HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Kallo ɗaya zaka yiwa *Ummi* ka fahimci tana da wani irin kyawu mai tsafta, ba irin bau ɗin nan ba. Tana da dara daran idanuwa ga hancinta madaidaici. Fuskarta tana da ɗan faɗi madaidaiciya mai ɗauke da ƙaramin baki, launin fata kuwa kai tsaye zamu iya kiranta da chocolate color dan kuwa ita ba irin baƙa har can ba ce ba. Gefe da gefen kumatunta kuwa a lotse suke da zarar tayi murmushi suke ƙara lotsewa.

*Ummi* ta kasance natsassiyar yarinya marar hayaniya ga ta da tsantsar kunya.

______________________________________________________________________

*Reviewed by: Musaddam Idriss Musa*

????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

 

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

_Jama’a ku shaida na sadaukarwa da wannan littafin ga*Musaddam Idriss Musa*_

*Reviewed By Musaddam Idriss Musa*

5️⃣

*Remember, no one owes you anything. Your responsibilities are yours alone. Don’t expect anything from anyone. That way, you won’t be disappointed or begrudge anyone. Free your heart from ill feelings towards others. Depend only on the Almighty. Indeed, He is sufficient for us!,*

 

A tsayi kuwa *UMMI* ta kasance ita ba doguwa ba kuma ba gajera ba, kai tsaye sai dai mu kira ta da matsaikaiciya.

Yanayin kirar jikinta kuwa yayi yanayi da na ƙirar kwalbar coca-cola domin *UMMI* tana da kyawun jiki irin wanda akasarin mata sukan yi burin a ce su ke da irin tsari da zubinta. Irin matan nan ne da maza ke rububi da mafarkin ganin sun samu damar mallaka.

Rashin hayaniyar ta yasa da dama ƴaran unguwar sa’annin ta suke matukar son su ga sun yi ƙawance da ita duk da kasancewar *UMMI* ba ta son hakan sai dai sam ba ta iya nuna musu a zahiri. Amma da sannu rashin kulawar da take ba su yasa duk suka yi ta janye jikin su, sai guda ɗaya wacce ta jajirce har dai *Ummi* ta saki jiki da ita suka fara ƙawance cikin aminci ana kiranta kuwa da suna Maimuna.

*Wannan shi ne tarihin Ummi a taƙaitace*

Ko da suka shigo gida samun guri ta yi ta kwanta tana mai jin ƙaɗaici. A haka bacci yayi awun gaba da ita. Sai da Umma ta kai mata ruwa toilet sannan ta zo ta tayar da ita, da kunkuni ta shiga toilet ɗin saboda tashinta da aka yi. Ita kuwa Umma binta da addu’a kawai kafin ita ma ta juya ta shiga na ta ɗakin.

Ko da ta fito, zama ta yi ta shafa mai. Doguwar riga ta saka marar nauyi. Sosai kayan suka mata kyau dagwas abin ta don *Ummi* ba karya akwai diri mai daukar hankali.

Duk yadda Umma tayi da *Ummi* ta ci abinci ƙin ci tayi saboda ba ta jin yunwa. Yayin da a can kasar zuciyar ta kuwa cewa take, “Umma da za ki haƙura ki daina kawo min wannan abincin wallàhi da na ji daɗi dan kuwa ba shi da wani gurin zama a cikin nan”.

Ba don Umma ta so ba haka ta hakura ta dauke abincin ta fita da shi.

Tana zaune tayi zuru ta jiyo sallamar da ko shakka babu muryar Maimuna ce. Cikin sauri ta miƙe tayo waje tarbanta tana mai riƙo hannun ta. Kallonta Maimuna ta yi tace, “kin fara wannan abin haushin naki ko?”

Fashewa da kuka ta yi ta rungume Maimuna tana cewa,”kenan ke ma kin bi layin su Umma ko?”

Girgiza kai Maimuna tayi tace, “a a wallàhi ba haka ba ne ba *Ummi*  kar ki mance ke fa mace ce, kuma an san mace da kunya domin kunya a gun mace ado ce don ALLAH ki rinƙa rage wa kin ji, friend?”

(Wannan suna friend ɗin wallàhi bana son shi haka wani yake ce min Ni kuma sam nafi so yace, “min ƙanwa amma yaƙi ???????? lol)

Share hawayen ta ta yi tace,”shikenan, na ji. Nagode”.

“Tom babu damuwa dama ji na yi an ce *MUSADDAM* ba shi da lafiya yanzu haka…”

Wata irin cakuma da ta kai mata ne ya hanata ƙarasa maganarta ta, cike da mamaki take kallon ta tare da tambayar ,”mene ne friend?”.

Kamar wacce aka tsikara kuma ta miƙe cikin sauri hawaye na kwaranya gami da gangarowa bisa fuskarta kamar an saki ruwan fanfo tayi waje tana wani irin ajiyar zuciya cike da damuwa da tashin hankali. A lokacin kuma Umma tana sallar la’asar don haka ba ta san wainar da ake toyawa ba.

