HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Kuka take sosai.

Shi kuwa yana shiga toilet ya shiga ya wanke hannu shi dake fitar da jini, towel ɗin sa mai kyau ya ɗauka yana goge hannun sa, kallon hoton sa yayi ya ga kamar a jirkece take,sosai yayi mamaki dan kuwa bama a inda hoton yake aka ije ba an canza masa gurin zama,”Wanene ya shigo min ɗaki, a hankali yake takawa har gaban hoton wannan ƙamshin na ta daya jine yasa ya lumshi idanuwan sa yana shaƙa a hankali sosai yake cike da so da kaunar ta banda sambatu babu abinda yake saidai kuma a cikin zuciya yake yin ta.

Gyara hoton yayi ya nufi ma’adanar kayan sa yana mai sake jin daɗin jin ƙamshin turaran *Ummi* babu shakka ɗaya daga cikin ƴan bikin nan akwai wacece take amfani da irin turaran ta…

Buɗe ma’adanar kayan yayi yana mai sauke ajiyar zuciya……
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITERS’ ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idriss (M.I)*

_Jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idriss Musa_

4️⃣8️⃣

_*Sometimes the Almighty removes a particular person from your life because the relationship no longer serves any purpose. There’s no more positive growth. Learn to recognise it. Don’t run after that person who is not meant to be part of the next journey of your life. Move on!*_

 

_______Ƙame wa kawai tayi dan kuwa tuni ta sadakar ya gama ganin ta kiran wayan sa da akayi ne yasa yayi saurin komawa gaban mirro ɗinsa,ko me akai faɗa masa sai gani kawai nayi ya fita daga ɗakin gudu gudu sauri sauri,ganin haka yasa tayi wani irin ajiyar zuciya tana mai jaddada godiyar ta ga Allah daya rufa mata asiri.

Fitowa daga ɗakin tayi cikin sanɗa ba tare da kowa ya lura da ita ba,.ganin Maimuna a tsaye ba ƙaramin mamaki ya bata ba dan kuwa a kal’la kusan awan ta uku cikin gidan, rike mata hannu tayi ba tare data furta komai ba suka bar harabar gidan.

Kallon ta tayi tace”me kika tsaya yi a cikin gidan na tsawon wannan awannin?”

Yanda abin ya kasance ta zaiyana mata,aikuwa banda dariya babu abinda Maimuna take har suka isa gida.

Shigar su gidan keda wuya suka tarar da wannan hamshakiyar matar zaune sai wani hura hanci take, gaisheta  sukayi kawai ,*Ummi* ta shige ɗaki.

Haɗe fuska Aunty tayi tace”Ina kika shiga akai ta niman ki haka?”.

“Aunty babu inda na tafi mun kai wa sauran ƙawaye na alawa ne”.

Shikenan maza ku shirya dan kuwa an rigada an kwashe duk abinda kuke buƙatar an kai su wancan gidan ke kawai muke jira idan akwai abinda kike so cikin wa’annan kayan.”

“Eh Aunty kawai a ijewa Maimuna zata kwashe su.”

“To shikenan muna iya tafiya ko dan kuwa hajiya babba ke kawai take jira, yarinya kinyi goshi dan kuwa hajiya bata zuwa da kanta saidai ta aiko yaran ta abin mamaki ke tun kafin ma akira ita da kanta ta zo.”

Da mamaki tace”To ai duk azarɓaɓin ta dai ba yau bane ɗaurin aure bare tace zuwa tayi dan cin abinci.”

Ɗaka mata duk Aunty tayi”Shalele ki fita daga idona Kinji dai na faɗa miki.”

Haka suka ƙwashe duk abinda suke da buƙata suka koma sabon gida, tsabar murna Abba Saida ya zuba ƙwalla ganin gidan da yake kuma wai mallakin sa.

Saida komai ya lafa sannan aka nunawa wa Hajiya ɗakin da za’a fara gyara*Ummi* a ciki,sosai wannan lamari ya bata mamaki ganin yanda ake ta haɗe haɗan abubuwa.

Hajiya kuwa zama tayi ta shiga dirje mata jiki sosai dan kuwa yarinyar ta shiga ran ta kama take mata da ɗiyar ta Nana wacce ta rasu sanadiyyar haɗarin mota.

