Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

Afnan cikin sauri ta d’ago kai ta kalli gabanta, ganin Affan tsaye cikin jerin mutanen dake harabar gurin a tsaye yasa ta zazzaro idanu, cikin sauri kuma ta fara ja da baya tana girgiza kai sai tayi cikin gida da gudu, ganin haka yasa Lateefa tabi bayanta itama.
Abinda Afnan tayi ya d’aurewa Affan kai sosai, ita da ya kamata ganinshi ya d’imautata saboda farin ciki amma ta shiga firgici har tana guduwa, tunani ya farayi meyasa tai hakan.
A gefenshi yaji wani dake kusa dashi yana cewa “amarya ta gudu, ko me ta shiga yi cikin gida kuma oho, k’ila dan bataga angonta bane.”
Wani irin matsanancin fad’uwar gaba Affan yaji, kardai Afnan ce amaryar, amma saboda ya kawar da zargi ya matsa kusa da yaron yace “sannu bawan Allah, dan Allah wacce ce amaryar a ciki?”
Yaron yace “sunanta Afnan, itace wadda ta shiga gida da gudu, wadda ta bita a baya k’awarta ce sunanta Lateefa.”
Saida Affan ya tambayi mutane har wajen uku suna tabbatar mishi da bikin Afnan akeyi.
_Wayyo Allah nah, hum tashin hankali wanda ba’a sa masa rana_
Muje zuwa dai
Page 30 to 35
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un!!!!!,” abinda Affan keta maimaitawa kenan, nan da nan jiri ya fara d’ibarshi, sai hawaye shaaaaaaa kamar famfo, k’afafunsa sunyi mishi mugun nauyi ya kasa d’agasu, hakanan ya tsaya a tsaye yana hawaye.
Afnan kuwa da gudu ta shige cikin gida ta fad’a d’akinta, ta zauna bakin gado tana dafe da k’irji, tana fad’in “na shiga uku, wallahi shine, Affan ne.”
Lateefa ce ta shigo d’akin Afnan d’in tana mata masifa “ke kuma ya haka, ya zaki kama ki wani baro cikin fili da gudu salon ai tunanin wani abune.”
Afnan ta mik’e cikin sauri ta kama hannun Lateefa tace “Lateefa na shiga uku, Affan na gani yazo, wallahi yana cikin jama’ar dake wajen taron nan.”
Lateefa tace “haba dai bashi kika gani ba sedai in me kama dashi,” Afnan tace “ni zan fad’a miki kamannin Affan ko ke zaki fad’a min?” hannunta ta kama suka lek’a window wanda zasu iya ganin mutanen dake wajen, sukai sa’a kuwa sun hangoshi, Afnan ta nunawa Lateefa shi da hannu, tace “kin ganshi can da alamu ma kuka yake yi.”
Lateefa na hangoshi itama ta zazzaro idanu tare da dafe k’irji tana fad’in “mun shiga uku, yanzu ya zamuyi kenan, gashi m.c sunanki kawai yake ambata ke ake jira.”
Suna cikin magana wata k’anwar mahaifin Afnan ta shigo d’akin tace “oh kuna nan dama kenan kun shanya bayinku suna jira koh, to ku wuce mu tafi,” ba yanda suka iya haka suka fito.
Lateefa taiwa Afnan rad’a tace “ki duk’ar da kai ne karki sake ku had’a idanu, karma ki nuna kin sanshi.”
Haka ko akayi, kanta na k’asa har suka k’araso fili, wanda a lokacin mijinta yazo har an buk’aci da a basu fili su taka rawa su biyu.
Nan fa aka sa musu wak’ar aurensu suka fara takawa ana zuwa ana zuba musu kud’i.
Afnan ya share hawayenshi, sannan ya laliba aljihunshi inda sauran kud’inshi suke jiki yaje shima ya lik’a musu, cikin rashin sa’a suka had’a idanu sakamakon d’ago kai da Afnan tayi, murmushi Affan yai mata had’e da hawayen da ke zubowa kan idanunshi har a lokacin, tai sauri wajen mayar da kanta k’asa sannan a hankali yace “Allah ya sanya alkhairi amarya, zan koma Allah ya baku zaman lafiya.”
Baro filin yayi zai tafi amma saida ya juyo yana kuka ya k’ara kallonta itama a dai-dai ta d’ago tana kallonshi suka had’a idanu, a haka yaita tafiya da baya da baya suna kallon juna kuma ta kasa tsayar da idanunta daga kanshi har ya b’ace mata.
Sai a lokacin da Afnan taga Affan ya tafi sannan ta saki numfashi ta fara fara’a walwalarta ta dawo har tana yin murmushi kamar ba abinda ya faru.
