HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Da Kunya ta kai rubar kitchen.

Kallo ya kunna  musu a laptop har kusan 9: pm sannan ya kashe yace su je su kwanta,sam bata kawo komai a ran ta ba ganin yanda jiya suka kwanta babu komai yasa ta kwantar da hankalin ta,wasu kayan bacci masu mattukar daukar hankali ya miƙa mata bayan ta sake yin wanka yace”Wannan zaki saka kuma bana son ganin wannan hijabin”.

Duk da haka bata kawo komai a rai ba,kwanciya tayi a jikin sa kamar yanda sukayi jiya, ganin haka yasa ya janyo ta daidai kan fuskar sa,hura mata iskar bakin sa yake a hankali yana shafe bayan ta,nan da nan jikin ta ya ɗauki rawa,ƙanƙame shi tayi hakan kuwa ba karamin sake ta yar masa da hankali yayi ba,dan kuwa yana iya jiyo tudun kirjin ta manne da nashi,lips ɗinta ya kama ya fara tsosa cikin salon sa mai rikitarwa,hana shi take son yi, amma babu hali dan kuwa hannun ta duk a kasan nashi suke,haka yasa tana ji tana gani ya gama tsose mata baki tas.

Kallon idanuwan ta yayi yace”Baby Angel dan Allah karki hanani baiyana miki irin so da ƙaunar da nake miki dan Allah kin wannan alfarmar kinji baby Angel ɗita?”.

“In sha Allah”.

tunowa da zancan Aunty kawai yasa taji babu abinda ba zata iya masa ba,kwantar da ita yayi ya shiga wasa da sassan jikin ta,ganin haka yasa nayi hanzarin ficewa daga ɗakin ina ƙwalla kiran Fatima adam ta zo ta haska min fitila karna faɗi lol ????????????????

Safnah Aliyu jawabi
08136746004
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITERS’ ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idriss (M.I)*

_Jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idriss Musa_

 

5️⃣1️⃣

_Never ever forget. Always remember that you can grow without destroying others. Always remember that you can grow without sabotaging others. Always remember that nobody must go down for you to rise._
_Always remember that nobody must be shamed or embarrassed for your smile to be sustained. always remember that while others are rising you can also rise. always remember that finding satisfaction in the pain of others will never bring you true happiness._
G✨M world ????

________Koda ta gama fitowa tayi kanta a ƙasa jin alamar babu kowa a ɗakin yasa ta ƙarasa gaban mirro ɗinta da sauri, Humura kawai ta ɗiba ta dan murza a fatarta, hijabi mai girma ta dauko haɗe da shamfiɗa musu Sallaya,anan ta zauna tana zaman jiran shi.

Da sallama ya shigo ɗakin, murmushi yayi ganin yanda ta dukunkune akan sallayar, shafa fuskarta yayi yace”Tashi muyi sallah ko baby Angel?”

“Tom”

Haka suka gabatar da sallar su bayan yayi mata wasu yan tambayoyi game da addini sannan ya kama tsakiyar kanta yayi mata addu’a kamar yanda Annabi Muhammad (S W A) ya umarce mu.

Saida ya gama sannan yace”Baby Angel kina jin yunwa ko?”.

Sunkuyar da kanta kasa tayi dan kuwa idan tace a a tofa tayi karya dan kuwa tun abincin daran jiya ke cikin ta.

Ganin tayi shiru yasa ya koma falo ya ɗauko mata abinda ya kawo mata,.har zata mike yace”Baby Angel rufa min asiri karkisa Mummy ta kore ni dan kuwa tace idan na bari kika yi aiki tofa ni sai yanda Allah yayi dani.”

Aikuwa bata san lokacin data tintsire da dariya ba, shi kuwa sosai hakan ya faranta ran sa,sosai dariya yake mata kyau kitchen ya nufa ya dauko musu plate, juye kazar yayi sannan ya dauko cup ya juye madarar, madara ce tacacciya,da kyar ta yarda ya rinƙa bata abaki,Saida ya tabbatar ta ƙoshi sannan yace”Yawwa yanzu sai a ramawa kura aniyar ta ko My baby Angel?”

Kallon sa take dan kuwa sam bata fahimci abinda yake nufi ba, murmushi yayi yace”Nima a baki zaki bani ai kamar yanda na baki

Babu yanda ta iya haka tayi ta bashi tana sunkuyar da kai,hamdala kawai yake a zuciyar dan wannan babbar kyautace daga rabbil izzati dan haka na ɗauki alkawarin baki duk wata soyayya wacce zata mantar dake wahalhalun da kika shiga a baya.

