BAKAR INUWA 59

Episode 59_*
………Bayan kwanaki biyar da wannan magana Bappi ya shirya da kansa yaje har masarautar Bina sukai magana da mai-martaba, sai dai bai sanar da shi
ainahin dalilinsu game da sihiri dake tare da Ramadhan ba. Ya nuna masa suyi hakanne kodan gudun abinda zaije ya dawo ga mutanen ƙasa akan kallo da
fasararar da zasuma al’amarin. Da yake mutum ne mai fahimta kuma yayi matukar yarda da Bappi a take ya amince ya kuma gamsu. Sai dai ya tsuke bakinsa ko
fulani bai tunkara da zancen ba.
Haka shirye-shirye ya cigaba da gudana har biki ya rage baifi saura kwanaki takwas ba. Su gimbiya Su’adah nata shirye-shiryen fara sanarwa a gidajen
redio da television Pa ya dakatar. Cikin ɓacin rai ta nema dalili yace idan lokaci yayi zata sani ai. Acan bangaren mai-martaba ma ya dakatar da Fulani da
Adda Asmah, dan koda mijinta ya tsawatar shi da yake ya zama mijin tace batajiba, saima tujara data zuba masa gwargwadon iyawa shiko ya sanarma mai-martaba
da dama shine ya bashi umarnin shima.
Wannan abu ya cuɗa musu zuciya. Babu kunya Gimbiya Su’adah harda kai karar Pa gaban su Bappi. Anne zatai magana Bappi ya girgiza mata kai, yace Gimbiya
Su’adah taje zaiyo magana da Pa. Sai dai har yau da ya rage saura kwanaki biyar basuji komai daga bakin Bappin da suka san zai iya yiwa har mai-martaba
magana ya janye sharaɗin daya sharɗanta akan duk wanda yay wani abu babu umarninsu a bakin auren Fulani ne. Tashin hankali kennan da ba’a saka masa rana.
Domin kuwa wannan furuci na mai-martaba ya matuƙar birkita kowa a cikinsu har Ramadhan ɗin kansa da Gimbiya Su’adah ta kira a waya ta sanarma komai lokacin
yana office. Da wannan ɓacin ran ya tabbatar mata zai shigo gidan da dare dama Bappi nata damunsa da son ganinsa ya sharesa.
GOVERNMENT HOUSE..
Yau kam da wuri ya shigo gida saboda son zuwa Taura house da anyi magrib. Raudha najin shigowar motocinsa kuwa ta mike daga falo inda suke zaune suna
tattauna tsare-tsaren bikin Bilkisu da ayanzu ta zame mata ƙawa dan dama bata da su sai school mate kuma ita iyakarta a gaisa babu aminiya. Saurin riƙota
Bilkiau tai ta zaunar. “Ni banga amfanin wannan wasan ɓuyan da kike da shi ba, kiyi zamanki dan ALLAH karma ya samu kafar rainaki dan zai ƙara aure ko ya
zata wani kishinsa kike ma”.
Kamar Raudha zatai kuka sai dai komai batace ba ta koma ta zauna ɗin. A haka Ramadhan ya shigo ya samesu.
Akan Raudha ko ya fara sauke idanunsa, itama anyi sa’a kallon nasa take. Lokaci ɗaya zukatansu suka harba cikin bugu mai tsanani. Raudha da taga
ya rame mata a ido sosai sai dai ya ƙara haske da ƙyau ta fara janye nata idanun fuskarta na nuna wani yanayi mai wajalar fassara. Shiko ido ya ɗan tsura
mata tamkar mai nazari ko kuma yau ya fara ganinta. Sosai ya ga ta ƙara masa girma da cika. Dan duk da ciwo da take fama da shi a watan nan baki ɗaya saita
kara buɗewa tai ƙiba da girma. Sannan komai nata ya ƙara girma ga haske tayi sosai mai tafe da wani sirrintaccen ƙyawu da duk hassadar mai hassada bai isa
mata kallo guda ya ɗauke ido ba.
Kansa ne yaji ya sara masa. Yay saurin janye idanun a kasalance, sai kuma yay ƙoƙarin barin wajen kamar da ƴar sassarfa dan ko gaisuwar da Bilkisu ke
masa bai amsa ba. Ƙofar ya maida ya rufe tare da jingina a jikinta lokcin da ya iso bedroom ɗin nasa. Ya ja ajiyar zuciya da sauke nanauyan numfashi
idanunsa har sun kaɗa sunyi jajur. Ya jima a wajen tsaye kafin yaja kafafunsa da ƙyar zuwa toilet, agogon kawai ya cire ya sakarma kansa shower. Sai da yay
sharkaf daga shi har kayan dake jikinsa sannan ya ragesu yay wanka….
