MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Ko da suka koma gida babu ɓata lokaci ya shiga toilet don watsa ruwa. Sai da ya shafe kusan sama da mintuna talatin sannan ya fito yana hamdala dan kuwa jinsa yake kamar ya kai wata bai yi wanka ba. Janyo kujerar gaban madubin ɗakin yayi, sai da ya taje sumar kansa Sannan ya shiga shafa mai, turaruka kuwa kamar za suyi kuka don fesa su yake kamar bai san zafin kuɗin da aka cire aka saya ba, sauke ajiyar zuciya yayi yana mai godiya ga ALLAH.
Kaya marasa nauyi na ga ya dauko tare da sa wa sannan ya samu guri ya kwanta. Kwanciyarsa ke da wuya aka fara doka sallama a bakin ƙofar ɗakin, amsawa yayi yana mai jin haushin wannan takura, can kasan zuciyarsa kuwa cewa yake, “wai sai yaushe za’a bar ni na huta ne mtwsss!” shigowa ɗakin tayi cike da natsuwa tace, “yaya ina yini”.
Faɗaɗa murmushin sa yayi don kuwa kaf duniyar nan idan aka dauke ALLAH da Manzon sa sai kuma daddy da mummy babu wacce *MUSADDAM* yake tsananin so sama da ƙanwarsa *SAFNAH*.
Sosai yake sonta don lokacin da take ƙarama ma tare suke kwana, ganin ta fara girma ne yasa ya ɗan rage yi mata wasu abubuwan, kallonta ya yi yace, “ya kike ƙanwata?”
“Lafiya ƙalau Yaya ya jikin naka yanzu?”
“Jiki Alhamdullahi”.
“To, ALLAH ya ƙara sauki. Yaya don ALLAH ka daina tunani da yawa ka ji?” Ka ga kai kaɗai kawai nake da bayan Mummy, kai ne nake fatan ka janyo hannun na har zuwa cikin ɗakin Mijina tunda yanzu Daddy baya nan”.
Kuka take sosai hakan yasa ya ji jikinsa yayi sanyi, riƙo hannunta yayi ya zaunar da ita a gefen gadon bayan shi ma ya tashi ya jingina bayansa da bangon gadon yace, “na yi miki alƙawari zan cire duk wata damuwa a rai na insha ALLAH sai dai ban yi miki alƙawarin zan yi tsawon rai har zuwa lokacin da zaki yi aure ba, domin kuwa ba na da iko da raina, ALLAH kaɗai shi ya san ranar da zan bar gidan duniyar nan, tashi ki je ki kwanta ki huta ke ma kin ji, kar kisa damuwar komai a ranki”.
Tashi Safnah tayi ta fice daga ɗakin tana jin duk wata gaɓɓa ta jikinta tayi sanyi…..
Washhhhh hannu na????????????
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga marubuci MUSADDAM IDRISS MUSA*
*_Reviewed by Musaddam Idiriss Musa_*
*_Life isn’t easy. Don’t expect a smooth ride. There will be road blocks. There will be diversions. There will be detours. But these are not dead ends. The roads ahead may be unfamiliar, unchartered territory but the Almighty has said He won’t test you beyond your capacity._*
_______Dafe kan shi *MUSADDAM* ya yi yana mai jin babu daɗi kan halin damuwar da yake saka ahalin nasa. Daidai saitin zuciyarsa ya dafe tare da runtse idanuwansa yace, “tabbas nan shi ne mazauninki *MY HEART DESIRE* komai runtsi ba za ki taɓa barin nan ba…nan na ajiye ki zan yi tattalinki kamar yanda zan yi tattalin lafiya ta….”
“….Dukda kasancewar ban san ki ba amma ina ji a jikina cewar kina kusa da ni..shin sai yaushe za ki bayyana a gare ni? Zuciyata kullum cikin begenki take ina jin tsoro saboda soyayyarki tana gab da raunata zuciya ta idan har aka yi rashin sa’a ta kai matakin da za ta yi bindiga, wallàhi na san duk inda kike sai kin yi kukan rashina saboda ba za ki taba samun wanda zai kaunace ki da ko da rabin son da nake miki ba…”
“…na riga da na nutse a koramar sonki. Ba na ji ba na gani bare na san mene ne aibun ki, komai kika yi gare ni tasiri zai yi wajen kara so da kaunar ki. Ki taimaka ki fito na ganki domin kuwa kece jijiyar dake samar da daidaituwar bugun zuciya da numfashina”.
Yau ma dai kamar kullum sambatu akan soyayar sa ya cigaba da yi har bacci ya yi awun gaba da shi.
