HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Yana shiga ta fito falo ta shanye na ta abubuwan tas duk da kuwa tana jin tashin zuciya, haka ta daure dan kuwa duk abinda zai faranta wa mijinta rai tofa ba ta damu da ita nata ba sam.

Zaune ya same ta har ta sake canza wasu kayan ta saka kayan bacci masu ɗauke hankali, towel ta ɗauko ta shiga goge masa ruwan jikin sa,saida ta gama tsaf sannan ta dauko turaran jiki ta shafe masa jiki dashi,tana yi tana masa tafiyar tsuntsu a jiki,ganin tana niman haukatar dashi yasa ya ɗaga  ta sama,bai dire ko ina ba sai kan gadon su…….

????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️????‍♀️

08136746004

SAFNAH ALIYU JAWABI
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITERS’ ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idriss (M.I)*

_Jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idriss Musa_

5️⃣4️⃣

*_When your turn finally comes, you’ll see why the delay was inevitable; why you had to wait. Remember, you can’t grow into a butterfly overnight, there is a process attached to it. Embrace every part of it because the process teaches us some valuable life lessons!_*

 

 

_____ Ranar kuwa albarka kala_kala babu irin wacce bai saka mata ba.

Ita kuwa a gare ta wannan yafiye mata komai na rayuwa.

kwance take tana latsa wayar ta,kiran Mummy ne ya shigo yasa ta ɗauka cikin sauri, da sallama a bakin ta,bayan gaishe gaishe tace”Fatan dai kuna cikin koshin lafiya ɗiya ta?”
“Lafiya kalau alhamdullahi Mummy na fatan keman haka?”

“Ma sha Allah”

“Yaushe zaku dawo ne wai? yau kusan watan ku biyu fa”.

“In sha Allah zamu dawo Mummy na nima na ƙosa mu koma ina son ganin ku Mummy na”.

“Karki damu in sha Allah zan kira shi nayi masa magana yanzu ba sai anjima ba”.

“Yawwa Mummy na Allah ya kara girma”.

“Amin Amin”

Da haka suka kashe wayar.

Koda ya dawo sam fuskar sa babu walwala,ganin haka yasa ta tashi ta kama hannun sa ta kai shi har toilet ta taimaka masa yayi wanka sannan ta bashi abinci yaci, sauke ajiyar zuciya yayi yace”Zamu koma gida gobe in sha Allah”.

Wani irin tsalle tayi ta faɗa jikin sa,tana murna, kallon ta yayi yace”Au farin ciki ma kike kenan ko”?

“Gida da za mu koma Hubby na”

“Shikenan ai tunda har kin gaji da zama dani”.

“Haba Hubby ka daina cewa haka ai gida yafi daɗi ina jin kewan kowa da kowa”.

Tashi yayi yace”Muje ki shirya mana kaya”.

Aikuwa tun kan ya rufe baki shige ɗaki.

Washa gari tunda 7:am jirgin su ya ɗaga, tunda suka kira su kan zasu shiga jirgi aka fara shirya walimar tarbar su, gidan su kuwa tuni Mummy ta saka an gyara ko ina fes.

Ko cikin jirgi kasa rufe baki tayi tsabar murna, suna sauka da gudu Safnah ta zo ta rungume ta suna murnar sake ganin juna, kallon ta Umma tayi ganin yanda tayi kyau har wani sheƙi take yasa taji wasu zafafan hawaye suna zuba, rungume ta *Ummi* tayi tace”Umma na nayi kewan ki sosai”.

“Nima ai yakike? Fatan dai yanzu babu wannan rawar kan?”

Tura baki tayi tace”Umma ki tambaye shi idan yanzu ina yi”.

Gabaki ɗaya dariya suka yi ganin dai ga abinda tace ta daina kuma tana yi…

Da haka suka tafi gida,kowa ka gani yana cikin farin ciki har akayi walima aka tashi, kowa sai sam  barka yake ganin yanda *Ummi* ta koma, shi kuwa ganin yanda jama’a maza da mata suke kallon ta yasa ya janye matar sa suka shige cikin gidan su.

