HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Ganin haka yasa ita ma ta bi bayansa a kiɗime, *Ummi* ma ji take kamar ta ruga ta bi bayan ba su ko me kuma ta tuna sai gani nayi ta dawo da baya. ɗaukar wannan hanky ɗin tayi tana mai kakkaɓe inda ƙasa ta taba jiki.

Ba tare da wani tunani ba ta kai shi daidai saitin hancin ta tana mai shaƙar ƙamshin sa, ƙamshi mai tsayuwa a rai, ƙamshi mai gusar da damuwar da ta addabi ruhi.

Ai *Ummi* ba ta san lokacin da wani irin ƙayataccen murmushi ya kubuce  mata  ba. Kallon ta kawai Maimuna take don kuwa ta ma kasa furta komai, ga shi ganin *UMMI* da Mummy suna magana kuwa ba ƙaramin mamaki abin ya ba ta ba, “wai da ma *Ummi* kin san mummyn *MUSADDAM* ne?

Janye hannun Maimuna kawai ta yi suka nufin hanyar barin asibitin.

Ji suka yi daga bayansu an kira su da wata irin murya mai cike da nutsuwa da jarumta da cewa, “bayin ALLAH!”.

Gabaki ɗaya *UMMI* ji tayi numfashinta yana niyyar barin gangar jikinta don kuwa har duniya ta naɗe ba za ta taɓa mance gani da jin wannan muryar tun ranar farko ba.

______________________________________________________________________

*Reviewed by: Musaddam Idriss Musa*
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

PERFECT WRITER’S ASSOCIATION????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

 

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

_Jama’a ku shaida na sadaukarwa da wannan littafin ga Musaddam Idriss Musa_

* Reviewed by Musaddam Idriss Musa*

 

7️⃣

 

*Some people don’t realise what they have until it’s gone. Sadly, they’ll only realise it when it’s too late. That’s why gratitude is important. Value what you have. Recognise your blessings. Sometimes the Almighty might take it away from you completely and you won’t get it back!*

 

 

 

_______Juyowa suka yi cikin sauri, ganin ba da su yake ba yasa duk suka sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Cikin sauri suka bar harabar asibitin, shi kuwa *MUSADDAM* bai tashi lura da su ba sai da suka zo dabda za su fita daga get ɗin.

Dafe kansa yayi yace, “kash! Gashi sun fita Mummy kuma tace na kira su”.

Juyawa yayi ya koma ciki, a  ɗakin da aka kwantar da yarinyar samu Mummyn inda ya sanar da ita cewar ɓai gansu ba.

 

Cikin adaidaita kuwa *Ummi* banda shaƙar ƙamshin *MUSADDAM* dake tashi cikin wannan handkerchef babu abinda take, lumshe idanuwanta tayi tana jin wani irin sanyin daɗi da natsuwa yana shigarta ta ko’ina.

Maimuna kuwa Binta da kallo kawai take don kuwa yau ta sake tabbatarwa kanta cewar *MUSADDAM* ya cancanci ayi masa so fiye da wanda *Ummi* take yi masa ma.

Da haka suka isa gida, *Ummi* ko tsayawa ba wa mai adaidaita kuɗi ba tayi ba ta sa kai za ta shige gida, harararta Maimuna tayi tace, “ke wai haukacewa kike neman yi halan?”

Ba tare da ta juya ba tace, “irin wacce kika yi a can asibiti lokacin da kika ga muradin raina ba?…Ai ina kallon ki kuma zaki biya ba shi”.

Tana kai wa nan ta shige gida tana murmushi alamar tsokanarta take, Maimuna kuwa dafe ƙirjinta ta yi tace, “na shiga uku na ashe tana kallo na, tab aíkuwa dai samuwar wancan handkerchef ɗin ya taimaka min”.

Mai adaidaita kuwa duk da bai san abinda suke magana akai ba sai da yayi murmushi, ƙarasawa da ita yayi gida ya juya yayi tafiyar sa, yana ayyana shiririta irin ta ‘yan matan zamani.

Sallamar da *Ummi* tayi kaɗai ya isa shaida maka cewar tana cikin tsantsar farin mciki, da gudu ta rungume umma wacce ke zaune bakin kitchen tana hura wuta.

ALLAH sarki mahaifiya duk da tana cike da fushi da ɓacin ran abinda tayi musu ɗazu amma hakan bai hana ta jin daɗin ganin *Ummi* cikin farin ciki ba.

