MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Ganin tayi shiru yasa ya koma falo ya ɗauko mata abinda ya kawo mata,.har zata mike yace”Baby Angel rufa min asiri karkisa Mummy ta kore ni dan kuwa tace idan na bari kika yi aiki tofa ni sai yanda Allah yayi dani.”
Aikuwa bata san lokacin data tintsire da dariya ba, shi kuwa sosai hakan ya faranta ran sa,sosai dariya yake mata kyau kitchen ya nufa ya dauko musu plate, juye kazar yayi sannan ya dauko cup ya juye madarar, madara ce tacacciya,da kyar ta yarda ya rinƙa bata abaki,Saida ya tabbatar ta ƙoshi sannan yace”Yawwa yanzu sai a ramawa kura aniyar ta ko My baby Angel?”
Kallon sa take dan kuwa sam bata fahimci abinda yake nufi ba, murmushi yayi yace”Nima a baki zaki bani ai kamar yanda na baki
”
Babu yanda ta iya haka tayi ta bashi tana sunkuyar da kai,hamdala kawai yake a zuciyar dan wannan babbar kyautace daga rabbil izzati dan haka na ɗauki alkawarin baki duk wata soyayya wacce zata mantar dake wahalhalun da kika shiga a baya.
Tana gama bashi ta ƙwashe plate ɗin ta shigar dasu kitchen saida ta wanke sannan ta fito,hannun sa sarƙafe da juna, kallon ta yake kallon mai cike da zallar ƙauna,ita kuwa kasa shiga ɗakin tayi ganin yanda ya tare kofar ɗakin,alama yayi mata data zo gare shi,kanta a sunkuye ta ƙarasa,”Baby Angel kinga wancan ɗakin shine ɗakin kwanan mun yanzu ki shiga ki dauko duk abinda kike da buƙata ki zo kinji?”
“In sha Allah”.
Gabaki ɗaya jikin ta a mace yake tsoro da fargaba ne suka cika mata zuciya dan har rawa ƙafarta take, koda ta isa abin mamaki sanye da wannan kayan da Aunty ta bata ta ganshi, duk da itama shi ta saka amma har yanzu wannan hijabin ne dai a jikin ta.
Tarota yayi yace”Ɗan wannan mintinan da bamu tare baki ji yanda naji ba my baby Angel kin zama komai nawa ina miki so kwatankwacin yanda makaho yake son ido,haka kamar yanda mayunwacin zaki yake son nama, kamar yanda uwa take son ɗanta ina son ki sosai Baby Angel ki daure ki so ni koda kaɗan ne dan Allah duk da kuwa nasan wannan auran haɗi ne amma ki min alfarma ki agaji rayuwa ta”.
Banda hawaye babu abinda take sharewa dan kuwa ji take kamar mafarki take ba gaske bane.
“Kinyi shiru”
“In sha Allah Zanyi yanda kace Yaya na”
“Shhhhhh yanzu ba sunana kenan ba ki canza min suna kinji Baby Angel”.
Gabaki ɗaya abubuwan da yake yasa take ƙara ji kunyar sa irin sosai ɗin nan,Aikuwa saida ta canza masa suna sannan hankalin sa ya kwanta, cire mata hijabin yayi yana cewa”Allah baby Angel ke ɗin nan wani lokaci kamar wacce ta fito daga Suleja”.
“Su ƴan sulejan yaya suke to”.
” A a ni dai ba za’aji mutuwarsa Sarki a baki na ba sam dan haka muje mu kwanta”.
Cire hijabin keda wuya gabaki ɗaya niman sandarewa yayi a gurin, ma sha Allah kawai yake iya furta a cikin zuciyar sa, tabbas Allah ya game masa gata babu makawa,komai na haliltar ta masu ɗaukar hankali ne..ganin yanda yake kallon ta yasa tayi saurin fisge hijabin zata mayar jikin ta, karɓa yayi yace”Kwantar da hankalin ki, da haka ya jata har bakin gadon ya zaunar da ita,dayan ɓangaran ya bi ya haye samman gadon sannan ya janyo ta,abin mamaki hawaye take sosai a rikice ya sake janyo ta jikin sa,”Menene meyasa kike kuka?”.
“Dan Allah Yaya *Musaddam* kayi hakuri karka min komai kaji?”
Sauke ajiyar zuciya yayi bai ce da ita komai ba saima kwantar da ita da yayi saman kirjin sa, addu’a ya umarce ta dayi,yana kwance yana shafe suman kanta har tayi bacci, fitar numshin ta yasa ya fahimci tuni har tayi bacci, murmushi yayi yace”Ƙwantar da hankali ki Baby Angel nima babu abinda zanyi miki dan kuwa soyayya ta tayi arha idan na baiyana miki ita nan matata,gyara mata kwanciya yayi ya sauka ya fara haɗa kayan sa,saida ya gama tsaf sannan ya nufi ɗakin ta,akwati ɗaya na kaya ya fito dashi,inda ya ije nashi a falo haka ya ije na ta sannan ya koma ɗakin ya kwanta, bacci kai daɗin gaske ne duk rayuka biyar sukayi cikin wannan dare Umma,Abba , Mummy, Musaddam,Ummi.