Washa gari tunda tayi sallah ta koma ta kwanta, wanda sam ba  haka ta saba yi ba, fitowar sa kenan daga gidan Mummy da mamaki yake kallon ta dan kuwa babu abinda take sai rawar sanyi, cikin sauri ya ƙarasa inda take taɓa jikin ta keda wuya yaji wani irin zafi, jiki na rawa ya kira Mummy kasancewar gidan babu nisa yasa cikin mintina biyu ta shigo cikin gidan, jin yanda jikin ta yayi zafi yasa tace  ya canza mata kaya, suka nufi asibiti.

Cikin mintina goma asibitin ya cika da ƴan uwa da abokan arziki, *Musaddam* banda safa da marwa babu abinda yake, gabaki ɗaya a firgice yake.

Fitowar Dr yasa gabaki ɗaya suka nufi gunsa,rike masa hannun yayi yace”Dr ya jikin matata?”

Murmushi Dr yayi yace”Kwantar da hankalin ka yallaɓai duk ba wani abu bane na tashin hankali, dan kuwa matar ka dai juna biyu gare ta”.

Kasa buɗe bakin sa yayi dan kuwa ji yayi komai ya daina aiki a jikin sa.

Jijjiga masa hannu Dr yayi yace”Yallaɓa lafiya kake kuwa”?

Rungume Dr yayi yace”Ka min albishir mai daɗin ji, Ni kuma nayi maka alƙawarin saka maka da kyauta mafi tsada Dr”.

Kan kace me tuni magana ya zaga dangi ai matar *Musaddam* tana ɗauke da juna biyu.

Saidai tayi kwana biyu a asibiti sannan suka sallame su,Mummy kuwa cewa tayi  ba zata koma gidan su ba saidai ta tafi gidan ta su zauna tare dan ta rinƙa bata kulawa, babu yanda ya iya duk da kuwa ransa a ɓace yake, duk abinda yake tana lura da shi hakan yasa itama ta kasance a tsakanin farin ciki da ɓacin rai dan kuwa sam yaƙi ko saurarar ta, hakan kuwa ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba.

Ganin duk hankalin su baya kanta yasa ta miƙe ta nufin ɗakin sa na cikin gidan, kwance ta same shi, idanuwan sa a lumshe,zama tayi kusa dashi tana shafe fuskar sa, duk da kuwa yaji ƙamshin ta hakan bai saka ya buɗe idanuwan sa ba,riƙe hannunsa tayi tace”Nasan ba bacci kake ba, dan Allah ka buɗe idanuwan ka Hubby na ka ji abinda zan faɗa maka”.

Buɗe idanuwan sa yayi wanda suka koma kalar ja tsabar ɓacin rai yace”Kina jin daɗi zaki yi nisa dani ba?”

“Kwantar da kansa tayi akan cinyar ta tana masa wasa da suman kansa tace”Ni kuwa wani daɗin zanji idan aka ɗaure ni cikin ɗakin da babu haske a cikin ta? Ina wani jin daɗi yayin da jini ya daina gudana a cikin jijiyar jiki? Ina wani jin daɗi yayin da aka fitar da kiffi daga cikin kogi aka saka shi cikin kwarya? Ka yarda dani rayuwa a tare da kai itace rayuwa mai cike da farin ciki da nishadi Hubby na”.

“Karka mance kai ne kace dani duk  hanyar da iyayan mu suka ɗaura mu a kai muddun ba hanyar saɓon Allah bane ba,tofa babu shakka binta itace daidai haka ne?” Girgiza kansa kawai yayi alamar haka ne.

“To meyasa kuma yanzu kake nuna ɓacin rai akan hukuncin Mummy? Bayan kasan cewa nima wannan wani abu ne wanda ba zan taɓa jin daɗin sa ba”kuma ka kwantar da hankalin ka kullum a tare zamu rinƙa ƙwana kaji”.

Miƙewa daga jikinta yayi ya zauna yana cewa”Ta yaya kenan?”.

Murmushi kawai tayi tace”Ƙofar baya”.

Miƙar da ita yayi yace”Kece kyauta mafi girma a rayuwa ta”.

Itama rungume shi tayi tace”Kai ne zaɓi na a koda yaushe”.

Ganin abin na niman canza akala yasa ta zame da gudu ta bar ɗakin tana dariya”.

Sosa kansa yayi yace”Haba har yaushe zan iya jure rashin ki a kusa dani?

08136746004
Safnah Aliyu jawabi
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITERS’ ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idriss (M.I)*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button