MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

Cikin mintuna ƙalilan ta karaso gurin da take son zuwan. Sauke ajiyar zuciya tayi don kuwa ba ƙaramin gudu taci ba, kasancewar hada gudu da sassasafa tafi yawa a tafiyar tata kuma daga gidan nasu akwai ɗan nisa da wajen kadan, hango masallacin dake kusa da gurin tayi aikuwa cikin sauri ta nufi bakin fanfo, kafa bakinta tayi sai da ta ji ta ƙoshi sannan ta sarara.
Komawa inda take ɓoyewa tayi tana jiran fitowarsa, aíkuwa ba ta gama rufe baki ba ta ji mai gadin gidan yana ƙoƙarin buɗe kofar get ɗin.
Ƙara kallon inda take ɓoye din tayi sai da ta tabbatar babu wanda zai iya ganinta sannan hankalinta ya kwanta.
Fitowar motar daga gidan yasa *MUSADDAM* jin duniyarsa ta tsaya cak, gabakiɗaya ji yayi wani irin nutsuwa da farin ciki suna shigar sa. Nan da nan kuwa ya faɗaɗa murmushin sa ta yadda har sai da maigadin dake tsaye a gefe yana daga masa hannu ya lura da sauyin da ya wanzu a fuskar tasa. Hamdala yake wa ALLAH cikin zuciyar sa don kuwa ya daɗe bai ji irin wannan yanayin ba da haka ya wuce *Ummi* wacce take maƙale jikin bishiya gabakiɗaya hawayen ya gama wanke mata fuska, wace irin masifa ce wannan? Ganin ya wuce yasa ta share hawayanta ta nufi gida.
Tana shiga gida ta tarar da Maimuna zaune a kofar ɗakin ta.
Hararar ta tayi tace, “yau kuma gulmar ce ta motsa yasa kika wani yi sammako haka?”
Dariya Maimuna tayi tace, “Na dai ji saboda kin tafi baki gan shi ba ne yasa kika zo za ki sauke mana bala’i a kai”.
Murmushi ita ma tayi tace, “to yar bakin ciki aíkuwa dai baki faɗa daidai ba don kuwa na gan shi gani na sosai ma”.
Hararar ta Maimuna tayi tace “shi ne ba ki jira ni na zo mun tafi tare ba ai wannan bakin ciki ne, saboda kin ga yana dakyau ne yasa kike ɓoye mana shi ko?”
Cak wani abu ya soki kirjin Ummi, nan take kuma yanayinta ya sauya….
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????
( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*
_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idiriss Musa_
9️⃣
*No prayer goes unanswered. Don’t rush things. Good things take time. Have patience. Allah loves believer who is patient.*
*When u try to rush things, u indicate that u don’t trust Allah. Remember, He is listening to u. He will shower on u the blessings that u never thought possible*
______Ganin irin kallon da take mata yasa tayi saurin miƙewa tana cewa,”ke dalla baki san wasa ba ne?”
Fuska a murtuƙe tace,”ba na son irin wannan wasan kuma ke ma kin san haka”.
“Na tuba a gafarce ni”.
“Shikenan amma gaskiya da gaskiya karki ƙara ba na so”.
Kama kunnuwan ta Maimuna tayi, tana mai nuni da tuba tace, “sorry sweet friend”.
Shigewa ɗakin Umma *UMMI* tayi can kuma sai ga ta ta fito hannunta ɗauke da kofuna guda biyu dayan hannun kuma kwano ne mai dauke da ƙosai, ajiyewa tayi da sauri tana yarfe hannun tace,”washhhhh hannu na”.
Dariya maimuna tayi tace, “wannan raki naki wallàhi zan so ganin yadda za ki yi idan kika yi aure”.
Murmushi kawai *Ummi* tayi tana cewa,”wallàhi aiki zan yi sosai da sosai”.
“Au kice yanzu mugunta kawai kike wa Umma”
Tun kan ta karisa maganar ta ta *Ummi* ta dauki murfin ƙwanon ta jefe ta da shi. Dariya duk suka yi, a tsanake suka gama karyawa sannan *Ummi* ta shiga ɗaki, cikin kanƙanin lokaci ta fito sanye da uniform ɗin makarantar islamiyar su, sai yanzu na kai duba na ga kayan dake jiki Maimuna naga ashe uniform ne ita ma ta saka, sallama suka wa Umma suka nufi makaranta.
