MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

“A a ai ni kam na gama nawa yanzu kuma dabara ta rage ga mai shiga rijiya”.
Tana kai wa nan tace”ka tashi ka mayar dani gida”.
Murmushi kawai yayi yace”miskilancin ya tashi kenan ba?”
Itama Murmushi tayi tace kai kuma ka sani babu ruwa na matsoraci kawai yarinya ƙarama tana niman zautar da kai.”
Yana ijeta a gida bai tsaya ko ina ba sai gidan su *Ummi* idan ba kasan da gyaran ba gani zakayi kamar wata anguwa ka shigo ba wanda ka sani ba, sosai tsarin gidan yayi masa kyau dan tun wancan ranar bai kuma zuwa ba, komai na gida kama daga tsari har da paint irin na gidan su ne haka yake so kuma haka ya tsara ga shi da yardar Allah komai ya kammala..
********
*Ummi* kuwa suna dawowa gida ta nufi gidan su Maimuna kwance ta same ta a daƙi tana bacci, ɗaka mata duka tayi tace” Idan kana neman malalaciyar ƙawa to fa wannan kaɗai ta isa”.
“Idan kana neman ƙawa raguwa aka same ki an dace, a nan dai suka taɓa raha kamar yadda suka saba, sannan tace” Umma tace daga yau ba zan sake fita ba don Allah zaki min wata alfarma?”
“Ina jin ki.”
“Rakani za ki yi gidan su Ya *Musaddam* ko da sau ɗaya ne na gan shi Maimuna hakan zai kwantar min da hankali na”
“Kin tabbatar da idan kika ganshi za ki saduda kuma ki nuna farin ciki da zaɓin iyayen ki?”
“Insha Allah”.
“Amma yanzu ta yaya kika shirya ganin sa ba tare da Mummy ta ganki ba?”
“Niƙabin ki zaki ara min ban fito da nawa ba”.
“Shikenan tashi mu tafi.”…
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITERS’ ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A
*THE BOOK IS WRITTEN*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idriss (M.I)*
_Jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idriss Musa_
_*Do yourself a favour. Surround yourself with those who speak of visions, ideas, goals, growth. Not those who sit and gossip about others. And if you do find yourself in that situation, excuse yourself and walk away. The game ends when you choose to leave such a gathering.*_
_______ Sallama yayi a gidan aka bashi izinin shiga, Saida suka gama gaisawa da Umma sannan tace”Mummyn ku ta faɗa min cewa baka jin daɗi ya jikin dai?”.
“Jiki alhamdullah Ummu”.
“Madalla”.
Daga haka ta cigaba da aikin ta tana Murmushi ƙasa ƙasa dan kuwa tsaf tasan abinda ya kowa shi.
Ganin har kusan awannin uku babu ita babu labarin ta yasa yace”Umma wai ina ƙanwa ta ne?”
” *Ummi* ai tana can gidan su Maimuna suna shirye shiryan abubuwan da zasu gabatar na biki”.
Shiru yayi gabaki ɗaya ji yayi jikin sa yayi sanyi” kenan ma har wani shiri take sabida bakin, tana farin ciki? to idan har tana farin ciki da wannan bikin me yasa ni kuma zan zo gare ta awannan alokacin kawai dai samun nawa farin cikin? Idan nayi haka anya ba son kai bane ba?”
Tashi yayi yace”Umma zan tafi idan ta dawo kice mata nazo kuma ban ganta ba.”
“Idan ka tafi ka gaishe min da Mummyn naku”.
“In sha Allah”.
Da haka ya fita a gidan yana jin kamar farin cikin sa ya zo ƙarshe.
******
Ita kuwa suna fita basu tsaya ko ina ba sai gidan su, gidan a ciki yake da jama’a hakan yasa aka bar get ɗin gidan a buɗe,,, koda suka shiga harabar gidan tsayawa*Ummi* tayi tace”Yanzu ta ina zamu fara kenna?”
“Bakin san ɗakin sa ba?”
“Idan na sani sai kuma nayi me?
“Allah ya baki hakuri”.
“Ni ba faɗa nake miki ba kawai dai gani nayi babu amfanin zuwa gun sa kai tsaye tunda ba cewa zanyi ina son sa ba.”
“Shikenan yanzu menene abin yi?”.
“Kawai ki jira ni anan bara na shiga”.
Har zata tafi kuma wani dabara ya faɗo mata da gudu ta dawo gun mai gadi tace”Sannu malam”.
“Yawwa sannu.”
“Dan Allah *Mussadam* yana ciki?”
“A a ya fita amma ina da tabbacin ba zai daɗe ba zai dawo saboda sha’an da ake a gidan”.
“Shikenan na gode”.
Murmushi tayi tace”ki jira ni ina zuwa”.
Cikin sanɗa ba tare da mai gadi ya lura da ita ba tabi ta kofar baya, a hankali take tafiya kamar hawainiya har ta haura saman ɗakin sa ba tare da kowa ya lura da ita ba.
