Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

“Hello,” abinda Adnan yaji an fad’i kenan da wata murya, bayan sun gaisa Adnan yace “dan Allah ina me wayar?” d’an sandan nan yace “yana hannun jami’an tsaro sakamakon sata da yayi aka kamashi, dak’yar muka k’waceshi a hannun ‘yan unguwa da tuni sun kasheshi, kuma dama ya dad’e yana aikata laifuka irin wad’annan sai yanzu dubunshi ta cika, munyi munyi ya fad’a mana wad’anda suke sashi aikata irin wad’annan laifukan amma yak’i ya fad’a mana, yama k’i cewa komai banda kuka da yake aikin yi, dan haka mun yanke shawarar turashi gidan yari, dan barin irin wad’annan suna cigaba da yawo ba abu bane me kyau,” ok kawai Adnan yace sannan ya katse kiran.
Nan da nan Adnan ya birkice, a hankali ya sauke wayar, idanun Inna suna kanshi tana sauraron su gama waya taji me zaice.
Adnan ya kalleta yai murmushi, sannan yace “da oganshi mukai magana Inna yace wai ya aiki Affan d’in ne amma yanzu zai dawo.”
Sai a lokacin yaga Inna tai murmushi tace “ashe har ya fara aikinma, to Allah ya taimaka,” Adnan yace “ameen Inna, bari inje gida nai wanka na shirya sai in dawo daga k’wallo nake na biyo mu gaisa, idan nadawo zan kirashi sai ku gaisa nasan lokacin ya dawo.”
Inna tace “to sai ka dawo, nagode Allah yai muku albarka, Adnan yace “ameen sannan sukai sallama ya fice da sauri.
Sauri yakeyi kamar zai tashi sama, ya k’osa ya k’arasa gidansu.
Koda ya k’arasa gidansu be tarar da mahaifinsa ba ya fita, kiranshi yai a waya ya shaida masa tafiya ta kamashi amma bazai wuce kwana biyu zuwa uku ba, yai mishi fatan alkhairi sannan sukai sallama, yana ajiye wayar ya hau had’a kayanshi.
Da yake yanada mota yana d’ibar abubuwan da zai buk’ata irinsu takardun haihuwar Affan da yake duk suna wajen Adnan d’in, ya had’a harda I.D CARD d’insa da muhimman abubuwa dai na Affan d’in ya fice.
Cikin sauri yaja motarsa sai hanyar legos, bayan ya kashe wayarsa kar Inna ta kirashi dan besan kuma abinda zai fad’a mata ba.
B’angaren Afnan kuwa basu dad’e da komawa sun zauna ba sai taga message d’in Affan d’in ya shigo, ta karanta, bayan ta gama karantawa sai ta kantare baki irin kaita shafa d’innan sannan ta goge message d’in.
Page 35 to 40
Koda Adnan ya fara tuk’i sai ya d’auko wayarshi ya sake kiran lambar Affan, ana d’agawa yaji mutumin nan ne dai da ya d’aga a farkon wayarsu.
Bayan sun gaisa Adnan yace “yallab’ai wanda kuka kama d’an uwana ne, kuma wallahi asalinshi ma ba d’an nan garin legos d’in bane, kuma sedai in ya taka sawun b’arawo amma Affan bazai tab’a d’aukar kayan wani ba,” nan dai yai mishi cikakken bayani akan Affan d’in, kuma da alama d’an sandan ya d’an gamsu da bayanin, hakanne yasa Adnan ya rok’i alfarma akan su sanar dashi station d’in da suke saboda yana kan hanyar tahowa legos d’in yanzu haka.
Cikin ikon Allah suka bashi adress d’in inda suke, sannan sukai sallama da d’an sandan ya ajiye wayar tare da cigaba da bawa mota wuta kamar zai tashi sama.
Afnan kuwa sun cigaba da gudanar da shagalinsu cikin kwanciyar hankali, sedai duk yanda taso kaucewa tunanin abinda ya faru ta kasa.
Dama an riga da an shirya cewa sai bayan biki da kwana biyu za’a tafi kai amarya saboda ba’a legos d’in zasu zauna ba a Abuja ne.
Zaune suke a cikin d’akin Afnan suna hirar Affan, Lateefa tace “Allah ya taimakemu ya tafi cikin sauk’i, da ya tada fitina a wajen nan da yanzu masifaffun yayyin nan naki sun fara nasu tijarar, amma fa ya bani tausayi, nasha zaki bashi hak’uri ma kafin ya wuce.