Cikin kwana biyu kacal *Ummi* ta koma kamar jaririya,ko kuma nace jaririyar wata,fatar ta har wani sheƙi yake,ƙamshi kuwa gabaki ɗaya gidan ya ɗauka, tun abin yana damun ta har ta fara jin daɗi dan kuwa ko ruwa baya tsayuwa a jikin ta, abu ɗaya ke damun ta yanzu shine abubuwan da Hajiya take kawowa kuma ta matsa mata dole sai ta sha, haka babu musu take karɓa ta sha dan kuwa tuni ta gane matar tana ƙaunar ta, duk da haka kullum cikin tunanin sahibin ta take.

Bangaran sa kuwa shima haka abin yake gidan da yake ginawa tuni Mummy ta saka an sake masa sabon yanayi, koda ya tafi gidan zama yayi yana tunanin yanda rayuwar sa zata kasancewa dan kuwa rayuwa babu *Ummi* a cikin ta tofa tamkar riga babu wando ne.

Mummy kuwa kullum sai ta kira hajiya ta sake bata sabon haɗi dan ta rinƙa bawa*Ummi* yau ma kamar kullum kiran ta tayi tace”Ina fata ƴata tana cikin ƙoshin lafiya?”.

“Eh lafiyar ta kalau saidai ina yawan ganin damuwa akan fuskanta ta

“Eh wannan babu matsala kinsan dole dama hakan zata kasance ai rabuwa da iyaye ba ƙaramar al’amari bane ba”.

Da haka suka sauke waya, ana gobe ɗaurin aure duk wanda ya shigo gidan nan sai ya yaba da kyawu da zubin haliltar da Allah yayi wa wannan yarinyar, dan ramar da tayi sai ta kara haske,rashin cin abinci yasa cikin ya  sake lafewa a jikin ta kamar ba’a halilci wani abu a gurin ba, hips ɗin ta kuwa yanda kasan zai tsule idanuwan mai kallo, haka kirjin ta abubuwan da ake bata yasa suka sake cikowa suka tsa_tsaya .

Ita kanta tana jin sabon sauyi a jikin ta saidai kuma babu wanda zata iya faɗawa wannan sirrin tane.

A daran wannan rana Mummy ta saka shi gaba dole ya kawo ta gidan su *Ummi* zata  bata kaya.

“Mummy wai dole sai cikin daran nan za’a kai mata kaya?”
“Eh Kaga ba zan samu zuwa bikin ta ba tunda ga naka shiyasa zan kai mata wa’annan kayan ka gane?”

“Shikenan Mummy Wai shikenan ni ba zanga matar da zan aura ba?
“Mummy kiji tausayi na mana dan Allah ni fa *Ummi* nake so”.

“Kai wai tunanin me kake haka ka tsare ni da idanuwa kamar zaka cinye ni.”

Cikin sauri yace”Sorry Mummy na wani abu nake tunani.”

Murmushi yayi yana ai yanawa a ransa kenan zancan zuci nake hmm”.

Da haka har suka shiga cikin layin su,banda duka babu abinda kirjin sa yake sam bai so sake haɗuwa da ita ba dan kuwa haɗuwa da ita tamkar fama masa ciwon sane, da haka dai ya samu guri yayi parking ɗin motar sa, daidai bakin get ɗin gidan a cewar sa baya son shiga da motar sa ciki.

Kwance take amma tako ƙafar sa daya cikin gidan yasa ta miƙe cikin sauri tana jin yanda tsigar jiki ke tashi, share hawayan daya gangaro mata tayi tana cewa”Nasan ba zan sake ganin ka ba Yaya *Musaddam*  wannan yanayin ma kawai dai nasan yanda nake ji ne a kwanakin nan,  ni dai nasan sam ba zanyi tsawon rai ba ,zan rayu ne cikin so da kaunar ka, tabbas babu maganin da zata samawa zuciya ta sauki face kasancewa da kai Yaya *Musaddam* haka dai ta rinƙa sambatu,jin Sallamar Mummy yasa ta fita a ɗakin da gudu ta nufi falon gidan Allah ya taimaka dogowar riga ce sanye ajiki ta saidai kanta babu ko ɗan kwali, ganin ta a haka kuwa yasa ya *Musaddam* ya zama kamar status daidai da idanuwan sa basa ko motsi, ita kuwa rungume Mummy tayi ta fashe da kuka ,kuka take sosai kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwa,jin sautin kukan ta yasa Umma da Abba duk suka fito, janyo ta Mummy tayi suka zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon ,shafe mata kai ta rinka yi tana mai Rarrashi ta da kalamai masu sanyaya zuciya.

Da mamaki Umma tace” Zo ka zauna mana ka tsaya kuma kamar bako”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button