HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

“To malam kafin a cire maka rai ni ina da tabbacin za ka raba tawa da gangar jikin da na ta ruhin…” ya ji ance da shi “…wai *MUSADDAM* me kake so ka zama ne? Wace ce wannan wacce take nrman tarwatsa min farin ciki na?”
Tashi *MUSADDAM* yayi jiki babu kwari ya riƙe mata hannu yana wani sunne kai ƙasa dan kuwa ya san ya taro match domin kuwa sam bai san cewa a fili yake furucin nasa ba kuma mommy na wajen.

 

Suna isa harabar asibitin *Ummi* da Maimuna suna shigowa.

Wani irin wawan duka kirjinsu ya bada lokaci ɗaya .

______________________________________________________________________

*Reviewed by: Musaddam Idriss Musa*
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

_Jama’a ku shaida na sadaukarwa da wannan littafin ga *Musaddam Idriss Musa*_

_Reviewed by Musaddam Idiriss Musa_

6️⃣

*Keep your problems in perspective. No matter how bad you think your life is, your problems are always small when you think of what others are facing. Cancer, sudden death, losing a loved one, the list goes on. Even on a bad day, you have to realize how fortunate you really are!*

 

_______ Jin yadda ƙirjinta ya buga lokaci ɗaya ne hakan yasa tayi gaggawar rintse idanuwanta, kallonta Maimuna tayi tare da cewa, “lafiya kuwa?”

Ganin tafiyar na neman ta gagare ta don kuwa har ta fara haɗa hanya yasa Maimuna yin saurin kama hannunta ta zaunar da ita tana yi mata sannu.

Nodding da kai kawai tayi don yadda take jin ƙirjin nata yau kam ya fi na kullum. ƙoƙarin miƙewa take don zuwa ga muradin ranta, ita kuwa Maimuna kallonta tayi tace, “don ALLAH ki ƙwantar da hankalinki”.

Ɗago kai tayi ta kalle ta, gabakiɗaya idanuwanta sun ƙanƙance saboda tsabar kukan da take tun a gidan har zuwa nan, “Maimuna kin san wa kika ce ba shi da lafiya kuwa?”

Murmushin takaici Maimuna tayi tace, “na sani mana idan baki mance ba ai ni ce na faɗa miki ko?”

“Nagode ALLAH da kika tuna da hakan da kanki kafin ni na tunatar dake, amma kin mance da abu guda ɗaya, shi ɗin jinin dake gudana a jikina da jijiyane ne, *MUSADDAM* shi ne cikar buri na, *MUSADDAM* shi ne komai nawa, idan nace komai, to ina nufin komai”.

Jinjina al’marin Maimuna tayi tace, “To mu tafi kafin ki mutu”.

Duk da yanayin yadda Maimuna ta furta hakan ya so ba ta dariya amma sannin cewa yanzu ba lokacin wasa ba ne yasa ta miƙe, daidai lokacin shi kuma *MUSADDAM* yake fitowa. Tafiya yake cike da ƙasaita sai dai duk da yadda yake jin tsanantar bugun zuciyar tasa sam ba zaka taɓa fahimtar hakan a fuskar sa ba saboda dakakkiyar zuciya da ya mallaka. Bugun ƙirjinsa ya ƙara tsananta ne daidai lokacin da *Ummi* da Maimuna suka shawo kwanar da za ta sada su da juna, rintse idanuwansa ya yi haɗe da tsayawa cak a lokaci guda kamar wanda aka zo zarewa rai don kuwa duk dauriyar ta sa yanzun kam jin abin yayi ya fi karfin dakewa da tunanin sa.

*Ummi* kuwa tana hango sa cikin sauri ta janyo Maimuna jikinta, rungumeta tayi haɗe da sunne kanta jikin Maimunan. Duban gurin da yake tsayen Maimuna tayi cike da mamaki take kallon *MUSADDAM*
“lallai wannan duk yadda nake ganin sa cikin mota wallàhi a fili ya fi kyau, tsarki ya tabbata ga ALLAH mahaliccin kowa da komai tsira da amincin ALLAH su ƙara tabbata ga *ANNABI* Muhammad (S A W)”.

Duk a cikin zuciya Maimuna take faɗar wadannan maganganu don kuwa ta san tsaf idan a fili ta faɗa babu shakka yau zasu ƙwance ƙawance da aminiyar tata.

A fili kuwa cewa tayi, “wai mene ne haka kike yi?” Bayan tayi kokarin dakewa tare da basar da wancan tunanin.

Sake rufe fuskarta tayi da hijabin Maimuna ta yadda za ta rika hangensa ta hujin hijabin Maimunan. Wata irin ajiyar zuciya take ta saukewa akai-akai.

