MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Ganin abin nashi yayi yawa Mummy ta kore shi waje.
Ranar suna kuwa yara suka ci sunan Daddyn *Musaddam* da Umma suna yayi armashi duk inda ka leƙa kama daga gidan tv, jarida, gidan rediyo, ranar duk labari akan sunan yaran *Musaddam* ake.
Cikin haka Sale yaji wannan sanarwa,ciki sauri ya nufi gidan su, mai gadi kuwa da ƙyar ya yarda ya shiga gidan, shima saboda *Musaddam* yace a barshi ne, kuka yake sosai yana rokon su gafara kan abinda yayi musu daga shi har iyayan sa, sannan yake sanar dashi duk abinda suka faru ashe ma dai basu da dangantaka da juna, a ranar ne *Musaddam* yaji ya sake jinjina lamari Ubangiji dan kuwa ba ƙaramin jijjiga shi labarin yayi ba.
“Babu komai na yafe muku saidai niman tafiyar Ubangiji wanda dama shi gafurur rahim ne, kuɗi masu yawa ya bashi yace”Yaje ya nimi sana’ar yi kuma sun rigada sun zama ɗaya duk da kuwa babu wannan dangantakar da ake tunanin tun farko Allah yasa mu dace”.
Sale kuka yake sosai har ya fita daga gidan.
Bayan an watse daga sunan kowa ya kama gaban sa.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin Ni’ima Allah wanda sam rahamar Sa da ni’imar sa basa gushewa, yara kuwa suna samun kulawa ta ko wacece fuska agun iyaye da abokan arziki.
Soyayya kuwa kullum cikin sake tsurowa yake a cikin zuciyar masoya biyu…..
Safnah Aliyu jawabi
“`Alhamdullah alhamdullahi alhamdullahi..
[ad_2]