(”Uwa! Uwa!! Uwa!!! Babu abinda zamu ce ga mahaifiya sai godiya da fatan gamawa da duniya lafiya. Ga mu wadanda tasu mahaifiyar ta rasu sai dai mu yi musu addu’ar saduwa da Annabin Rahama, ALLAH ka jiƙan mahaifan mu, ALLAH ka haskaka maƙwamcin su, ALLAH kasa aljanna ta zama maƙoma ga kowace Uwa. Amin

Lallai Uwa bango ce da ƴaƴa suke jingina a jikinta domin samun sanyi ko kuma sauƙin wata cuta dake addabar su, uwa ita ce inuwar da muke zama a ƙarƙashinta domin shan ni’imantacciyar iska, uwa itace ruwa ga rayuwar ƴaƴanta wanda suke sha domin gusar da ƙishin dake addabar maƙoshin su.

ALLAH ina roƙonka da ka zama gata ga marar uwa, wadanda mahaifiyar su take raye ina muku nasiha da ku kyautata mata da iya ƙarfin ku, dukiyarku lafiyarku da duk abinda kuka mallaka don wallàhi wallàhi wallàhi idan ta tafi ba za ka/ki taɓa samun madadinta ba.

ALLAH ka jiƙa iyayan mu”.????????????????)

Rungume juna suka yi suna masu farin ciki, kallonta Umma ta yi tace,”ni kuwa mene ne yasa ka ki farinciki haka *Ummi* na?

Fari tayi da daradaran idanuwanta tace, “umma yau kam addu’ar ki tayi tasiri matuka na ga *MUSADDAM* gani na sosai umma kalla, nuna mata handkerchef ɗin tayi tana mai ƙara manna shi saman karan hancinta. Da mamaki umma tace, “shi *MUSADDAM* ɗin ne ya ba ki wannan?”

Girgiza kai *Ummi* tayi tace,”a’a umma faɗuwa yayi daga aljihunsa ni kuma na ɗauka”.

“Kenan sata kika yi?”.

Turo baki *Ummi* ta yi tace, “sata kuma umma?

“Eh mana”.

“A’a wallahi, ni dai ba sata nayi ba, ai kayan ALLAH na Annabi ne ko?”

Murmushin wautarta umma tayi tace, “kenan yanzu ke da shi kun zama abu ɗaya?”

Tsalle *Ummi* tayi tace, “yauwa ƴar gari!” cikin sauri ta dafe bakinta jin ƙatoɓarar da tayi, murmushi kawai umma tayi tana cewa, “yanzu ni ce ƴar gari ko *Ummi* na?”

“A’a umma kiyi haƙuri wallàhi suɓucewar baki ne”.

“Ke dai wannan soyayya da kike wa wannan yaron ALLAH yasa idan kuka yi aure ba za ki mance da mu ba?”

Nan da nan hawaye ya cika mata ido rusunawa tayi daidai fuskar umma wacce ita ma jikinta yayi sanyi don kuwa ta san dole wata rana za’a rabu ko da babu aure ai akwai mutuwa tace, “umma na ki sani duk son da nake wa *MUSADDAM* wallàhi umma bai kai kwantanƙwacin yadda nake son ku ke da Abba ba, umma kilarki manta ku ne kuka samar da ni, ku ne kuka rai ne ni, ku ka ciyar da ni kuka shayar da ni, kuka tufatar da ni, kuka nuna min hanyar ALLAH da Manzonsa, Umma ku ne kuka ba ni tarbiyya wace nake alfahari da ita a yanzu, ku ne kuma kuke jure duk wata kuruciya da shirme na ba ku taba gajiyawa da ni ba, shin ta yaya kike saka ran zan mance da ku?”

“….Wallàhi ba na fatan ganin wannan ranar da zan mance da ku ko da kuwa na daƙiƙa ɗaya ne”.

Janyota jikinta Umma tayi ta rungume a tare suka fashe da kuka mai tsuma zuciya da sanya tausayinsu a ran duk wanda ya dube su a wannan yanayin. Domin kallo daya za kayi musu ka fahimci irin tsananin kauna da shakuwar dake tsakanin ‘ya da uwar.

Janye ta daga jikinta Umma ta yi tace, “insha ALLAH za ki samu cikar duk wani buri naki *Ummi* na”.

“ALLAH yasa Umma, nagode sosai”.

“Yanzu ki tashi ki je ki ɗauko abincin ranan da baki ci din ba ki zo ki zauna ki ci tunda yanzu an samu abinda ake so”” cike da kunya *Ummi* ta nufi ɗakin ta sum-sum-sum kai a kasa tana murmushi.

**********

*MUSADDAM* kuwa ba su bar wannan asibitin ba har sai da ya tabbatar wannan yarinyar ta samu cikakkiyar kulawa, mummy kuwa albarka tayi ta sanya masa saboda taimakon da yayi wa bayin Allahn nan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button