, ganin tana waya yasa ya ɗan tsaya yana jiran ta, koda ta gama kallon sa tayi tace”Son kalli wani abin mamaki ashe ita ma ƙanwar ka yau ake kawo kayan auran ta.”

“Mummy lil Sis aure zatayi shine bansani ba sai yau da za’a kawo kaya?”

“A a ba ita ba kanwar ka *Ummi* nake nufi fa”.

Tana gama fadan haka tayi gaba abinta tana sake kiran waya tana shaida musu auran sa.

Innalillahi wa Inna ilaihi raju’un kawai yake maimaitawa gabaki ɗaya jikin sa banda rawa babu abinda yake wani irin ciwon kai ne yayi masa dirar mikiya.

Kwanciya yayi a ɗaya daga cikin kujerun falon,babu abinda bakin sa ke fartawa sai tasbihi ga Allah dan kuwa shine kawai zai iya sama masa sauki.

Bangaran*Ummi* kuwa itama dai fitowar ta daga ɗaki kenan Umma tace”Yar albarka zo ga abinci nan ki ci kinjii sannan kuma ga Auntyn ki nan zuwa  wai zaku fita anguwa”.

Zama tayi umma tana bata abinci a baki hawayen na zuba, saidai ta gama ci sannan Umma ta shiga mata nasiha game da bin umarnin iyaye,sosai taji daɗi a ran ta.

Kallon ta tayi tace Kuma gashi shima dai *Musaddam* ɗin naki an saya ranar auran sa dan jiya aka kai kaya kamar dai yanda aka kawo naki”.

Da gudu *Ummi* ta nufi makwararar ruwan dake gidan amai take babu ƙaƙautawa saida ta  amayar da duk abinda taci.

Nan fa hankalin Umma ya tashi……

 

_Safnah Aliyu jawabi_✍️✍️✍️✍️✍️
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITERS’ ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idriss (M.I)*

_Jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idriss Musa_

4️⃣6️⃣

*_Allah is the only one who can understand your unspoken words, can see your tears. He can feel your pain where no one else can feel it. Don’t waste your time worrying when Allah is the controller of everything. Trust him.Allah knows what is best for us. He is wise and all knowing._*

 

 

______Shiru kawai ta yi hawaye na zuba ba tare da ta furta ko da kalma ɗaya ba…

“Ni ce sanadiyyar komai kuma ba zan yafewa kai na akan hakan ba dole na tafi gun Ya *Musaddam* na faɗa masa abinda ke cikin rai na, amma kuma ta yaya? Sam ba zan iya fuskantar shi nace masa ina son sa ba, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un Allah ka kawo min mafita.

Riƙo hannun ta Aunty tayi tace, “ki kwantar da hankalinki. Shalele ina mai tabbatar miki za kiyi alfahari da zaɓin da iyayenki suka miki wannan alkawari na ne.”

“Aunty ni ba na zargin iyaye na ko kuma tunanin za su jefa ni cikin wani hali, a’a sam abin ba haka yake ba wannan yare ne wanda zuciya da zuciya kawai ke iya fahimtar sa. Aunty zuciya ta yaya *Musaddam* kawai take wa kirari, Aunty Ya *Musaddam* shi ne kawai inuwar da nake laɓewa a jikin sa domin samar da salama ga ruhi na, shin me kike tunani yayin da aka ce babu shi?”

Murmushi kawai take jin wannan maganar daga bakin ta lallai an ce abinda babba ya hango yaro ba zai iya hango shi ba.

“Yanzu ki share hawayan ki kin ji, za ki iya zuwa kasuwar kuwa?”

“Zan yi ƙoƙari ko dan Umma na ta ji daɗi.”

“Shikenan shirya mu tafi.”

Da haka suka tafi kasuwa, sosai abin na ta ya bawa *Ummi* mamaki ganin yadda take ta harhaɗe wasu irin kaya marasa kyawun gani, abin dai har ya ishe ta tace, “Aunty wai duk wannan kayan na mene ne haka?”

“Ga shi nan dai nima ban san abinda ake da su ba amma dai na san cewa watarana za ki buƙaci na rakaki za ki zo sayen wasu”.

Daga haka ba ta kuma cewa komai ba don kuwa a ranta cewa take, “Insha Allah wannan rana ba za ta taɓa zuwa ba”.

