MY LADY BOSS

MY LADY BOSS 9

Ad

_____


Idan kin San kan ki baxai ɗau abun dake ciki ba,bazaki iya jura ba ,don Allah kar ki karanta ki dawo mun da zancen kutumelesi…ban san wani kitimurmura labarin Romantic ne👌haka kema idan kin san zaki saya ne don ki fitar mun na yafe ki adana kuɗin ki, kar ki fitar mun adawo mun da zancen gntlw…..masoya na billions naji saƙon nin ku gareni ina gdy Allah yabar🫶

Free page zai ƙare a page 10…ku hanxarta wajen biyan kuɗin littafin LADY BOSS domun jin daɗin ku na cigaba da karanta wannan labari , kin shirya biya?? Na shirya! To yanda tsarin biyan ya kasance… Regular payment ₦300 vip payment₦500 special payment ₦1000…zaku iya turo da kuɗin ku ta wannan asusun bankin 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank…ko kuma ki tura katin MTN naki ta wannan number 08081202932…Idan Vtu trnsfer ne ki tura ta wannan MTN number 09061466409 sai ki tura da shaidar biyan ku duka ta wannan WhatsApp number 08081202932 asha karatu lafiya…

SADAUKARWA GA MUTAN ZAZZAU gami da godiya ga masoyana billions ko trillions ne gdy duk😍😂


“Girgiza kai kurum Sumayya tayi a zuciyar ta tana cewa ” To Sumayya ya kika iya? Dole kiyi haƙuri ki jure mawa duk wani tijara da cin mutunci , idan bakiyi haƙuri ba ya zakiyi ? Zaki bar Umman ki da yunwa ne ,kece kaɗai gare ta kece mai nemo mata dole . Yarinya wa kike nema ? Nan inda kike nufa ba hanyar Part ɗin Hajiya bane , Part ɗin Boss ne”. Juyowa Sumayya tayi tana kallon wacce take mata maganan Muryar na ba cikakkiyar bahaushiya ba. Ohk to Don Allah zaki iya kaini Sasan Hajiyan gidan?”. Eh ba damuwa taho muje! A sanyaya Sumayya ke bin Oruma tana tafe tana kallon ikon Allah komai na gidan abun burgewa ne , ga kyau da tsari , wata ƙofa ne ta buɗe tana ɗaga labulen mai laushin gaske , dark Blue Oruma tana kutsa kanta ciki tare da Sallama ,nan Sumayya itama ta shigo tana bin ta a baya… Kaman yanda Ta zube Gaban Hajiya Juwairiyya tana yin ƙasa da kanta kaman baiwa a gaban gjiyar ta yasa Sumayya cewa ” Barka da Rana Hajiya?’.

Ɗagowa tayi tana kallon Sumayya , wanda taji gaban ta ya faɗi daranmmm , sai ta kauda kanta tana kallon Oruma kana ta motsa bakin ta da kyar cike da izza tana cewa ” Oruma ina aikin dana saki? Kin ɗebo jiki kin dawo, kin san Gobe ne dawowar Su Fahad da Nurƙalby na ko?”. Cikin rawar murya Jidda Oruma tace ” Eh Hajiya na sani, na rakota ne na nuna mata nan Part ɗin ki. Shiru Hajiya Juwairiyya tayi kana tace ” Ok you are free to Go”.

Miƙewa Oruma tayi tana fichewa cikin sauri tare da nufar inda hjy Juwairiyya ta umarci taje. Kusan mintuna biyu da fitar Jidda Oruma Hajiya Juwairiyya ta ɗari da idanun ta ,tana kallon Sumayya wanda anan ma Ita take kallo haɗa ido sukayi nan take taji wani Abu yayi circulating blood ɗin ta game da Sumayya ,fara magana tayi cikin Muryar mai ɗauke kamala tana cewa ” Ammm kaman na san ki?”.