Raudha da dama a cikin yanayi. dauriya take zaune a wajen ta miƙe da gudu tabar wajen hanunta toshe da bakinta. Da sauri Bilkisu ta bita har cikin
toilet data shiga. Amai ta shiga kwarawa tamkar zata amayar da hanjin cikinta. Hankalin Bilkisu ya sake ɗagawa matuƙa ta riƙe Raudha. Sai da komai data
ɗanci ya fita tas sannan aka samu lafiya. Bilkisu ta tamaka mata ta gyara jikinta da wajen suka fito tana jera mata sannu.
Cikin sauke numfashi a wahale tana kaiwa kwance ta ce, “Kai aunty B ƙamshin turare nan na Yaya babu daɗi”.
Sosai Bilkisu ta zaro idanu waje, sai kuma tace, “Kutt Aunty Raudha ƙamshin Boucheron ɗinne baida daɗi? Anya kuwa kin shaka dai-dai?”.
“Ni wlhy lafiya lau na shaƙa, kuma dai tun yashe muke zaune a falon na ƙamshin komai bai dameni ba sai daya shigo ne ƙamshin turaren nan mai kama da
ka…..”
Da sauri Bilkisu ta ruƙe mata hannu tana dariya, “Uhmm to lallai Taura grandchild bai zo da wasa ba.”
Sam Raudha ba wani fahimtarta tai ba. Bakuma tabuƙaci ba’asin mganar ba tama lumshe ido dan barci ke ɗan figarta ga kanta daya fara ciwo.
TAURA HOUSE
Cikin matuƙar bayyanar tashin hankali Ramadhan ya ɗago yana duban Bappi da ya gama masa jawabi. A take idonsa ya rufe yama manta da wanda yake
tare.
“Gaskiya bazai yuwuba Bappi, duk ma wada yake tunanin sharɗanta hakan ya janye dan ba yarda zanyi ba. Tayama kamar ni za’ace a ɗaura aurena a sirri
sai kace wani funafunci? Na muku biyayya na amince da zabinku kukai yanda kuke so nima dole a barni nai yanda nake so akan nawa zaɓin. Sannan maganar events
banajin akwai ɗaya da za’a janye a ciki, ba sai kun dinga nuna hassadarku da adawa aka dangin mahaifiyata zan san kun isa da ni b…..”
Ji kake “tauuuu!!” Wani bazafaren mari ya sauka a saman kuncin Ramadhan har sai da ya kifa kamar zai faɗi. Pa da yake a fusace zai ƙara masa Bappi ya
dakatar da shi. “No Basheer barsa barsa. Kai Ramadhan mu kake faɗama muna adawa da hassada da dangin uwarka!!”.
Har yanzu hanunsa a saman kuncinsa dan da gaske marin yay matuƙar ratashi. Cikin ƙanƙanin lokaci ya sake birkicewa gaba ɗaya, idanunsa suka rufe ruf.
“Idan ba hassada ba a gayamin mi kuke musu? Kun rabani da su komai sai ku, tun ina 2years a rabani da uwata tayi kawaici ta bar muku amma hakan baisa kunga
haƙurinta da kawaicinta ba. To wlhy daga yau ku sani ta ƙare, idan kuma kunce a’a to muzuba mu gani!!”.
Ya ƙare maganar cikin ƙaraji da nufar hanyar fita.
Da sauri Pa ya miƙe cikin wani irin fushi yay kansa shima. Sai da Bappi yay azamar riƙo hanunsa yana girgiza masa kai. Duk yanda Pa yaso yin
magana Bappi ya hana shi, ganin yanda jikinsama ke rawa sai kawai ya rungumesa yana shafa bayansa murmushi na subuce masa na tsantsar zafin da yakeji a
ransa. Da wahala kaga fushin Bappi. Mutum ne mai yawan fara’a da dattako, akoda yaushe fuskarsa ɗauke take da murmushi. Duk abinda kaga faɗansa akai an
ƙuresane.
GOVERNMENT HOUSE
Baƙaramin faɗuwa gaban Raudha dake zaune a gado tana karatu yayi ba. Babu haske mai yawa a ɗakin. ta zabi tai zaman karatu ne kafin lokacin da zata
tashi ganawa da UBANGIJI ne. Ta zaro manyan idanunta akan Ramadhan daya shigo a tsananin fusace. “Innalillahi…..” har ƙarshe take ambata a jajjere harya