HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

_Jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idriss Musa_

*_The end_*

5️⃣5️⃣

“_*Don’t judge a person based on just one particular clip you saw of them. It’s unfair. It could be fake, edited or taken totally out of context. Be mindful. The damage we’re doing to ourselves and others by such opinions can have disastrous effects on us in this world and the next.”*_

________Haka kuwa akayi kullum cikin dare yake shigowa gidan ta buɗe masa ƙofar baya, da asuba ana kiran sallah yake barin gidan, hankali kwance suke rainon cikin su, gani yanda ya kwantar da hankalin sa ga wani ɗan ke ba daya kara yasa Mummy ta fara zargin akwai abinda ke faruwa duk da kuwa bata taɓa kakowa a gidan yake kwana ba,saboda haka ta yanke shawarar sanya masa ido dan ta ga abinda ke faruwa.

Musaddam karami kuwa tuni har ya soma zama,ranar da aka kawo shi gidan Mummy kuwa ya ga gata dan kuwa tsabar ɗauka sa da suke yasa ya fashe da kuka,jin kukan sa yasa Ummi fitowa da gudu tana hararar Safnah wacce yaron ke hannun ta tace”Wallahi baki da kunya yanzu Big bro ɗinki kike wa haka ko?”.

“Aunty *Ummi* tsaya yanzu wai da cikin  kika fito da gudu haka? Wallahi ki daina kin dai ji abinda dr yace ko? Walahi da Big bro yana wajan nan yau da ran ki yayi mugun ɓaci,dan kuwa yanda yake ji da cikin nan ko kansa baya kulawa dashi haka”.

Ɗago kai da zatayi suka haɗe ido ai kuwa bata san lokacin da zufa ya fara karyo mata ba.

Ko kallon su baiba ya janye hannun ta har zuwa ɗakin da take yace” duk abinda zaki yi  na rashin natsuwa ki tsaya iya ke,karki yarda ki min wasa da ɗana dan kuwa akan cikin nan babu abinda ba zan iya yi ba dan haka ki kula”.

Da mamaki taka kallon sa dan kuwa yau itace rana ta farko da yayi mata magana irin haka.

Rungume shi tayi tace”Ni mai laifi ce dan haka a min aikin gafara wallàhi ba zan sake ba nayi alkawari”.

Cire ta daga jikin sa yayi yace”Duk nasan manufar ki kuma nasan abinda kike ɓoye wa tsayin wannan lokaci baki faɗa min ba, kuma ban mance ba,ina sane da cewar auran dole aka miki, dan haka karki damu fata na ki haifa min ɗa wanda zan rinƙa gani a madadin ki daga nan sai ki tafi duk inda zaki tafi ki kuma aure wanda kike so tunda dama can ba ni kike so ba”.

Wasu irin zafafan hawaye ke sauka akan fuskarta,dole yau na faɗa masa abinda ke cikin zuciya ta koda kuwa haka zai saka ya daina ganin daraja ta, buɗe baki tayi da niyyar magana cikin sauri yace”Bana bukatar jin komai daga gare ki amma ki sani ina mattukar kaunar ki tun kafin idanuwa na suyi arba da naki *Ummi* na kuma….
Daka masa tsawa tayi tana hawaye tace”Kai a cikin mafarki ka Fara gani na, ni kuma a zahiri nake ganin ka amma matsayi na bai ka yanda ko da magana nayi da kai ba, nayi rayuwa cikin fargaban rasa ka duk da kuwa nasan wutsiyar raƙumi yayi nisa da kasa, adalilin kaunar da nake maka nayi ciwo babu adadi,nayi kwanan yunwa, kullum cikin tunanin ka, nice tafiya ƙofar gidan ku dan kawai nayi tozali da kai  sanyin idaniya ta,……..nan ta shiga zaiyana masa duk halin data shiga a dalilin sa, rungume ta yayi da ƙarfi ajikin sa yana sumbatar ta, karan tafin daya jine ya dawo dashi hankalin sa dan kuwa tuni har ya mance dasu Mummy suna kallon su ta cctv dake malƙale a ɗakin, gabaki ɗaya kuma sai kunya tasa ya ƙasa ɗaga ido ya kalle su.

Dafe shi Safnah tayi tace”Basar kawai Big bro amma fa Mummy tace zaka kara aure dan kamar wannan tayi kaɗan”.

Binta zaiyi da gudu Mummy tace dawo mara kunya”.

