MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Lafewa tayi a jikin ta tana sauke ajiyar zuciya, tana ji aka fara ɗaurin auran wanda daga karshe aka ambaci sunan da saida ta firgita,shafe idanuwan ta tayi dan kuwa babu shakka wannan irin wannan mafarkin da take ne, kabbarar da jama’ar ɗakin suka ɗauka ne yasa ta tabbatar ba mafarki take ba sam wannan gaskiya ne Sunan yaya *Musaddam* taji kuma dashi aka ɗaura mata aure kallon Mummy tayi dan sake tabbatarwa murmushi tayi mata hakan ne ya sake tabbatar mata da cewar da gaske yaya *Musaddam* shine zaɓin da iyayan ta suka Mata, buɗe baki tayi da niyyar magana, shigowar Maimuna ɗakin yasa tayi shiru tana share hawayan dake kwarara a kan fuskar ta gabaki ɗaya ta kasa gani dalilin wannan kukan.
A rikice Maimuna take magana da Mummy”Mummy Yaya *Musaddam* babu lafiya yanzu haka an tafi dashi asibiti, ai Ummi bata san lokacin data ƙaraso gare ta ba, cike da firgici take tambayar ta abinda ya same shi, “nima dai ban sani ba amma jama’a da dama sunce yana jin an ɗaura auran kune ya sume”.
Komawa da baya tayi ta zauna tana jin wani sabon kuka mai cike da ƙunar zuciya, da gudu Mummy da sauran jama’a suka fita dan ganin abinda ke faruwa.
“Innalillahi wa inna ilaihi raju’un Umma meyasa kuna ji kuna gani kuka yarda aka ɗaura min Aure da mutumin da ba sona yake ba, yanzu gashi a gaban jama’a ya sume jin an ɗaura min Aure dashi, a haka kuke so na tafi nayi Rayuwa dashi a matsayin miji, innalillahi wa inna ilaihi raju’un na shiga uku na,Yaya *Musaddam* nayi alƙawarin muddun rayuwa da ni ba zai samar maka da farin ciki ba ina mai tabbatar maka ba zan taɓa yarda wannan auran ya ɗauki lokaci ba tare da an raba shi ba, babu abinda nake so da ƙauna kamar ganin ka cikin farin ciki”.
Haka ta zauna tayi ta sharɓan kuka har zazzaɓi mai zafi ya rufe ta, shigowa ɗakin Umma tayi fuskar ta ɗauke da murmushi tace”Daina kukan haka ya farfaɗo dama ba komai bane bace fargaba Kinji*Ummi* na”.
Ɗago kai tayi tace”Umma ni bana son zama da shi dan Allah a raba wannan auran kinji Umma na.”
Janye ta tayi daga jikin ta ranta a ɓace irin ɓacin ran da bata taɓa ji game da ita ba tace”Idan na kuma jin wannan Maganar daga bakin ki sai na saɓa miki saɓawa irin wanda baki taɓa tunanin ba.”
Daga haka ta fice daga ɗakin.
Kuka take mai cike da kuna” yanzu yaya zan yi wanda suka aura min ba sona yake ba daga jin an ɗaura mana Aure ya suma, Umma tace zata saɓa min idan na sake furta kalmar rabuwa dashi.”
*********
Shi kuwa a sume aka isa dashi asibitin kowa na mamakin abinda ya same shi haka, saidai dr suka duba shi kuma aka saka masa ruwa sannan suka sanar dasu cewar ba wani abu mai tsananin bane ba kawai damuwa ce da rashin bacci.
Da sunan ta ya farka hawaye na kwarara a fuskar sa,rike masa hannu Faruq yayi yace”Yanzu ina ne ke maka ciwo?”.
“Zuciya ta Faruq zuciya ta ke ciwo ina jin cewar komai ya zo karshe a wannan ɓigirin dan kuwa na rasa duk kan farin ciki na faruq”.
Muryar Mummy da suka jine ya saka yayi shiru cewa take”Idan har ina raye in sha Allah zaka samu dukkan farin cikin ka koma ince ina maka albishir da samuwar farin ciki ka wacce muke fatan ta kasance a hannun ka har i zuwa mutuwa Son.”
Gyara kwanciyar sa yayi yace”Sam baki fahimta ba Mummy na,*Ummi* itace komai nawa Mummy, Mummy *Ummi* nake so kuma da ita kawai zan iya rayuwa Mummy na ki taimaka min Mummy.”
“Share masa hawaye tayi fuskar ta ɗauke da murmushi tace”Zanyi maka albishir My son Kuma ka tabbatar ka tanadi kyautar da zaka min.”