Afnan tai dariya, sannan tace “ni nasan Affan yana sona sosai, bazai tab’a yin wani abu ba, shiyasa ma kikaga ban damu ba, ke nifa dama can ba wani sonshi nakeyi ba, kawai naga yana k’aunata sosai ne yasa nake kulashi,” nan dai suka wuni suna zancen daga baya suka hau whatsapp suka fara chat, a yayinda Lateefa ke chat da samarinta, ita kuma Afnan tana bankwana da wasu friend d’inta, ko shakka bataji ba kar tahau taga Affan akai.
Affan kuwa dama Allah ya taimakeshi k’aramar wayar da yake amsa kira da ita ‘yan sanda suka karb’a, basuga wadda yake chat da ita ba saboda yaimata kyakkyawan b’oyo, saida ya tabbatar babu motsi ko alamar giftawar kowa sannan ya fito da wayar yai sauri ya sakata a silent, sannan ya kunna data ya hau whatsapp ko Allah zaisa ya ganta.
Yana hawa ita ya fara dubawa sai yaga tana online.
Wak’a ya fara yi mata na Audio ya tura mata, ga wak’ar a rubuce kamar haka.
_”kinyi nisa da idanuwana kina kusa da zuciyata, jigon rayuwa soyayyace, na tab’a jin hakan sai na mance, da naga mai kuka a so sai ince ya kauce, ni a tunanina mai yin haka ya zauce, yanzun gashinan a kan kaina, ina kuka kan soyayya, munyo sabo dake muna tare, kullum muna chatting ko waya soyayyarmu abar yabo, shak’uwarmu takai shak’uwa in k’ark’are, har mun fara tunanin aure muja zare, rashinki yasa rana ta zama dare, bana iya bacci da idaniya, duniya tai d’aci rashinki ne, bana iya bacci dominki ne, na zama a kad’aici gani a jingine, rayuwata k’unci yayi mata kane kane, yaushe hawayena zai bar zuba kizo ki tare aminiyata, yaya zanyi in misalta soyayya, yaya zanyi in fasalta soyayya, itace ba’a siya da kud’i duk dukiya, itace mai gida na mulki shine zuciya, ta sanya mai k’arfi ya sunkuya ya zubda hawayen idaniya.”_
Da k’yar ya k’arasa rera mata wak’ar ya tura saboda kuka da yaci k’arfinshi ga wani irin zafi da saitin zuciyarshi ke yi mishi had’e da wani matsanancin ciwon kai me tsanani duk a lokaci guda, nan ya fara tari sai aman jini da k’yar ya samu ya kashe datan wayar tashi ya maida ita mab’oyarta sannan ya kwanta, amma bawai dan yai bacci ba, domin ya manta rabon da yai bacci.
Afnan tana cikin chat taga ya turo mata da sak’on voice not, kuma koda ta duba taga ya sauka amma be dad’e da sauka ba.
K’ok’arin bud’eshi tayi sannan ta fara saurara, bayan ta gama saurara taji duk jikinta yayi sanyi, tausayinshi ya fara kamata.
Tunda take bata tab’a jin wani iri akan abinda ya faru ba tsakaninta dashi sai yau da taji voice not d’inshi yana mata wak’a had’e da kuka, sai ta tuno zuwanshi gidansu da yanayin da yabar wajenta, nan take taji duk jikinta yai sanyi.
Itama dai k’arshe sauka tayi ta kashe data, tare da cire layinta sannan ta kwanta, saida ta dad’e a kwance sannan bacci yazo ya d’auketa.
A cikin daren Adnan ya k’araso, kuma da yake d’ansandan yanada kirki da mutunci be tafi ko ina ba yana nan yana jiran zuwan Adnan d’in.
Bayan ya shigo harabar station d’in kai tsaye wajen Affan aka kaishi, ko lokacin da suka isa wajenshi yana dafe da k’irjinshi yanata tari, ga hawaye dake bin idanuwanshi d’aya bayan d’aya, salati Adnan yayi, cikin sauri aka bud’e wajen koda suka shiga sukaga ashe harda aman jini ma yayi.
Adnan ya durk’usa kusa dashi yana kuka yana fad’in “Affan kaine ka dawo haka, me sukai maka haka, shima Affan cikin k’arfin hali ya rik’o rigar Adnan da hannayenshi duka biyun yana kuka yace “Adnan basu bane, itace Adnan, ta barni Adnan, aure tayi zata tafi ta barni, dan Allah Adnan kaje ka fad’a mata ta dawo gareni, wallahi ni kad’ai nasan me nakeji anan, ya nuna saitin zuciyarshi, sannan ya cigaba da cewa idan har ta barni wallahi Adnan mutuwa zanyi, ka taimakeni kaje ka dawomin da Afnan.