MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Ita kuwa yana fita ta shiga cikin ruwan,zaman ta keda wuya ta tsaga ihu tana kiran sunan sa,a rikice ya faɗa toilet ɗin yana tambayar ta abinda ya faru,banda hawaye babu abinda take, nan ya fahimci abinda ke taruwa,rarrashin ta ya shiga yi da nuna mata wannan shine kaɗai hanyar samun waraka kafin zuwa safe su tafi a asibiti,a hankali yake tsomata cikin ruwan tun tana ƙanƙame shi har ta saki jiki alamar ta ɗan daina jin zafin da take ji.
Ganin haka yasa ya fita ya bata wuri dan ta samu ta tsarkake jikin ta.
Zanin gadon ya koma ya ƙwashe sannan ya canza wani,ya gyara ko ina sai tashin ƙamshi kawai kake iya jiyuwa daga ɗakin.
Fitowa tayi ɗaure da towel,kallon ta yake babu ko ƙiftawa,ganin haka yasa ta shige jikin sa tana sauke ajiyar zuciya, murmushi yayi ya rungume ta yana shafe bayan ta,”Jaruma ta Allah yayi miki albarka kinji”.
“Sunkuyar da kanta tayi tace”Amin tare da kai ma Hubby na”.
Kwanciya tayi ya lulluɓe ta da zanin gado,sumbatar goshin ta yayi yace”Bara nayi wanka nima kinji Baby Angel ɗita sai mu koma ko?”
Zaro ido waje tayi nan da nan har hawaye sun cika idanuwan ta,da sauri ya dawo yace”Kwantar da hankalin ki wasa kawai nake miki baby rigima”.
Da haka ya shiga toilet hamdala kawai take ga rabbi izzati dan kuwa samun miji irin wannan ba karamar sa’a bace ba.
Koda ya fito kwanciya yayi kusa da ita da haka bacci yayi awan gaba dasu,basu suka farka ba sai asuba,tashin ta yayi da kyar take taka kafar ta tayi alwala suka gabatar da sallah a tare.
Suna idarwa ya saka mata kaya suka nufi asibiti, ganin halin da take ciki yasa cikin gaggawa suka shiga duba ta, sosai Dr ɗin take faɗa dan kuwa sunyi dace ƴar Nigeria suka tarar a gurin tana aikin dare,ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,sai masifa take masa akan aika aikan da yayi,shi kuwa da gabaki ɗaya a ƙage yake da ya ji halin da take cike yasa banda haƙuri babu abinda ke fitowa daga bakin sa, nasiha tayi masa sosai dan kuwa irin haka ba ƙaramar matsala yake haifar wa ba.
Saida aka gyara mata jikin ta aka mata allurori sannan suka nufi gida bayan sun tsaya sun saya magani, banda shagwaɓa babu abinda take masa dan kuwa tuni ta daɗe da gane yana mattukar so da ƙaunar ta idan haka ne kuwa kamata yayi tayi aiki da maganar da Aunty Farida ta faɗa mata, narkewar da take a jikin sa ba ƙaramar ɗaga masa hankali take ba gashi kuma ba lafiya gare ta ba,da haka har suka isa gida,suna zuwa ta sha maganin ta sannan ta kwanta, bacci take sosai dan kuwa cikin alurorin da aka mata akwai na bacci.
Kwanciya yayi kusa da ita yana kallon fuskar ta wacce tayi fayau sai kuma idanuwan ta da suka shige ciki alamar ba ƙaramar wahala tasha ba.
Shafe fuskar ta yayi yace”Nayi alkawarin zan kula da ke zan baki duk wata soyayya wacce zata saka ki jin cewa ke ɗin ƴar gata ce wannan alƙawari na ne”.
Ko kafin ta farka har ya tafi ya saya mata abinci da kayan ruwa kamar yanda Dr ta faɗa masa,kama daga kankana lemo abarba inibi da dai sauran su, da sunan sa a baki ta farka,rike mata hannu yayi yace”Kin tashi lafiya?”.
“Lafiya kalau Hubby na”.
“Ya jikin naki yanzu?”
“Da sauki zanyi wanka”.
“Dagata yayi a hankali har ta miƙe,abin mamaki sam bata jin wannan zafin yanzu sosai saidai abinda ba za’a rasa ba.
Wanka tayi tayi sallah sannan ya kawo mata abubuwan daya saya mata,abaki suka rinƙa bawa juna abinci har suka ƙoshi, saida suka gama tsaf sannan ya janyo wayar sa ya kira Abba bayan sun gaisa itama ya bata sukayi magana bayan doguwar nasihar da yayi mata sukayi sallama,daga nan suka kira Umma itama dai duk zancan ɗaya ne duk da kuwa ta ji sauyin da aka samu daga muryar ta hakan yasa ta fahimci bata da lafiya, duk da kuwa tana so taji lafiyar yar ta amma kara irin ta mahaifiya yasa ta bita da addu’a kawai.