“Tashi yayi ya zauna yace”Zanyi miki duk kyautar da kike da buƙata Mummy na”.
“Kamar yanda na faɗa maka ba’ayin alƙawari a yayin da ake cikin farin ciki, haka ba’a yanke hukunci a yayin da ake cikin fushi sabida haka bana buƙatar komai”. Amma ka sani bada kowa aka ɗaura mata Aure ba sai kai My son kai ne mijinta ba kowa ba,itace dai zabin ka kuma zaɓin iyayan ka”.
Fisge karin ruwan da aka masa yayi sabida tsabar farin ciki, rungume faruq yayi yana cewa” Tabbas babu mai uwa irin tawa nafi kowa dacan uwa a duniyar nan faruq.
Murmushi kawai tayi tace”Yanzu tunda ka warke ai sai ka tashi mu tafi gida ko ɗan Soyayya”.
Shafe kansa yayi cikin kunya yace”Yanda kika ce Mummy na”.
_*Safnah Aliyu jawabi*_ ✍️✍️✍️✍️✍️
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITERS’ ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*THE BOOK IS WRITTEN*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idriss (M.I)*
_Jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idriss Musa_
5️⃣0️⃣
*Remember, no one owes you anything. Your responsibilities are yours alone. Don’t expect anything from anyone. That way, you won’t be disappointed or begrudge anyone. Free your heart from ill feelings towards others. Depend only on the Almighty. Indeed, He is sufficient for us!,*
______Jama’a kuwa sai bidiri ake a gidan biki.
Tayar da ita Umma tayi aka bata wasu kayan ta saka,sosai kayan suka ɗauki jikin ta, gashi ƙwalliyar ta tayi masifan kyau,. Abin mamaki tana fitowa daga ɗakin ya *Musaddam* ne tsaye a bakin kofar yana mata murmushi mai cike da so da ƙauna, abubuwa biyu ne suka haɗu mata a wannan lokaci mamaki da kuma tsantsar jin kunyar ganin yanda ya buɗe mata hannuwan sa alamar tazo gare shi… tsayawa tayi kanta a ƙasa dan kuwa wannan shine abinda ba zata taɓa iyawa ba.
Ganin ana jiran su yasa ya janyo ta aikuwa ta faɗa ajikin sa, sauke wani nannauyar ajiyar zuciya duk sukayi a tare,mannewa tayi a jikin sa tana lumshe shanyayyun idanuwan ta tarin tambayoyi ne a zuciyar ta amma kuma wa zata tambaya?
Gyara mata mayafinta yayi yace”Kuma ko da ance kiyi rawa kika sake kika yi sai na karya miki kafafuwan ki kinji dai na faɗa miki”.
Hannuwan su a sarƙafe da juna suka shiga gurin taron wanda musamman aka kira masu kiɗin ƙwarya, abin kuwa sosai ya bada ma’ana.
Abin mamaki duk yanda akayi da amarya kin yin rawa tayi,shi kuwa duk wani motsin ta akan idanuwan sa take yin shi.
Ƙarfe biyu nayi aka dakatar da kiɗin saboda lokacin sallah yayi.
Tsabar murna rungume Maimuna tayi tace”Na kasa yarda da wannan mafarkin wai dan Allah da gaske yaya *Musaddam* shine ango na ba Safyan ba?”.
“Tabbas shine angon ki kuma zan kara miki wannan albishir ɗin bayan wannan saboda ke ya sume ɗa zu, duk tunanin sa wani zaki aura ba shi ba”.
Miƙewa tsaye tayi,”kina nufin saboda ni ya sume? Saboda tunanin ya rasa ni yasa ya sume?”
“Tabbas wannan ba labari bane ni ganau ce ba ji yau ba”.
Da gudu ta shige toilet ta sake ɗauro wani alwalan sallah tayi raka’a biyu tana mai sake jaddada godiyar ta ga Allah daya nuna mata wannan rana.
Ƙarfe biyar aka shirya zuwa dinner leshi ruwan madara tasa mai ratsin baki sosai tayi kyau abin ta banda fara’a babu abinda kake iya hangowa akan fuskar ta,duk wanda ya ganta a wannan lokacin kowa yasan wannan tana cikin farin ciki dan kuwa daidai da minti ɗaya bata rufe haƙoran ta ba.
Jerin motoci ne masu kyau da tsada a Kofar gidan, saida aka tabbatar da kowa ya samu shiga sannan aka saka amarya a cikin motar da ango yake,shigar ta keda wuya ya janyo ta jikin sa, ɗago kanta tayi tana kallon sa ido cikin ido,lakutar hancin ta yayi yace”Kinyi kyau abin ki rigimammiya ta”.