Ta ce, “wallahi cikar zatinsa da ƙwarjinin sa a kullum suke min katanga da shi”.

“Friend ba ki ganin yanayinsa? Kalle shi fa ko dariya ba ya yi ta ya kike tunanin na je gare shi? To idan ma na tafi me zan ce masa?”

Murmushi Maimuna tayi tace, “au dama baki da abin faɗa kika taso mu muka zo nan?”

Shiru *Ummi* ta yi ganin ya zo daf da su zai wuce, hannun ta ɗaya tasa ta damƙi kirjinta, gefe guda kuwa wani irin ƙamshi mai samar da natsuwa ne ya bugi hancin su.

Dukkansu lumshe idanuwan su suka yi saɓanin shi *MUSADDAM* ɗin da ya ji kamar ana kiran sunansa da wannan zazzaƙar muryar juye-juye ya fara da waige-waige. Ganin yadda hankulan mutanen gurin ya fara dawowa kansa suna kallon sa ne yasa shi furzar da wata iska mai zafin gaske saboda kunar da zuciyarsa take ciki. Saka hannun sa a aljihun wandonsa yayi ya zaro wayarsa, a daidai nan kuwa handkerchief ɗin dake aljihunsa ya faɗi wanda shi sam bai lura ba.

Yana barin wajen cikin rawar jiki *UMMI* ta nufi gurin da niyyar ɗauka. Dafe ƙafaɗarta da aka yi shiyasa ta ɗago kai jiki na rawa, sauke wata nannauyar ajiyar zuciya *UMMI* tayi ganin cewa mummy tsaye tana mata murmushi, ita ma murmushin tayi kokarin kirkirowa ta mayar mata tare da gaishe ta “ina yini Hajiya”.

Haɗe fuska mummy ta yi tace, “Ni ba hajiyar ki ba ce ba, ki kira ni da mummy kin ji ƴata?”

Nodding da kai kawai *Ummi* tayi tana jin wani irin sanyi cikin ranta, sosai ta ji damuwar ta  kaso casa’in cikin ɗari ta gushe yayin da kaunar matar ta kara shiga ran ta.

“To mummy ki yi haƙuri ba zan sake kiranki da hakan ba”.

Murmushin jin daɗi mummy tayi tace, “me kuma kika dawo yi, ina ɗazu mahaifiyar ki ta ce gida zaku tafi?”.

Cikin natsuwa tace, “Eh mummy maganin da aka rubuta mana ne muka mance da shi.

Haka kawai ta samu kanta da yiwa mummy karya.

Sosai mummy taso fahimtar yanayin ta kamar a firgice take amma gudun raini yasa ba ta matsa mata ba.

Tace, “Ayya! To mu ma yanzu tafiya zamu yi ki daina sa wa ranki damuwa kin ji ƴata”.

“Insha ALLAH mummy na yi miki alƙawarin hakan”.

“Yawwa ƴar albarka” mummy ta amsa cike da jin dadi. Haka kawai yarinyar ke burge ta.

 

*MUSADDAM* kuwa ganin har yanzu mummy ba ta fito ba yasa ya fito daga cikin motar kallo ɗaya za ka masa kasan yana cikin damuwa amma saboda jarumta da juriya irin tasa yasa sam ba lalle ka taɓa fahimtar hakan ba ko da kuwa a fuska ne.

Kallon gefensa yayi tare da ware idanuwansa a daidai lokacin da yayi arba da wata mata tana kuka hannun ta riƙe da ƙaramar yarinya  ga jini yana zuba daga baki da yancin yarinyar da alamun dai kamar hatsari ne suka yi ko kuma mota ta buge ta. Abin mamaki kuma ga ta a cikin harabar asibiti mutane suna ganin ta amma babu wanda yayi ƙoƙarin taimaka mata.

 

Da sauri ya nufi gurin ta ko magana bai yi mata ba ya ƙarbi yarinyar ruga a gaggauce izuwa cikin ginin asibitin ganin yadda numfashin yarinyar ke fita sama sama yasa ya hadata da jikinsa yana gudun yana kwalla kiran Doctor! Nurse! Sam bai yi la’akari da fararan kayan dake jikinsa ba da cewar jinin dake zuba daga jikin yarinyar zai bata masa su.

Mummy kuwa jin muryan *MUSADDAM*. A bayan ta yasa tayi saurin juyowa tana tambayar sa, “lafiya kuwa wace ce wannan?”

Tsabar ruɗewa ma *MUSADDAM* ko lura da wanzuwar mummy a gurin bai yi ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button