Tana gama bashi ta ƙwashe plate ɗin ta shigar dasu kitchen saida ta wanke sannan ta fito,hannun sa sarƙafe da juna, kallon ta yake kallon mai cike da zallar ƙauna,ita kuwa kasa shiga ɗakin tayi ganin yanda ya tare kofar ɗakin,alama yayi mata data zo gare shi,kanta a sunkuye ta ƙarasa,”Baby Angel kinga wancan ɗakin shine ɗakin kwanan mun yanzu ki shiga ki dauko duk abinda kike da buƙata ki zo kinji?”

“In sha Allah”.

Gabaki ɗaya jikin ta a mace yake tsoro da fargaba ne suka cika mata zuciya dan har  rawa ƙafarta take, koda ta isa abin mamaki sanye da wannan kayan da Aunty ta bata ta ganshi, duk da itama shi ta saka amma har yanzu wannan hijabin ne dai a jikin ta.

Tarota yayi yace”Ɗan wannan mintinan da bamu tare baki ji yanda naji ba my baby Angel kin zama komai nawa ina miki so kwatankwacin yanda makaho yake son ido,haka kamar yanda mayunwacin zaki yake son nama, kamar yanda uwa take son ɗanta ina son ki sosai Baby Angel ki daure ki so ni koda kaɗan ne dan Allah duk da kuwa nasan wannan auran haɗi ne amma ki min alfarma ki agaji rayuwa ta”.

Banda hawaye babu abinda take sharewa dan kuwa ji take kamar mafarki take ba gaske bane.

“Kinyi shiru”

“In sha Allah Zanyi yanda kace Yaya na”

“Shhhhhh yanzu ba sunana kenan ba ki canza min suna kinji Baby Angel”.

Gabaki ɗaya abubuwan da yake yasa take ƙara ji kunyar sa irin sosai ɗin nan,Aikuwa saida ta canza masa suna sannan hankalin sa ya kwanta, cire mata hijabin yayi yana cewa”Allah baby Angel ke ɗin nan wani lokaci kamar wacce ta fito daga Suleja”.
“Su ƴan sulejan yaya suke to”.

” A a ni dai ba za’aji mutuwarsa Sarki a baki na ba sam dan haka muje mu kwanta”.

Cire hijabin keda wuya gabaki ɗaya niman sandarewa yayi a gurin, ma sha Allah kawai yake iya furta a cikin zuciyar sa, tabbas Allah ya game masa gata babu makawa,komai na haliltar ta masu ɗaukar hankali ne..ganin yanda yake kallon ta yasa tayi saurin fisge hijabin zata mayar jikin ta, karɓa yayi yace”Kwantar da hankalin ki, da haka ya jata har bakin gadon ya zaunar da ita,dayan ɓangaran ya bi ya haye samman gadon sannan ya janyo ta,abin mamaki hawaye take sosai a rikice ya sake janyo ta jikin sa,”Menene meyasa kike kuka?”.
“Dan Allah Yaya *Musaddam* kayi hakuri karka min komai kaji?”

Sauke ajiyar zuciya yayi bai ce da ita komai ba saima kwantar da ita da yayi saman kirjin sa, addu’a ya umarce ta dayi,yana kwance yana shafe suman kanta har tayi bacci, fitar numshin ta yasa ya fahimci tuni har tayi bacci, murmushi yayi yace”Ƙwantar da hankali ki Baby Angel nima babu abinda zanyi miki dan kuwa soyayya ta tayi arha idan na baiyana miki ita nan matata,gyara mata kwanciya yayi ya sauka ya fara haɗa kayan sa,saida ya gama tsaf sannan ya nufi ɗakin ta,akwati ɗaya na kaya ya fito dashi,inda ya ije nashi a falo haka ya ije na ta sannan ya koma ɗakin ya kwanta, bacci kai daɗin gaske ne duk rayuka biyar sukayi cikin wannan dare Umma,Abba , Mummy, Musaddam,Ummi.

Kiran sallar asuba ya tashe su saida suka gabatar da sallah sannan yace ta shiga tayi wanka,tana fitowa shima ya shiga, abayar ta mai kyau ya miƙa mata yace”Maza ki saka jirgin 6:am zamu bi”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button