MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

08136746004
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITERS’ ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*THE BOOK IS WRITTEN*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idriss (M.I)*
_Jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idriss Musa_
5️⃣3️⃣
*Keep your problems in perspective. No matter how bad you think your life is, your problems are always small when you think of what others are facing. Cancer, sudden death, losing a loved one, the list goes on. Even on a bad day, you have to realize how fortunate you really are!*
_____Can na hango shi cikin ƙungurumin daji sai magana yake shi ɗaya,bakin wani bishiya mai girman gaske, zagayowa nayi har zuwa gaban sa dan kuwa abin nasa azimun ne, rufe idanuwan sa yayi yana wasu irin sulkullan sa, can kuwa naji itaciyar tayi wani irin ƙara, nan da nan reshan jikin ta suka fara karyewa, a razane ya ɗago yana kallon bishiyar cike da mamaki da kuma tsoro dan kuwa itace itaciyar dake bashi duk wata nasara da yake ganin ya samu ta hanyar bokancin sa, ko kuma nace aljannan dake jikin bishiyar.
Bai gama fita daga firgicin sa ba wani irin halilta mai mattukar girman jiki ya sauka gaban sa bakin sa na dalalar da wani irin jini mai kauri da wari,kallon sa yayi yace”Babu makawa yau komai ya zo karshe kuma komai ya kare, saboda haka kamar yanda duk wani aiki da mukayi a bayan ƙasa tare muke yi shi tofa babu shakka haka zamu tafi tare dan kuwa ba zamu taɓa barin ka ba.
Kafin ya buɗe baki wannan haliltar ya kafa masa baki a wuya, kan kace me tuni ya zuƙe masa jinin jikin sa tas ba tare da tausayi ko jin ƙai ba.
Nan fa ya faɗi yana shure shure cikin mintina rai yayi halin sa.
(Allah kayi mana ƙyaƙyyawar ƙarshe, daga niman maganin ƴar ka kai kuma ajalin ka ta riske ka ba tare da ka tuba ga mahaliccin ka ba,ina son duniya da abinda ke cikin ta zasu kai mu ƴan uwa? Allah ka shirye mu cikin shirin addinin musulunci Amin ya Allah)
Sale kuwa yana nan yana cigaba da niman ilimin sa haɗe da sake nimawa ƴan uwan sa shiriya a gun Allah mai kowa mai komai.
****
Inna Salma Kuwa jiki yaƙi daɗi ga barazanar daukar ta matsayin alƙawarin jini da tayi, a kullum sai sake firgicewa take ga tsufa ga jinya kuma ga mugun aiki, wata rana cikin dare tana bacci wata sharɓeɓiyar majiciya ta biyu ta har ɗaki ta sare ta,kafin gari ya waye tuni har rai yayi halin sa.
Suwaiba jiya i yau dan kuwa babu cuta ɗaya data samu sauƙin ta, gashi babu Uwa ba Uba, babu mai kulawa da ita, wannan rayuwa saidai muce innalillahi wa inna ilaihi raju’un.
Cikin abinda bai fi sati ba har ta kara ƙiba komai ya zauna sai zuba soyayya kawai wanda kullum jin su suke kamar yau aka ɗaura,kulawa sosai take bashi da taimakon Aunty Farida dan kuwa kullum cikin koyar da ita sabbin dabaru take,itama tuni har ta haihu ranar kuwa ba karamin kuka *Ummi* tasha ba dan kuwa taso ace ta zo suna, jin an saka wa yaron sunan *Musaddam* kuwa ai babu zama nan fa suka kira su vidio call aka ta hira abin gwanin sha’awa.
hakan kuwa ba karamar daɗi yake wa mutumin ku ba dan kuwa yana shan zumar sa babu ɗaga ƙafa ????
