MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Turo baki tayi tace”Wallahi ni ba rigimammiya bace ba tom”.
Haɗe bakin su yayi guri ɗaya, kissing ɗin ta yake cikin salon sa mai rikitarwa, gabaki ɗaya banda ɓari babu abinda jikin ta yake saida yayi mai isarsa sannan ya sake ta,kallon ta yayi yace”idan na kara magana kika sake tura min baki sai na miki wanda yafi wannan rigimammiya kawai”.
Hawaye take sosai gashi duk jambakin ta ya goge, kallo ta yayi yace”Au kina so na ƙara kenan ko?”.
“Dan Allah kayi hakuri wallàhi ba zan sake ba”.
Kunshi dariyar sa yayi yace”Matsoraciya kawai”.
Koda suka isa gurin taron kiran Safnah yayi tazo ta gyara mata ƙwalliyar tana dariya.
“Dariyar me kike magulmaciya?”.
“Allah ya baka hakuri yaya na”.
Ita dai shiru tayi har aka gama gyara mata ƙwalliyar dan kuwa sosai ta tsorata da lamarin sa.
Murmushi yayi yace”Na ɗauki alƙawarin ba zan taɓa nuna miki cewa Faruq ya bani labarin gwagwarmayar da kika yi akai na ba har sai zuwa lokacin dana shayar dake zumar soyayya ta,babu shakka zan nuna miki so fiye da yanda kike tsammani zan girmama ki zan agazawa rayuwar ki, zan nuna miki gata. fata na Allah ya bamu zaman lafiya mai ɗaurewa.
Da haka suka shiga gurin taron, wuri fa yayi wuri babu abinda ke tashi cikin gurin sai ƙamshin kuɗi,can na hango Aunty farida rike da zabgegiyar kaza tana ci tana miko min hannu alamar nima na zo,cikin shagwaɓa nace”Eyyah Aunty na Wallàhi yau tsabar murnar wannan biki sam ba zan iya saka komai a ciki na ba, juyawar da zanyi muka haɗa ido da Rukkaiya,can tace”Aunty Safnah ki bani abinci na kaiwa Uncle Umar da sauran Musaddam ne zaɓi fan’s dan kuwa nasan suna nan suna jira,dariya nayi nace”Babu ruwa na nima nan ta kaina nake garin sato muku abinci kar a kama ni babu ruwa na lol ????????.
Gata iya gata wannan rana an nuna ta a fili, dan kuwa da kuɗi suna magana babu shakka aranar sai sunyi magana.
Bayan an tashi kin shiga motar ango *Ummi* tayi mamaki sosai Maimuna take tace”Meyasa ba zaki shiga ba?”.
“Saboda naji suna cewa daga nan gidan su za’a tafi dani ni kuma nafi so na tafi gidan mu muyi bankwana da Umma na kafin na tafi hawaye take sosai kamar anyi mata mutuwa,ganin mutane sun fara cika a gurin yasa ya fahimci akwai abinda ke faruwa,kiran Safnah yayi yace ta duba abinda ke faruwa”.
Aikuwa jin abinda take faɗa yasa ta kira shi tace ya fito yaja hannun matar sa”.
Haka kuwa akayi fitowa yayi yaja hannun ta ,abin mamaki babu musu bare kuma turjiya suka shiga mota,yanzu ma dai a jikin sa ya ƙwatar da ita yana shafe bayan ta yace”kina son zuwa gun Umma ne?”
Cikin Muryar kuka tace”Eh dan Allah ka kai ni gun Umma na ganta dan Allah.”
Ɗago kanta yayi ya sa harshan sa yana share mata hawayan, ita kuwa sandarewa tayi a gurin, tsabar mamaki da al’ajabi.”Shikenan daina kuka zamu tafi ki ga Umma amma sai kin min alkawarin ba zaki yi kuka ba idan muka zo tafiya?”.
Baki na rawa tace”Nayi alkawari”.
“Idan kika saɓa fa”.
“Ka Amin aikin gafara”.
“Idan kin yarda zan sake miki abinda nayi miki ɗazo kin yarda”.
“Eh na yarda.
Kallon driver yayi yace”Kai mu gidan su.
Abin mamaki motacin dake bayan su sai ganin an canza hanya kawai sukayi duk kiran da aka masa kuma babu amsa haka suka hakura suka bi bayan su.
Koda suka tafi da kyar aka ɓamɓare *Ummi* daga jikin Umma tsabar kuka.