********
A zaune, Mummy ce sai faman haɗe fuska take, kallon ta Safnah tayi tana murmushi tace, “Mummy yau kuma wa ya taɓo mana ke?”
Hararar ta tayi tace, “wato gani masifaffiya ko?”
“A’a Mummy ni fa ba haka nake nufi ba ki yi haƙuri”.
“Hmmm ke dai ki bari wallàhi wata yarinya ce jiya muka haɗu a Asibiti ita ma ba ta da lafiya, wallàhi sosai nayi wa yayanki sha’awar auren ta, wannan maganar tayi daidai da fitowar *MUSADDAM* daga saman benin da zai sauko da ɗakin sa zuwa kasa. Wata irin firgita yayi har yana neman zamewa daga saman benin ya fado, cikin ikon ALLAH ya samu ya riƙe ɗaya daga cikin karafan da ak yiwa benin matokari.
Gabaki ɗaya ji yayi duniyar ta hau juya masa.
Safnah kuwa cike da mamaki ta dubi mummy tace, “mummy yanzu da gaske auren dole za ki yi wa Yaya *MUSADDAM?*
Daƙuwa mummy tayi mata tana cewa,”ke yanzu kina jin daɗin ganin sa gansameme da shi babu mata? Baki masa tsoron faɗawa sharrin zamani?”
“…To bara ki ji wallàhi na yi takaici rashin tambayar wannan yarinyar unguwar da suke ko kuma ma na ƙarbi number ta idan tana rike da wayar”.
Juyowar da Mummy za tayi sai karaf suka haɗa ido da *MUSADDAM* don kuwa sam bata ma lura da wanzuwar sa a gurin ba. Cikin sauri *MUSADDAM* ya fara ƙoƙarin mayar da hawayan dake neman zubuwa daga idanuwan sa.
Murmushin ƙarfin hali yayi yace,”Good morning sanyin idaniya ta”.
Ita ma mummy murmushi tayi tace, “how are you my happiness?”
Lafiya ƙalau Mummy na”.
Kallon sa Safnah tayi tace, “Good morning big bro”.
Shafa kanta yayi yace, “morning my beautiful sister”.
Ganin hawaye na neman zubo mata yasa yayi sauri zama kusa da ita yana mata alama da kar ta yarda wannan hawayan su zubo.
Riƙo hannunta ya yi har zuwa D table sai da suka yi breakfast sannan ya miƙe yayi wa Mummy sallama albarka tasa masa sosai haɗe da fatan nasara a duk abinda yasa gaba yayin da yasa kai ya fice zuciyarsa a nauyaye Safnah ma ta bi bayan shi.
Har yanzu hannun su sarke da na juna har suka fito daga cikin gidan kallon ta yayi yace, “ba na so ki nunawa Mummy rashin dacewar abinda za tayi domin kuwa ganin na yi aure shi ne cikar burinta saboda haka kar mu numlna mata ba ma so kamar yadda ita ma a kullum take ƙoƙarin ganin ta faranta mana to muma wannan karon mu yi mata hakan kin ji lil sis?”
Nodding da kai kawai take tana jin wani sabon kuka yana neman kufce mata, cikin dakiya yace,”ko akwai abinda yake baki tsoro game da lamarin ne?”
Kamar da ma jira take tace,” Yaya ba ka jin tsoron Mummy ta kawo ma ka wacce za ta cutar da kai ka san fa ita Mummy gani take kamar yadda zuciyar ta take da kyau haka na kowa take”.
Murmushi yayi yace, “kar ki damu da yardar ALLAH babu wani abu makamancin wannan tunda a kullum sa albarkar ta da kuma addu’ar ta suna yawo a jikin mu ai shikenan”.
Nodding da kai tayi tace, “ALLAH ma cikin ikon sa ba ta samu ta karɓi number yarinyar da take magana ba, kawai dai tsoro nake kar ta ƙara haɗuwa da ita”.
“Kar ki damu ƙanwata idan har haɗuwar su shi ne mafi alkairi ALLAH ya tabbatar”.
“Amin” ta amsa a sanyaye.
Da haka suka yi sallama sai da ta ga fitar motarsa daga gidan sannan ta koma cikin gida tana mai ƙara godiya ga ALLAH daya ba ta ɗan uwa irin *MUSADDAM* da sam ba ya son ya ga damuwar daya cikin ahalinsa.
**********
*Ummi* kuwa tunda ta tashi tayi sallar asuba ba ta yarda ta koma bacci ba. Wanka tayi ta dauko doguwar rigarta mara hannu ta saka gami da fesa turare kawai tayi ta fice daga gidan. Umma kuwa tana kallon sanda ta fice din girgiza kai kawai tayi ta cigaba da aikinta.