Kallon ta Sumayya tayi kana ta ɗan girgiza kanta alamun a’a …ɗan caɓa baki Hjy Juwairiyya tayi kana ta miƙa hannun zuwa glasscup ɗin dake gaban ta tana kaiwa bakin ta …bayan tasha ruwan ne ta aje tana cewa ” Lyk i know this face in somewhere else”. So mah lady any thing you want from me?”. Aƙwai abun da kike buƙata?”.

A hankali Sumayya ta fara cewa ” Eh Hajiya nazo ne ki taimaka ki ɗauke Ni aiki gidan ki”. Aiki?? Kaman yaya kenan? No no it’s too late ,yanxu na daina ɗaukar ma’aikata Cox basu da amana , saboda ba ko wacce ma’akaciya ce Son ke buƙata ba , may b yace baki masa ba, Kuma ina da ma’aikata da yawa wanda bana buƙatar ko wacce ƴar aiki yanxu.

Wani irin ƙwalla ne ya ciko idon Sumayya cikin sauri tace ” ki taimekeni Hajiya , kona sati biyu ne ko ɗaya nayi maki aiki ki biyani ,Ni baƙuwa ce ban san kowa anan ba , kima Allah ki taimaka idan ya dawo yace baya buƙata na sai na tafi…..ta ƙare maganan hawaye na sauko mata sharrrr….. Ganin haka yasa Hajiya Juwairiyya cewa ” Ina ne gidan mahaifin ki?”.

Wani irin bugawa ƙirjin Sumayya yayi ,a hankali tace ‘ Abba na y rasu, daga Lagos muke ,bamu da kowa anan , dagani sai Umma na , kwatanta mata gidan da suke haya Sumayya tayi ,wanda nan Take Hajiya Juwairiyya ta gane gidan Hayan mlm sabo ne.

Ad

Shiru Hajiya Juwairiyya tayi tsawon lokaci kana ta buɗe murya da ɗan ƙarfi tana kirar Hajara ! Hajara!! Cikin sauri wacce aka kira Hajara ta fito tana zubewa gaban ta da cewa ” Na’am Hajiya Gani .

Ga sabuwar ma’aikaciya nan na ɗauka , ki nuna mata bedroom ɗin Son ta gyara . Tare da gabatar mata da duk aikin gidan da tsare tsare”. Anan zaki rinƙa kwana ko can gida zaki na rinƙa komawa?”. A’a gida zan rinƙa komawa da safe na rinƙa zuwa”.

To naji amma yau ki koma gobe idan kin zo bazaki koma ba sai jibi, saboda dawowar babban mutum Alh DR Abdullah yana hanya Khamal kuma zai taho yau!.

Wani irin dammm ƙirjin Sumayya ya buga a zuciyar ta tana cewa ” Wani Khamal ɗin , ohk na gode Hajiya Allah ya saka da alheri. Yowa kuje ,shine Amsan da Hjy Juwairiyya ta basu Hajara na gaba Sumayya na bin ta a baya’.


Tsayawa tayi tana kallon Hoton shi ,wanda take jin zazzafan So da ƙaunar shi a zuciyar ta , a hankali takai hannun ta tana sauke farin galashin idon ta , kana ta shafa hoton ɗan nata tana cewa ” I love You my lyf. Allah yaƙara karemun kai yayiwa Rayuwar ka Albarka. Hajiya Sarah ke maganan tana murmusawa kaman wanda Ɗan nata Fahad ke gaban ta. Shigowa Ma’aikaciya na ta tayi na hannun daman ta ,tana ƙarasowa gaban ta , wanda a zuciyar ta cewa take ” Wuuuu Ranan da aka wayi gari Fahad ya mutu ko wani Abu ya faru dashi ƙila Hjy Sarah zaucewa zatayi ko itama ta mutu ta bishi…kullum yana aikin kallon hoton shi , sai kace mara abinyi ? Don Allah yabaka ɗa ɗaya tilo ai bai kamata ki ɗauki son duniya ki ɗaura masa ba ,gashi yaron ma ba ji yakeyi ba , aikin sa kenan lalata ƴaƴan jama’a kuma kin sani amma kike take sani.

Ad

_____

1 2Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button