Da kuka aka shigar da motar,sam wannan karon ɓace da ita komai ba har suka isa gidan da zasu zauna dan kuwa Mummy tace”a Kaita gidan kawai dan ta samu ta huta.
Bayan barkwanci da tsokana irin na abokan ango da ƙawayan amarya aka watse ya rage daga ita sai Aunty matar Faruq kallon ta tayi tace”Shalele karki mance kin faɗa min cewa”MUSADDAM* shine zaɓin ki kuma dashi kawai kike fatan yin rayuwa haka ne?”
“Eh Aunty”.
“Yawwa to alhamdullah gashi nan Allah ya Mallaka miki shi a lokacin da kika cire tsammani samun sa matsayin mijin aure ko? Dan haka yanzu gyara lamarin kuma ya rage naki idan kika tsaya sanya kina ji kina gani zai canza akalar rayuwar sa zuwa ga wata macan kuma nasan ba zaki so haka ba, saboda haka ki zage dantse gurin nuna masa kulawa ta rayuwa duk da kuwa nasan abin ba mai saukin bane ba amma ki sani da haka kowa ya fara kuma har aka saba, saboda haka ki daure kuma ki zama mai juriya akan duk kan abinda ya bijiro miki dashi,ki nuna masa cewa wannan ba auran haɗi bane a a auran soyayya ne wanda duk zuciyoyi biyu suka yarda zasu rayu a tare, ki zama mai tsaftace duk wani abu naki,ki bashi kulawa kinji shalele, kuma yanzu ki tashi muje na nuna miki kayan da zaki saka”.
Duk jikin ta yayi sanyi jin zancan Aunty, tashi tayi ta ɗauko ɗaya Daga cikin akwatin da aka mata na kayan bacci, ɗaya daga ciki mai kyau wanda haɗe yake dana maza ta fitar mata dashi tace”wannan zaki saka,tashi kuma karki bashi da hannun ki Amma ki ije a inda dole zai gani na tabbatar hakan ba ƙaramin farin ciki zai saka shi ba”.
“In sha Allah zanyi aiki da duk abinda kika faɗa min”.
Da haka Aunty ta tafi ta barta cike da kewar ta.
Shigowar sa kenan bayan ya sallami faruq da matar sa, shigowa yayi bakin sa ɗauke da sallama,Amsawa tayi Murya a dashe, tsayawa yayi a bakin kofar ya buɗe hannuwan sa yace”Ki taso ki min Oyoyo idan kuma baki zo ba ahaka zan tsaya har gobe”.
Babu yanda ta iya haka ta zo ta shige jikin sa, ɗago kanta yayi yace”Har yanzu kukan kike?”
“A a na daina ai”.
Yawwa ƴar kirki to maza shiga kiyi wanka daga nan ki ɗauro alwala ki fito ina jiran ki, jiki a sanyaye ta nufi toilet ɗin kirjinta na dukan uku uku.
Ganin ta shiga toilet ɗinta yasa shima ya nufi nashi ɗakin dan watsa ruwa.
08136746002
Safnah Aliyu jawabi
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITERS’ ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*THE BOOK IS WRITTEN*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idriss (M.I)*
_Jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idriss Musa_
5️⃣1️⃣
_Never ever forget. Always remember that you can grow without destroying others. Always remember that you can grow without sabotaging others. Always remember that nobody must go down for you to rise._
_Always remember that nobody must be shamed or embarrassed for your smile to be sustained. always remember that while others are rising you can also rise. always remember that finding satisfaction in the pain of others will never bring you true happiness._
G✨M world ????
________Koda ta gama fitowa tayi kanta a ƙasa jin alamar babu kowa a ɗakin yasa ta ƙarasa gaban mirro ɗinta da sauri, Humura kawai ta ɗiba ta dan murza a fatarta, hijabi mai girma ta dauko haɗe da shamfiɗa musu Sallaya,anan ta zauna tana zaman jiran shi.
Da sallama ya shigo ɗakin, murmushi yayi ganin yanda ta dukunkune akan sallayar, shafa fuskarta yayi yace”Tashi muyi sallah ko baby Angel?”
“Tom”
Haka suka gabatar da sallar su bayan yayi mata wasu yan tambayoyi game da addini sannan ya kama tsakiyar kanta yayi mata addu’a kamar yanda Annabi Muhammad (S W A) ya umarce mu.
Saida ya gama sannan yace”Baby Angel kina jin yunwa ko?”.
Sunkuyar da kanta kasa tayi dan kuwa idan tace a a tofa tayi karya dan kuwa tun abincin daran jiya ke cikin ta.