Kiran sallar asuba ya tashe su saida suka gabatar da sallah sannan yace ta shiga tayi wanka,tana fitowa shima ya shiga, abayar ta mai kyau ya miƙa mata yace”Maza ki saka jirgin 6:am zamu bi”
Kamar ta tambaye shi inda zasu tafi sai kuma dai tayi shiru ganin babu dacewar haka,sosai yaji daɗin rashin tambayar nata kuwa dan hakan ya nuna masa ta yarda dashi ne.
Saida suka kulle ko ina sannan suka nufi Airport bayan duk ya kira iyayan su ya shaida musu tafiyar na su,Umma da Abba fatan alkairi kawai suka musu, Mummy kuwa sosai tayi faɗa dan akwai baƙi da yawa wa’anda suke son zuwa ganin amarya amma saboda azarɓaɓi zaki tafi da ita, wallàhi zaka dawo ka same ni ne ai.”
Rarrashin ta ya rinƙa yi har saida ta sauko tayi musu addu’a sannan hankalin sa ya kwanta,duk da kasancewar hawa jirgin ta na farko kenan hakan sam bai saka ta nuna ƙauyanci ba duk da kuwa a tsorace take,ganin haka yasa ya janyo ta jikin sa, ƙoƙarin ƙwacewa take,cikin dabara ya nuna mata wata mata kwance jikin mijinta kuma fuskar ta ɗauke da niƙabi yace”Kinga inda ake nuna so ko baby Angel dan haka ki natsu ko kuma suyi mana dariya”.
Haka tana ji tana gani ya rungume ta yana shafe kanta har bacci yayi awan gaba da ita, kiran sunan ta yake a hankali kamar mai raɗa yace”Tashi kinji har mun zo ai”.
Miƙewa sukayi a tare, hannun su sarƙafe da juna kallon sa tayi tace “Nan wace ƙasa ce?”.
“Dubai”.
Murmushi tayi dan kuwa bayan Makka da Madina wannan shine ƙasar da take so sosai.
Wani matsakaicin gida suka shiga mai masifar kyau dan kuwa gidan ya tsaro babu karya, bayan sun aje kayan su sunyi wanka yace”Ta shirya fita zasuyi, abin mamaki aduwa ne a hannun sa da yawa,kallon sa tayi tace”Yanzu daga gida ka riƙo wannan?”
“Sure”.
“Kana son sa ne haka?”
“Eh”
Gabaki ɗaya sai ta rikice jin yanda yake bata amsa a takaice,abin mamaki lokacin da suka shiga gidan babu mota, amma kuma yanzu ga mota mai kyau a harabar gidan.
Haka dai suka shiga, miƙa mata aduwar yayi yace”Ki rinƙa kirga min adadin wanda na sha dan guda goma kawai nake da bukata”.
“Tom”
( Kuma kanaji karna gani a tambaye ni dalilin da yasa yake shan aduwa,idan kina da hali ki sayawa mijin ki ki bashi guda goma ko wacce rana zaki kira ni ki min godiya* )
Restaurant suka tafi ya sayo musu abincin haɗa da abin sha, ganin zuma agurin yasa ta ɗauka dan kuwa tana da buƙatar shi,bayan sun gabatar da sallah sannan suka ci abinci, kasancewar akwai gajiya a jikin ta yasa ta sake komawa bacci ba ita da farkawa ba sai kusan 6:pm zaune ta same shi yana dane danan laptop ɗin sa da alama aiki yake hakan yasa ta gaidashi kawai ta koma ɗakin ta, wanka tayi sannan ta gabatar da sallar magrib, shima dai hakan ce ta kasance saida yayi sallah isha’i sannan ya shigo gidan Kasancewar akwai masallaci a gidan.
Zaune a falon ya same ta hakan yasa ya buɗe fridge ya ɗauko wani abu cikin ƙaramin ruba ya miƙa mata,ƙamshin daya bigi hancin ta ne yasa tayi saurin kallon cikin rubar,kankana ce anyi mata yanka ƙanana sai madara da zuma a haɗe, ɗago kai tayi tana kallon sa,shi kuwa, haɗe girar sama data ƙasa yayin dan kuwa baya son wasa, ganin haka yasa ta fara sha, daɗin sa yasa har ta shanye ba tare da sanin ta ba, murmushi yayi yace”Baby Angel ai ya kare ki bari gobe na haɗa miki wata ko?”.