Kiran Mummy sukayi tana jin Muryar ta tace”Ta tashi ta shiga ciki ta bar inda yake,haka kuwa akayi ta miƙe ta shige cikin ɗaki, tambayar ta tayi abinda ya same ta shirun da tayi ne yasa ya fahimci inda matsalar take, sauke ajiyar zuciya tayi tace”Ki daure kinji ƴata da haka duk muka zama abinda muka zama yau,karki ɗauke ni matsayin suruka ke ƴa tace, kallo ɗaya nake mike da Safnah dan haka ki saki jikin ki dani kinji? Yanzu ki duba cikin ƙaramin akwatin ki akwai sako na aje miki a ciki da yanda zakiyi amfani dashi kinji ƴa ta? Allah yayi miki albarka ya baku hakurin zama da juna sai anjima.”
Gabaki ɗaya kasa magana tayi sai hawayen dake kwarara akan fuskarta,ɗaura hannuwan sa saman fuskarta yayi yana share mata hawaye yace”Jama’a kuji kukan karya bayan kin ƙwace min mama kuma kika wani min kukan gulma Allah kuwa ba zan yarda ba”.
Murmushi tayi ta kwantar da kanta saman kirjin sa tace”Babu abinda zance da kai sai godiya Hubby na Allah ya saka maka da mafificin alkairi,ka ƴan ta ni ka rufa min asiri,alfarma guda ɗaya nake bukata daga gare ka, dan Allah kaji tausayi na ka taimaka min gurin ganin na share hanya ta, ta zuwa aljanna, ka kasance mai yafiya da karɓar uzuri na, ka faɗa min kuskure na idan nayi, ka, duk abinda nayi ba daidai ba ka faɗa min saboda karna maimaita irin sa,idan nayi maka laifi karda ka kai kara na, idan har haƙuri ba zai wadace ka ba,kamin hukuncin daidai da yanda zaka zamu gamsuwa, ni kuma nayi alƙawarin faranta maka daga nan har zuwa ƙarshan numfashi na”.
Ƙanƙame ta yayi yana jin so da ƙaunar ta yana ratsa jini da jijiyar jikin sa.
“Nayi miki alƙawarin haka in sha Allah Baby Angel ba zaki taɓa yin kuka dani ba in sha Allah”?
Haɗe bakin su yayi guri ɗaya,ita kuwa bata hana shi ba dan kuwa tayi imani ba zai wuce gona da iri ba.
********
Kwance take kan katifar ta tana juyi gabaki ɗaya idanuwan ta sun canza kala sunyi ja jazir kamar wacce ta kwana kuka, sallamar mahaifinta yasa tayi saurin gyara ƙwanciyar ta, kallon ta yayi ya sunkuyar da kai, miƙewa tsaye tayi tace”Daddy ka tafi gun ta?” “Me tace maka, ina fata ta amince?”
Zaunar da ita yayi yace”Haƙuri kawai shine mafita dan kuwa mahaifiyar sa ta tabbatar min babu maganar aure biyu cikin rayuwar ɗanta,saidai idan hukunci ne na Allah shikenan babu yanda zata iya amma ita dai tace yayi aure har abadan wannan furuci ba zai fito daga bakin ta ba”.
“Wallahi zan mutu Daddy na idan har ban aure Musaddam ba”.
Daka mata tsawa yayi yace”Ke dakata na gaji da wannan rashin tarbiyyar taki Fairuza duk da kuwa na ɗauki duk ka laifin na ɗaura a kai na, na rashin tsayawa nayi aiki na a matsayi na na uba, rashin mahaifiyar ki yasa nake jin tausayin ki duk abinda kika ce kina so nake miki ba tare da tunanin kyawun sa ko akasin hakan ba, to daga yau abin ya tsaya haka dan kuwa ina fita daga gidan su na kira ƙanina marwan dan su fara shiri zan aura mike Imran tunda ya daɗe yana bibiyar ki amma kike kin kula shi.
“Kuma idan kika yi ƙoƙarin bijirewa umarni na wallahi sai na saɓa miki mtssss aikin banza kawai”.
Da haka ya fita a ɗakin yana share hawaye dan kuwa ba ƙaramin kuskure yayi a rayuwar sa ba,duk dai da sunan gata.
Ita kuwa fitar sa keda wuya ta ɗauko gubar da dama tuni ta ije shine saboda idan taji akasin abinda take son ji ta shanye dan kuwa babu wata rayuwa mai daɗi idan babu Musaddam a cikin ta.
Aíkuwa babu daɗewa ta fara ihun cikin ta, ƴan aikin gidan ne suka fara jiyo sautin Muryar ta cikin sauri aka sanar da mahaifinta, ko kafin su isa asibiti tuni rai yayi halin sa. Wa’iya zubillahi Allah kayi mana ƙyaƙyyawar ƙarshe Amin.????????????????????????