Cike da natsuwa suka tafiya suna hira abin su, duk kansu kuwa fuskokinsu a lulluɓe suke da niƙab, kallo ɗaya zaka musu ka ji sun burgeka saboda yadda yanzu zamani ya canza abu ne mai matukar wahala ka ga budurwa tana zuwa islamiya a wannan lokacin cikin kuma shiga ta mutunci bisa tarbiyyar addini.
Suna isa makarantar cikin sauri suka shige ajin su kasancewar yau malam Yunusa ne cikin ajin, gabaki ɗaya*Ummi* a tsorace take ganin wannan malamin don kuwa sam ba ya musu da wasa musamman idan suka yi lattin zuwa.
Har za ta zauna ta ji ya kira sunanta muryar sa cike da hassala yace, “ke *Maryam* ɗago kanta ta yi tace,”Na’am malam”.
“Zo nan”.
Kallon gefen Maimuna tayi hawaye gabakiɗaya ya gama cika mata ido, jiki a sanyaye ta ƙarasa kusa daga nesa kadan da inda yake a gaban allon, rusunawa ta yi kana a marukar tsorace, baki na rawa tace, “malam ga ni”.
“Na gan ki ai ko dai kin ga na yi miki kama da makaho ne!?”.
Girgiza kanta tayi tace,”A gafarce ni malam, ka yi hakuri don Allah”.
“Ba a zo nan ba tukunna. Wai ke me kike ɗaukar kanki ne? A tunaninki kin fi sauran daliban makarantar nan ne da har za ki makara kuma ki nemi kaucewa hukunci, kyau kika fi su ko nasaba?”.
Ɗago kanta ta yi tace,”A’a malam babu ko ɗaya ai dukkan mu ALLAH ne ya halicce mu kuma babu wanda yafi wani a wajen sa sai wanda ya fi tsoronsa da kuma kiyaye duk wani sharaɗi da ya gindaya akan bayin sa, malam wannan karantarwar kune, idan wani laifin nayi don ALLAH malam ka yi hakuri ba zan sake ba”.
Tsaki yayi wanda *Ummi* ta ji kamar a tsakiyar kanta ya yi wannan tsakin, “sai wani abu take sum-sum kamar ta ALLAH nan kuwa zuciya bakiƙirin take wa ma yasan abinda kike aikatawa a bayan fage?”
Ɗago kai *Ummi* tayi kamar zata mayar masa da maganar ta sa kome ta tuna kuma kawai sai tayi shiru hawaye na tsiyaya kan fuskar ta.
Kallon ta ya sake yi a fusace don kuwa yaso ace ta amsa domin kuwa babu abinda yake so da ƙauna sama da ganin ya wulaƙantata haka kawai ya ji yarinyar ba ta masa ba, yace “na ɗauka rashin kunya za kiyi min ai irin wanda iyayan ki suka koya miki”.
Murmushin takaici *Ummi* tayi tace,”me zai sa nayi maka rashin kunya Malam bayan ALLAH da manzonsa sun umarce ni da nayi muku biyayya?…”
“…Sam ba zan yi maka rashin kunya ba ko da kuwa hakan sabo na ne, abu ɗaya kawai nake so ka sani shi ne duk wanda ke cikin wannan aji yasan wanda akayi wa tarbiyya gurɓatacciya da wanda aka yiwa tarbiyya na gari….”
“…Malam kaci albarkacin ALLAH da Manzon sa amma ina mai baka shawara da karka ƙara yarda zancenka ya kai gun iyayena don kuwa ba za su ɗauka ba”
Duk wannan maganar da take har yanzu a tsugune take gaban sa kuma har yanzu hawaye bai daina malala daga idanuwanta ba”.
Zaro wata zabgegiyar bulala yayi zai tsula mata cikin azama Maimuna ta rike bulalar tana cewa, “malam idan har zaka doke ta to fa sai dai ka fara ta kaina. Malam me *Ummi* tayi maka haka?…”
“…A iya sani na babu wani laifi da tayi maka amma kullum cikin wulaƙanci da tozartata kake wai menene dalili?”
Cike da fusata ya fusge bulalar yana huci. Sake ɗagawa yayi da niyyar zuba musu dukkansu biyun cike da izza ya ji ance, “idan wannan bulalar ya taɓa ko da hijabin ɗaya daga cikin yaran nan wallàhi sai ka yi gidan yari,”.
Yana gama faɗar haka yayi gaba abinsa kamar ba shi ne yayi wannan maganar ba, kai idan ma ba lura kayi sosai ba sam ba za ka taɓa zaton na shi ne yayi maganar ba, tafiya yake yana waya hannun sa daya cikin aljihun wandon jins dinsa.