Sosai yanda aka sake gyara gidan yayi mata kyau, lumshe idanuwan ta tayi jin wani irin ƙamshe na tashi daidai Kofar ɗakin sa, cikin sauri ta buɗe kofar.
Sauke ajiyar zuciya tayi jin wannan mayatatcan ƙamshin sa tsam a ɗakin kamar yana ciki, komai na ɗakin a gyare yake kamar babu wanda yake zama a cikin sa, kamar ance ta juya sai ganin wani makeken freme tayi mai ɗauke da hoton sa yana Murmushi, cikin manyan kaya yanda kasan ranar ɗaurin auran sa, cire hoton tayi tana kallon sa cike da shauƙin so, wasu zafafan hawaye ne suka shiga zarya a kan fuska ta lokacin data tuna cewa nan da kwana biyar ya zama mallakin wata.
Zama tayi a ɗakin ta rinka risgar kuka kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwa.
Wasa wasa kusan awa ɗaya babu *Ummi* babu labarin ta tun Maimuna tana tsaye har ta ni mi guri ta zauna.
Ita kuwa tsabar kuka har ta bingere a gurin wani irin bacci ne mai daɗi yayi awan gaba da ita, bacci mai cike da mafarkan sa, bacci mai cike da natsuwa dan kuwa zanin gadon sa ƙamshe yake kamar Anyi ɓarin turare.
Fitan shi a gidan yayi daidai da parking ɗin motar Faruq kallon juna sukayi suna Murmushi yace”Kaga ango mijin Amarya”.
“Faruq bana cikin yanayin daɗi dan Allah karma ka fara.”
“Ban fahimci baka cikin yanayin daɗi ba.?”
“Yanzu dai ka faɗa min ina *Ummi* take?”
“Ji wani irin tambayar da kike min zuwa na gidan kenan ai nima”.
“Shikenan sai anjima ni zan tafi gida ina ɗan ganin jiri”.
“Shikenan Please do take care of yourself”.
“In sha Allah”.
Da haka ya shige motar sa yayi gida.
*****
Maimuna kuwa abin duniya sun taro sunyi mata yawa, kusan awa uku babu *Ummi* babu labarin ta .
Banda safa da marwa babu abinda take gashi duk wanda yazo wucewa sai ya kalle ta gabaki ɗaya a rikice take.
Hanyar da Ummi tabi ta nufa cikin sauri saidai kafin ta shige ciki motar *Musaddam* ta kusa kai cikin gidan.
Wani irin jiri ne taji yana niman kwashe ta cikin sauri ta dawo inda take tsaye tun farko.
Shi kuwa tunda ya parking ɗin motar sa yake jin bugun Zuciya sa na tsanan ta.
Jiki a sanyaye ya nufi cikin gidan, hayaniyar jama’a yasa ya fito yana cewa bara ina dawowa yanzu”.
Yana fita ya nufin kofar baya wanda kai tsaye zata sadashi da ɗakin sa.
Jin yanda ƙirjinsa ke bugawa da karfi yasa ya tsaya yana murza kirjin sa haɗe da lumshi idanuwan sa, banda hotunan ta babu abinda ke kai kawo cikin idanuwan sa, tsayin lokaci yana gurin dan kuwa ji yake kamar tana wajan sabida ƙamshin turaran ta wanda a koda yaushe yake manne cikin zuciyar sa.
Buɗe idanuwan sa yayi yana tunanin halin da zai shiga yayin da aka ɗauki *Ummin* sa aka ɗamƙata hannun wani a matsayin miji, wani irin ƙara yayi haɗe da buga hannu sa da bangwan gurin.
Nanfa jini yace Salamu alaikum ganin kamar ya janyo hankalin jama’a da wannan karan nasa yasa yayi saurin shigewa ɗakin haɗe da sanya kye.
****
Ita kuwa *Ummi* baccin ta take cikin sallama wannan karan da yayi ne yayi sanadiyar farkawar ta daga bacci, a firgici ta farka tana mai riƙe baki ganin yanda lokaci ya wuce ba tare da ta sani ba.
Leka ƙofar tayi ta ganshi rike da hannu kuma da alama ɗakin zai shiga, a riƙeci ta mayar da hoton cikin rawar jiki ta shiga ma’adanan kayan sa kirjinta na dukan uku uku”innalillahi wa inna ilaihi raju’un meneyi ne haka, yanzu me zan faɗa masa idan ya ganni anan ? Nashiga uku shikenan na zubawar wa iyaye na da mutunci, shikenan nasan Abba ba zai taɓa yafe min ba,duk da tarbiyyar daya bani amma kalli abinda nake wai sai yaushe ne *KARSHAN WAHALA* ta zata zo ne? kuma wai *DUK A SANADIN SOYAYYA* Gashi ina niman salwantar da *RAI NA* duk da kuwa yawan *NI’IMAR ALLAH* a gare ni amma kuma na bi son zuciya ta, yanzu idan aka tambaye ni me zance ya kawo ni *YAYA NA NE KO MIJINA*? Yanzu *INA MAFITA*? Yau ga ranar *AMJAD* Allah ka fitar dani daga cikin wannan halin ya Allah”.