Affan yana tafiya ne kawai, amma besan inda yake jefa k’afarshi ba.
A yayinda Afnan ke cigaba da shagalin bikinta cikin walwala a lokacin ne shi kuma Affan yake tafe a hanya yana kuka kamar mahaukaci, yana dafe da k’irjinshi dake yi mishi ciwo, tafiya kawai yake besan inda yake jefa k’afarshi ba
Wani dakali ya samu a wata unguwa ya zauna, sannan ya ciro wayarshi ya lalibo hotunanta yana kallo yana kuka, can ya fita daga wajen ya shiga wajen message ya fara tura mata da sak’o kamar haka.
_Afnan Allah ne shaidana akan k’aunar da na nuna miki, na k’aunaceki da zuciya d’aya ashe ke ba hakan a ranki, na k’yamaci so da masu yinta a baya, ashe dalilin da yasa na gujeta kenan saboda wani abu zai faru dani ta dalilin haka, Allah ya sani nai miki yardar da banyi tunanin haka daga gareki ba, nai tunani kina yimin soyayya ne domin Allah ba dan kud’ad’e ba, komai in kika sakani sai nayi bana ganin wuyarsa a kowane irin yanayi kuwa na tsinci kaina, ashe nayi wauta babu ni a cikin ranki, jiya kika gama fad’amin irin k’aunar da kike yimin harda rok’ona akan karna barki, ashe duk zancenda kikemin na k’aryane, Afnan bantab’a kawowa a raina cewar zakiymin haka ba saboda na yarda dake, ashe k’aunar da kikemin da duk kalaman da kike fad’amin ba gaskiya bane, bazan yi miki kowace irin muguwar addu’a ba saboda k’aunar da nake miki ta hanani yin duk abinda zai cutar dake, amma ki sani da tun farko kin fad’amin cewa bakya ra’ayin talaka irina shikenan duk rad’ad’in da zanji bazai kai na yanzu da na sakankance cewa ni kad’ai kikeso ba, kin yimin tabonda bazai tab’a warkewa ba, kuma na tabbatar rashinki shi zai zama sanadin ajalina, ina yi miki fatan alkhairi, kuma duk abinda kikaimin na yafe miki, Allah ya baku zaman lafiya.”_
Yana kuka ya tura mata sak’on, sannan ya tashi a haka yana ganin jiri yana had’a hanya ya cigaba da tafiya.
Yana cikin tafiya aka biyo wani b’arawo a guje ana binshi da gudu yazo ya wuce ta gaban Affan, yana zuwa daidai inda Affan yake ya jefa mishi abinda ya sato ya ruga a guje.
Wad’anda suka biyo b’arawon nan suna zuwa suka cafke Affan suka fara dukanshi ta ko’ina, Affan saboda halinda yake ciki ma ko k’ara ya kasa yi, kuma duk dukan da suke yi mishi baya jin zafin, a waje d’aya kawai yakejin zafi, wato zuciyarshi.
Allah ne ya taimakeshi ‘yan sanda sunzo wajen cikin sauri suka k’waceshi suka sakashi cikin motarsu suka tafi dashi station, ba don haka ba da tuni sun kasheshi.
Saida suka kai Afnan asibiti saboda wahalar da yasha, yai wajen sati a ciki sannan suka dawo dashi station suka gark’ame akan daga nan za’a wuce dashi gidan yari ne tunda ya dad’e yana addabar mutane da sata, kuma yak’i yi musu magana yak’i cewa komai balle su gane wad’anda suke sakashi aikata hakan, hakanan Affan yana ji yana gani ya taka sahun b’arawo.
B’angaren su Inna kuwa hankalin Inna ne ya fara tashi saboda bata samun lambar Affan.
Tana cikin wannan damuwar sai ga Adnan ya shigo d’auke da sallama fuskarshi da fara’a, amma ganin yanayin Inna yasa ya canza, bayan sun gaisane ya tambayeta meke faruwa yaga fuskarta da alamun damuwa.
Inna ta kalleshi tace “Adnan lambar d’an uwanka bata shiga ko na kira bana samunshi, shiyasa na shiga damuwa.”
Adnan yace “laaaa Inna lafiya lau yake fa, inaga abinda yasa baki sameshi ba sedai in matsalar network, amma ni ko d’azu munyi waya dashi, barima in kirashi ku gaisa.”
Adnan ya fad’a mata hakane kawai dan ya kwantar da hankalinta, amma ko shi yanata nema baya samu, ya lalibo lambar Affan ya rangad’a mishi kira cikin sa’a kuma yaji tana ringing, a lokacin kuma wayar tana hannun jami’an tsaro, hakan yasa suna ganin kiran suka d’aga.