MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Sai a sannan ya dawo haiyacin sa, zama yayi kansa a ƙasa dan kuwa babu shakka idan har zai matsa tofa hawayan da yake rikewa zubuwa zasu’yi,ganin yanda yake kallon ta yasa Mummy tace”Tashi mu tafi dakin ki na kawo miki wani abu kinji ƴata?”
Da haka suka tafi *Musaddam* kuwa kusan sumewa yayi a gurin ganin yanda komai ya ni mi guri ya zauna.
Suna shiga ta zaunar da ita tayi mata nasiha mai ratsa jiki da nuna mata hakin miji akan matar sa.
Sosai take kuka har da ajiyar zuciya.
Nuna mata kayan tayi tace ta gwada su, Allah cikin ikon sa kuwa kayan sunyi mata daidai kamar an gwada ta ,banda godiya babu abinda *Ummi* take mata har suka bar gidan,suna fita yace”Mummy ba zan iya jan motar nan ba kai na ciwo yake min ki taimake ni Mummy na”.
Dafe shi tayi taji jikin sa yayi wani irin zafi na fitar haiyaci hakan yasa tayi sauri taimaka masa ya shiga motar suka bar harabar gidan,ta kofar baya suka shiga saboda gidan kamar rana haka take ga jama’a ta ko ina lungu da saƙo, kiran Dr ɗin su tayi yayi masa allurai da karin ruwa, nan fa bacci yayi awan gaba dashi, Safnah kuwa wacce ta dawo a ranar da gudu ta haura ɗakin sa ganin halin da yake ciki yasa tace”Mummy wai dan Allah mecece hikimar yin duk wannan abin ne?”
Da ƙuwa tayi mata tace”Gidan ku nace dalla matsa min na fice saura kuwa ki faɗa masa za ki haɗu da bacin rai na”.
………
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITERS’ ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*THE BOOK IS WRITTEN*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idriss (M.I)*
_Jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idriss Musa_
4️⃣9️⃣
*Almighty. Keep hope alive in our hearts. We may not see a way out of our predicament but we know that You have a way. You always do in Your own time. Fill our hearts with deep rooted trust in You. Despite the setbacks we have to deal with, You will never disappoint! Aameen.*
_______ Duk da ƙarfin al’lurar da aka masa sam baccin bai yi wani nisa ba ya farka,gabaki ɗaya idanuwan sa sun kumbura haka fuskarsa ta ɗan kumbura ta yanda kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yana cikin damuwa sosai.
Kallon ta yayi yace”Lil Sis baki ƙwanta ba”.
“A a bro kana cikin wannan halin ta yaya har zan iya bacci kai kawai nake dashi a faɗin duniya ko tafiya makaranta na Mummy ce kawai ta matsa dan Allah yaya ka kwantar da hankalin ka in sha Allah ba zaka taɓa yin dana sani akan zaɓin Mummy da tayi maka ba bro”.
Share hawayan sa yayi” Lil Sis ko da wacce Mummy ta zaɓa min ba tai daidai da ra’ayi na ba zanyi mata biyayya karki mance duk wahalhalun da Mummy tayi duk dan dai mu zama ƴaƴa na gari,kama daga rashin mijinta haka ta tsaya tsayin daka ta bamu ingantacciyar rayuwa sabida haka babu komai zan jure in sha Allah”.
“Yawwa Bro haka nake so na rinƙa ji ka kwantar da hankali kayi bacci sai da safe”.
Tana fita ya ɗauko wayar sa kallon hoton ta yake hawaye na zuba kallon hoton yake cike da shauƙin so.
Tashi yayi ya ɗauro alwala da haka har aka kira sallar asuba yana zaune bisa sallaya.
Bangaran ta ma haka abin ya kasance gabaki ɗaya kasa bacci tayi banda kuka babu abinda take,tunda asuba aka saka tayi wanka Maimuna kuwa sai bata baki take amma ina, tunanin cewa nan da wasu awanni shikenan sun rabu kenan rabuwa ta har abadan yasa take sake jin gabaki ɗaya ta tsani duniya da abinda ke cikin ta.
Kiran Umma Mummy tayi ta faɗa mata irin kayan da *Musaddam* zai saka sannan ta kashe wayar tana Murmushi, “Yau nasan zaka fi ko wani ɗa namiji farin ciki my Son kuma nasan za kayi alfahari dani,fata na Allah ya albarkaci rayuwar ku da albarka mayalwaciya.”