Ita dai kallon su take da mamakin ganin harda Umma  a cikin su, shafe fuskar ta Mummy tayi tace”Allah yayi miki albarka ƴa ta, Allah yasa ki gama da duniya lafiya,tabbas samun ƴa irin ki abin alfahari ne ga ko wani dangi, fatan Allah ya baku zaman lafiya mai ɗorawa,ya raba ki da abinda ke cikin ki lafiya, happy birthday to you ƴa ta”

Sai yanzu ma ta tuna da wani zancan karin shekaru ta, haka ma Umma tayi mata addu’a sannan ta koma baya ta tsaya dan kuwa babu abinda zata iya cewa anan dan kuwa duk abinda zata mata anyi mata wanda ya fishi, shi kuwa kanne mata ido yayi yace”Dama buri na ki faɗa min da bakin ki kuma gashi kin faɗa Baby Angel, idan zan baki duk abinda na Mallaka a duniyan sam ba zan biya ki abinda kike min ba,kin bani so da kauna irin wanda bana buƙatar ƙari,ke ɗin ta daban ce a guri na, dan haka babu abinda zance saidai Allah ya bani ikon kyautata miki, na kuma rike amanar ki daga nan har zuwa karshan rayuwa ta, ki min alkawarin zaki kula dani, zaki rufa min asiri ki ɗauke ni ki saka can cikin lungun zuciyar ki, ta yanda ke kanki ba zaki samu damar fitar dani ba koda kuwa ke da kanki kina buƙatar haka, Happy birthday to you My Heart desire.”

Gabaki ɗaya gurin yayi shiru,kallon sa take gabaki ɗaya ta kasa furta komai sai hawayen dake zuba,hannu ya saka ya share mata hawaye yana cewa”Yau ba ranar kuka bace ba,yanzu ki shiga kiyi wanka ki fito kinji ga lil Sis zata taimaka miki ki shirya akwai abinda zan nuna miki”.

Fita duk sukayi aka barsu daga ita sai Aunty Farida da Safnah, rungume ta tayi tace”Da gaske ne yaya *Musaddam* yayi ciwo sabida ni?  kuma wai wani lokaci har kuka yake shima kamar banda nake yi a baya?”

“Tabbas big bro ya shiga wani irin yanayi na tsawon shekaru saidai kuma bai taɓa faɗa mana abinda ke damun sa ba sai yau da muke ji daga bakin sa, abinda na sani shine na sha zuwa ɗakin sa dan ta yar dashi zuwa sallar asuba, wasu lokutan na kan sameshi yana mafarki yana ambatar yaushe zata iso gare shi,kuma koda na tambaye shi sai yace,”Baya son gulma haka yasa nake tsoke baki na nayi shiru”.

Sauke ajiyar zuciya tayi ta shiga toilet tayi wanka, tana fitowa ta shafa mai sannan Safnah tayi mata kwalliya dan madaidaici, sosai tayi kyau abin ta gwanin sha’awa, leshi ne mai kyau da tsari ta saka,a hankali take sauka a mattatakalar ɗakin, saboda shauƙin so kasa ɗauke idanuwan sa daga kanta yayi har ta ƙaraso, shadda ce kalar leshin dake jikinta ya saka,sosai kuwa kayan suka masa kyau, ba tare da ɓata lokaci ba ta yanka cake  ɗin ta, saida ta fara bawa Mummy sannan ta bashi,nan kuwa ya fara korafi aka ta dariya abin dai gwanin  sha’awa.

Janye hannun ta yayi ya saka mata keys guda biyar,da mamaki take kallon sa kafin ta buɗe baki yayi waje da ita, motoci Masu kyau guda biyu ya shiga nuna mata yace”Wannan duk mallakin ki ne My Baby Angel” sauran keys guda uku kuma ɗaya na Abba ne ɗaya na Umma daya kuma na Maimuna”..

Gabaki ɗaya gurin aka fara saka masa albarka, Musamman Umma.

******

Allah cikin ikon sa ciki ya shiga watan haihuwa ai kuwa daga lokacin ya daina ɓoyewa a falo yake kwanciya da zarar Mummy tayi bacci ya haura ya samu matar sa, sarai Mummy tasan abinda ke faruwa shiru kawai tayi dan kuwa tasan yayi hakuri wata tara ba wasa ba, ni kuwa nace”Allah sarki Mummy ki zo ki bani can hanci na faɗa miki gaskiya” lol ????????

Cikin dare kuwa ta tashi da ciwon mara tun suna yi su biyu har abu ya gagara,cikin sauri aka nufi asibiti da ita, Allah cikin yardar sa babu wani ɓata lokaci ta haifo ƴaƴan ta biyu mace da namiji masu mattukar kyau, wato ranar zo ku ga Musaddam babu Kunya tsakiyar mata sai cewa yake”Dan Allah ayi musu a hankali ƙashin su babu karfi,”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button