A daidai mashigar zauren gidan ne suka yi kicibus da Abba wand saboda tsabar ruɗewa *Ummi* ko lura da wanzuwar mutum a gabanta ba tayi ba don kuwa neman bangaje shi take shirin yi. Ganin kamar ba a cikin haiyacinta take ba yasa ya kira sunan ta cikin ɓacin rai don kuwa ya san dai tatsuniyar gizo ba za fa ta wuce ta ƙoƙi ba.

Kallon sa tayi da idanuwan ta wanda suka koma kamar garwashin wuta tace, “Abba na shiga uku na Abba wai ba shi da lafiya, Abba! *MUSADDAM* ɗi na ba shi da lafiy….” Kuka take sosai kamar wacce aka yi wa mutuwa, Abba kuwa tsabar yadda wannan lamari ya ishe shi yasa ya ma kasa ko da motsi ne bare kuma ta saka ran jin maganar sa.

Fitowar Umma yasa duk suka juya suna kallonta, tambayar abinda ya faru tayi, Maimuna ce ta faɗa mata duk abinda ke faruwa.

Kallon Umma Abba yayi yace,” karki hana ta ki bar ta ta tafi gurin nasa kila mu ma yau mu samu damar runtsawa”.

Yana gama faɗin haka yayi cikin gida abinsa, *UMMI* kuwa duk da jikinta yayi sanyi amma hakan ɓai sa ta ji za ta iya yin hakuri da zuwa duba *MUSADDAM* ba.

***********

Shi kuwa *MUSADDAM* duk yadda ya so yayi bacci cikin daren nan abu ya faskara. Sosai yake jin zafi da ƙunci a zuciyar sa. Babu abinda yake iya tunawa sai zazzaƙar muryar ta tana kiran suna sa wanda zai iya rantsewa babu wanda ya iya kiran sunan sa kamar yadda ta iya, *MUSADDAM* wani irin yarrr ya ji tun daga tsakiyar kan sa har tafin ƙafarsa.

Addu’a kawai yayi ya rintse idanuwansa saboda ya samu yayi bacci amma ina yaki ya zo. Ganin yana ɓata lokacin sa a banza ne yasa ya tashi ya shiga toilet alwala ya ɗauro ya fara gabatar da nafila, ba shi ya samu ya rintsa ba sai da yayi sallar asuba.

Bacci mai cike da mafarkanta kamar dai yadda ya saba duk ranar duniya sai yayi wannan mafarkin, wannan karon ma a firgice ya farka yana faɗin “Don ALLAH kar ki tafi ki tsaya ki faɗa min ko da sunan ki ne”.

Dafe kansa yayi lokacin da yayi arba da fuskar mummy tana kallonsa, kallo mai cike da tarin ma’ana.
Sunkuyar da kansa yayi yana sosa keya yace, “I’m so sorry momma”.

Tahowa tayi zuwa inda yake tace,”har ila yau zan sake tunatar da kai cewar, “ba ka da wacce ta fi ni a rayuwarka, saboda haka ya rage naka ka faɗa min ko kuma ka cigaba da bari damuwa tayi ta illata rayuwar ka”.

Tana kai wa nan tayi ficewarta tana share hawaye, ɗago kansa yayi ya kalli agogon ɗakin kusan 12:pm girgiza kansa yayi yace, “lallai kuwa akwai buƙatar na gaggauta barin asibitin nan sam ba zan juri ganin ɓacin ran mummy ba.

Tashi yayi ya shiga toilet da nufin ya watsa ruwa amma dukda kuwa toilet ɗin a tsaftace yake hakan bai hana shi jin ƙyanƙyamin shiga ciki yayi wanka ba, haka nan ya fito ba tare da yayi wankan ba. Sai da likita ya duba shi sosai ya tabbatar babu wata matsala sannan aka sallame shi haɗe da ba shi wasu ƴan shawarwari.

Zama yayi a ɗakin yaƙi fita, shi kansa bai san abinda yasa yake jin ciwon fitar da zai yi daga asibitin ba. Ji yake kamar fitar sa kamar wata babbar asara ce, rintsa idanuwan sa yayi yace, “ban san a ina kike ba ,kuma ban san duniyar da kike ba, haka ban sani ba ko ke aljanna ce ko mutum. Abu ɗaya kawai nake so ki sani shi ne a duk yadda kika zo to fa *MUSADDAM* yana tare da ke. Ina matukar ƙaunarki gimbiyata, ke ce ma’aunin farinciki na, a tare dake kawai nake jin zan iya sauke damuwa ta, na tabbata duk inda kike a cikin duniyar nan wata rana zaki zo gare ni. Daga nan ni kuma nayi miki alƙawarin kasancewa dake daga nan har zuwa ranar da za’a cire min rai na”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button