Sai da suka biya gidan wata mata wanda kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da ƴar duniya ce don kuwa zata kai sa’ar Umma amma sai wani yauƙi take kamar ƴar 20 ɗin nan.

Sake baki kawai ta yi tana kallon ta har suka gama magana suka fito bata furta ko kalma ɗaya ba abin mamaki kuɗaɗen masu yawa Aunty ta miƙa mata, “ikon Allah Aunty wannan kuɗin da naga kin miƙawa wannan matar Aunty shi kuma kuɗin menene?”.

“Bana son yawan tambaya ni kaina a gajiye nake da kyar nake ɗaga ƙafata”.

Kallon kafar tayi gabaki ɗaya kafar ta kumbura daga ganin ta kusa haihuwa.

Haka dai suka shiga mota suka nufi gida.

********

Abu kamar wasa jama’a sai shigowa gidan suke ana musu Allah ya sanya alkairi,dangin Mummy tuni har sun fara ciki gida.

Gabaki ɗaya Mummy bata da natsuwa dan kuwa so take wannan bikin ya zama biki wanda zai daɗe yana ringing a zuciyar jama’a.

Ango kuwa yana nan luluɓe a ɗakin sa banda rawar sanyi babu abinda yake abu kamar wasa sallah ma ranar saidai yayi a daƙi, lokaci lokaci yake duba hoton ta wanda yayi mata ita kanta bata sani ba, shafe gaban hoton yayi yace”Ni kuma haka tawa ƙaddarar take son wacce bata taɓa ɗauka na matsayin masoyi ba  sai Yaya, Allah kasa duk wanda zai aure ta ya bata kulawa dan kuwa ko da wasa naji bata cikin kulawa tafiya zan har gidan ta na saka shi dole ya sake ta bayan haka na aure ta babu ruwa na da ta taɓa yin aure”.

“Auzubillahi Allah ka gafarta min, ganin kwanciyar yana saka shi ai yana mumunar nufi yasa ya miƙe ya ya nufin falon gidan,nan fa abokan wasa aka masa caaa kowa da abinda yake faɗa kallon su kawai yake yana Murmushi ɗaya daga ciki ne wanda sam babu wani shaƙuwa a tsakanin su kasancewa tana da izzar yasa ko kaɗan jinin su bai haɗu ba, tace” ina so nayi magana da kai”.

“Da Ni?”
“Eh amma ba anan ba”.

Sosai kowa yake mamakin wani magana ne kuma Khadijah take son yi da mutumin da ko gaisawa basa yi?”.

Haka dai ta fita yana binta a baya,motar ta ta nufa babu musu shima ya shiga suka bar harabar gidan, saida sukayi nisa sannan ta samu wani guri wanda ake shan iska ta shiga, Saida aka kawo musu abin sha sannan tace”Ya *Musaddam* me ke damun ka?”

Kai tsaye ya samu bakin sa da furta *Ummi* nake so itace farin ciki na kuma itace zaɓi na, amma Mummy bata ganewa a wannan karon ni da mahaifiya ta munyi hannun riga, a koda yaushe ra’ayin mu yana zuwa ɗaya amma a wannan ina”.

Dafe kansa yayi tsabida sara masa da take.

Sauke ajiyar zuciya tayi tace”Ita yanzu Ummi tana ina? A wani gari take? Shin itama tana son ka? Ka taɓa faɗa mata cewa kana son ta?

Sai a sannan kuma ya ɗago kai cikin sauri yace”Ban faɗa mata ba bata san cewa ina son ta ba amma kuma ai ita wani take so kinga koda ma na faɗa mata wancan dai zata aura”.

“Ta yaya kasan cewa shi take so bayan kai da kake namiji baka  taɓa nuna mata alamar da zata fahimci  cewar kana son ta ba?”
“Kana sa ran cewa har yanzu babu iri wa’annan matan har yanzu a duniya ko? To Nima haka nayi tunanin babu maza irin ka a duniya wanda suke son mace amma kuma su kasa furtawa har daga karshe suna gani wani can ya mallake su, dan haka akwai mata da yawa cikin duniyar nan wanda koda ciwon so zai zama ajalin su sam ba zasu taɓa furta kalmar so ga namijin ba”.

Wani irin gume ke karyo masa, saboda  hango gaskiya da yayi cikin kalaman ta,”Yanzu Sister menene abin yi?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button