Da kyar ta tsaya aka mata kwalliya dan ma Aunty ta tsaya tsayin daka kenan duk da kuwa itama sosai yau take jin ciwon mara da baya amma haka take daurewa dan ganin komai ya tafi daidai.
Ƙarfe tara aka sharya ɗaurin aure tun karfe 8 Mutane suka fara zuwa dan kuwa ba karamin abu bane ga sauran mutanan garin tunda kowa yasan irin taimakon da suke.
Zama yayi cikin toilet ɗin sa gabaki ɗaya kasa zuba ruwa a jikin sa yayi banda ruwan hawayen babu abinda yake.
Kiran suna sa da Mummy tayi ne yasa yayi hanzarin watsawa ruwa ya fito, faruq ne zaune yana jiran sa Murmushi yayi masa yace”Jama’a kunga Ango har wani kyalli kake Alhaji na”.
Shiru yayi kawai yana kallon sa haka kawai yaji yana da buƙatar jin ko da sunan amaryar ne,”Faruq yaya sunan amaryar ne?”.
“Kana nufin baka san sunan amaryar taka ba kenan gaskiya ka bani kunya.”
“Idan zaka faɗa min ka faɗa min kawai idan kuma shima jin sunan akwai Matsala ka barshi kawai”.
“Wane ni kai da matar ka ai dole na faɗa maka, sunan ta Maryam”.
“Maryam Maryam haka kawai kuma ya samu kansa da jin sanyi a ran sa wanda shi kansa bai san dalili ba”.
Tsayuwar da Mummy tayi a falon yasa yayi saurin shiryawa, fitowar sa yasa Mummy ta tsare shi da idanuwan ta babu ko kiftawa.
Rike mata hannu yayi yace”Mummy yau ba ranar kuka bace ba yau ne ɗanki wanda kika haifa yake shirin cika miki duk kanin burukan ki dan haka murna ya dace dake Mummy na”.
“Haka ne amma yau sai nake sake ganin kamanin ka da mahaifin ka,ina ma yana nan da yau yaga ɗansa wanda yake mattukar so da kauna yana shirin sauka daga wannan matakin zuwa wani wanda zai samar masa da farin ciki na tsayin rayuwa, amma nasan duk inda yake yana cikin farin ciki dan kuwa yau in sha Allah zan cika alƙawarin dana ɗaukar masa , yau nayi kamar yanda ya umarce ni, na cika masa alƙawarin dana ɗaukar masa Son”
Nan fa ta fara zubda hawaye,share mata hawaye yayi yaja hannun ta har zuwa falo wanda cike yake da jama’a kowa sai sam barka yake masa da yaba irin kyawun haliltar sa dan kuwa sosai kama yake da mahaifin sa harta Murmushin su iri ɗaya ne.
Kallon sa tayi tace”Amma dai zaka min wata alfarma yau kafin a ɗaura maka aure kaji Son?”
“Ina jinki Mummy na.”
“Kafin ka tafi ɗaurin auran ka ina so ka tafi auran *Ummi* na kaji tunda auran ka sai karfe goma ita kuma ƙarfe tara fatan zaka min”
Sauke ajiyar zuciya yayi yana jin wani abu ya tokare masa maƙoshi, danne wa yayi yace”Shikenan Mummy muna iya tafiya can ɗin”.
Da haka suka nufin gidan su Ummi cikin mota ɗaya suka zauna shi da Mummy, banda farin ciki babu abinda kake iya hangowa akan fuskar ta.
Ganin wannan kuwa a gunsa yafi komai daɗi dan haka ya dan ne abinda yake ji dan kuwa farin cikin mahaifiyar sa yafi komai a gun sa.
Nasihar da Hajiya babba tayi ta mata ne yasa ta dan ne kukan ta har ta saka kaya ya kasance komai iri ɗaya ne da wanda Mummy ta bawa *Musaddam* shadda ce fara tas wanda yasha aiki daga sama har ƙasa, sosai kayan suka karbi jikin ta gashi ta samu mai ɗarin ɗakwali dan kuwa sosai ya zauna mata a kai babu abinda ke fita daga bakin jama’ar dake ɗakin sai ma sha Allah,dangi da abokin arziki duk an cika gidan har ƴan Suleja ma ,taro dai yayi taro jama’a sai fatan alƙairi suke mata.
Ko da suka iso tuni ƙannan Mummy har sun iso an fara shirye-shiryan ɗaurin aure, banda gumi babu abinda *Musaddam* yake Mummy kuwa suna zuwa ta shigewar ta cikin gidan,rungume *Ummi* tayi tana saka mata albarka.