Yau tunda sanyin safe ta tashi da rigimar ita dai su tafi kasuwa akwai abinda zata saya, duk da ɗunbin aikin dake gaban sa haka ya fita dan faranta rai ta, abin mamaki cewa tayi kar ya biyo ta cikin shagon kawai yayi zaman sa cikin mota,haka kuwa akayi tana shiga ta fido wayar ta ta kira Aunty farida video call, bayan sun gaisa ta shiga nuna mata ƙananun kayan dake gurin,duk wanda Aunty Farida ta zaɓa mata ne take ɗauka kaya da yawa kamar zata bar gari, a haka ta biya kuɗi suka fito,baki buɗe yake kallon ta, kanne masa ido tayi tana murmushi, da haka suka tafi gida, yamma na yi ta fara markaɗe abubuwan ta kama daga Inibi abarba da kankana,madarar ta tacacciya ta samu ta juye a ciki duk da kuwa ba tare ta markaɗe su ba, ƙwaƙwar ta mai kyau haɗe da dabino suma ta zuba ta markaɗe bayan ta jika su sun jiƙu sunyi laushi,suma ta zuba musu madara,nan da nan gidan ya ɗauki kamshi,ɗauka tayi ta saka cikin fridge dan suyi sanyi, taliya ruwa ruwa tayi musu mai ɗankarin daɗi, shi dai sai binta da kallo yake ganin yanda gabaki ɗaya yau ta kasa natsuwa,bayan ta idar da sallar Isha’i ta shiga ta sake yin wanka, a nan ne ta ɗauko kananfarin ta wanda tuni ta jika shi tsawon kwana uku da ruwan sanyi,zuwa yanzu ya jika fiye da tunanin mai tunani, ƙaɗan ta ɗiba ta sha,sauran kuma ta ɗaura saman gas yayi zafi kaɗan sannan tayi tsarki dashi.
(Mata a kula wallahi yanzu ba lokacin kishin hauka bane ba ko kuma tunanin dole sai an mallaki miji ta hanyar boka ko malam, wallahi wallahi kina zaune a gidan ki zaki mallaki mijin ki a hannu ba tare da wahalar da kai ba, ta hanyar tsaftace jikin ki da kuma gyara ko ina, kasancewa cikin kamshi a koda yaushe, idan nace ƙamshi ba ina nufin ki kice dole sai turaran duba ɗaya ba ko dubu goma ba a’a sam akwai turaran ɗari biyu da hamsin wanda idan ke ɗaya ce zai miki kusan wata ma bai kare ba, kankanar hamsin ta isa, wata rana kuma ki saya ayaba shima koda na ɗari ne ba tare da kinci komai ba ki zauna ki cinye abin ki, ko kuma a barba duk dai wanda Allah ya hore miki.wallahi mijinki ba zai taɓa gajiya da ke ba saboda kullum cikin sabon yanayi kike zuwa masa, ina mai tabbatar miki ta hannun sa zaki rinka samun kudin sayan kayan marmari haɗa da kayan kamshi pls mata mu kula da mazajan mu.)
Gaban mirro ɗinta ta zauna ta shafe duk ilahirin jikinta da turaruka masu mattukar kamshi, tana gamawa ta nufi wannan akwatin wanda cike yake da kaya ta zaɓi wani mahaukacin riga wanda bashi da maraba da babu,babu ɗankwali a kanta hakan yasa suman ta suka zubo har gadon baya,koda ta gama shirin kuma sai taji sam ba zata iya fita a haka ba,kiran Aunty Farida tayi ta faɗa mata,ai kuwa nan ta hauta da faɗa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, hakuri ta bata tace”Zanyi in sha Allah”.
Tana gama wayar ta sake feshe jikinta da turare sannan ta fito,tun daga inda yake ya fara jiyo ƙamshin turaran,ganin zai juya yasa tayi saurin buɗe fridge din ta ɗauko dabinon ta ,cikin salo take tafiya,tana wani fari da idanuwan ta,duk da kuwa a ciki jikin ta har rawa yake amma a fili sam ba zaka iya fahimtar hakan ba,saboda murmushi dake kan fuskar ta.
Sakin baki kawai yayi yana kallon ta gabaki ɗaya ta gama tafiya da tunanin sa, tana zuwa kuwa ta rungume shi tana sakin ajiyar zuciya, babu ɓata lokaci shima ya rungume ta, ƙamshin dake tashi a jikin ta yasa gabaki ɗaya jikin sa ya sake, kallon sa take tana kanne ido, haɗe lips ɗin su tayi tana wasa da suman kansa, kasancewar a tsaye suke yasa ya janye bakin sa, dan kuwa babu shakka suna iya faɗi a gurin, zama yayi cikin ɗaya daga cikin kujerun falon, zama tayi a kan cinyarsa ta fara bashi wannan ƙwaƙwar yana sha yana lumshe idanuwansa dan kuwa ba ƙaramin daɗi yayi masa ba, Saida ta tabbatar ya shanye sannan ta jashi har zuwa ɗakin sa, toilet ta nuna masa alamar ya shiga yayi wanka, Mutumin ku kuwa sai wani narkewa yake dan kuwa yau yaga abinda yafi zare tsayi lol ????????.