HAUSA NOVELNa Baki Rayuwa Ta

Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

 

Kuka sukeyi sosai daga Affan d’in har Adnan.

 

D.P.O yace “kun barmu a duhu fa wacece Afnan kuma.

 

Cikin sauri Adnan ya mik’e ya kalli D.P.O cikin kuka yace “yallab’ai itace yarinyar da yazo legos saboda ita kuka kamashi, ku taimaka min in kaishi asibiti daga baya na fad’a maka komai.”

 

Aman jini Affan ya cigaba dayi, ko kafin su d’aukeshi ya suma

 

Cikin sauri aka d’aukeshi aka fito dashi daga station d’in suka sakashi cikin motar Affan d’in D.P.O shima ya shiga ciki shi yaja motar ma Affan da Adnan suna baya saboda yaga yanayin yanda Adnan d’in ya rud’e kuma akwai tazara tsakanin station d’in zuwa asibitin.

 

Suna k’arasowa aka fito dashi cikin sauri sai emergency, sun dad’e a kanshi saboda zuciyarshi da tai mugun kamuwa da ciwo, sannan suka fito suka wuce office d’in Doctor, Adnan ma suka bishi, acan ne yaita fad’a akan ya za’a bar mara lafiya jikinshi har yai tsanani haka, bayan ya gama bambaminshi ne kuma ya shaida musu cewa mara lafiyan da suka kawo ya kamu da ciwon zuciya, sunyi iyakar k’ok’arinsu suna jiran abinda Allah zaiyi a kanshi, in har suna son a samu nasara cikin sauki akan rashin lafiyar nashi to yanada kyau a samar mishi da abinda yake so, wanda zai taimakesu wajen samun lafiyarshi.

 

Adnan ya fara kuka wi-wi, d’an sandan nan ne ya dafa kafad’arshi tare da fara bashi baki.

 

Fitowa sukayi daga cikin office d’in sannan suka samu waje a bakin k’ofar d’akin da aka dawo da Affan suka zauna.

 

D’ansandan nan ne ya kalli Adnan yace “kayi hak’uri d’an uwa, amma ya akai ciwo farad d’aya ya sameshi irin wannan?”

 

Adnan yana kuka ya bashi labarin duk abinda ya faru daga farko har zuwa lokacin da Affan ya taho nan legos.

 

D’ansandan nan shima besan lokacin da ya fara zubar da hawaye ba na tausayi, yace “tabbas duk wanda yaji wannan labarin na bawan Allahn nan dole ya tausaya, amma itama ba zamu barta ba, dole sai mun hukuntata a matsayinmu na hukuma masu kare hakkin d’an adam.

 

Suna cikin wannan maganar ne sukaji Affan d’in ya fara tari, da gudu suka shiga d’akin, d’an sandan nan ne yaje ya kira Doctor ya shaida mishi cewa mara lafiyan da suka kawo ya tashi.

 

Cikin sauri Doctor ya fito suka taho d’akin, nan ya k’ara duddubashi, sannan ya rubuta wasu magunguna yace aje a kawosu yanzu, kuma ayi k’ok’arin kawo mishi abinda yakeso nan da gaggawa.”

 

D.P.O ne ya karb’a ya fita ya tafi siyowa, wato a duk inda kake baka rasa mutanen Allah, Adnan be tab’a sanin d’ansandan nan ba sai ta sanadin wannan case d’in, amma gashi yanata taimakonsu kamar sun dad’e da sanin juna.

 

Komawa bacci Affan yayi tun kafin a kawo magungunan, sudai Adnan da wannan d’ansandan a ranar sam basu runtsa ba.

 

Washe gari cikin ikon Allah Affan ya tashi, amma har zuwa lokacin yana kuka da kanshi da kuma k’irjinshi dai-dai saitin zuciyarshi.

 

Saida ya karya suka bashi magani sannan ya koma bacci.

 

Adnan ya kalli d’ansandan nan yace “zanje gidansu yarinyar nan, zan fad’a mata halin da d’an uwana ke ciki, kuma zan sanar da ita wallahi duk abinda ya samu d’an’uwana sai munyi shari’a da ita ko waye ubanta a garin nan kuwa.”

 

D.P.O yace “na yarda zakaje, amma ba zaka tafi kai kad’ai ba, kad’an jira akwai jami’an da nake jira suzo ne, sai mu bar biyu su kula dashi, mu kuma da sauran jami’an sai mu tafi, indai gidan Alhaji Bukar ne ai ba b’oyayyen gida bane.”

 

Adnan ya amince da shawarar da D.P.O ya kawo, basu dad’e da gama maganar ba sai ga jami’ai sun shigo, nan dai suka bar guda biyu a wajen Affan su kuma sauran suka tafi dasu, D.P.O ya shiga motar Adnan suna gaba, a yayinda sauran jami’an suka shiga d’ayar motar da suka taho a cikinta tasu ta ma’aikata.

 

A haka suka kama hanya har suka k’arasa k’ofar gidan, abun mamaki motoci suka gani reras ga jama’a sunata shiga cikin motar da alama za’a tafi kai amarya Afnan d’akin mijinta ne.

 

Cikin sauri Adnan da D.P.O suka fito suka nufo inda cincirindon mutanen nan suke sauran ‘yansandan suna biye dasu a baya, sallama sukayi sannan d’ansandan nan ya tambaya wacece Afnan aka nuna mishi ita, nan da nan Adnan ya nannad’e hannunshi zai shak’o shegiya D.P.O ya rik’eshi, nan fa wuri ya kaure da hayaniya, aka fara cacar baki tsakanin mutanen ango da su Adnan.

 

Mahaifin Afnan ne ya fito daga cikin gida shi da tawagarsa, wato manyan yaransa maza, suna tambayar lafiya, nan D.P.O ya gabatar da kansa, sannan ya fad’a musu cewa sunzo ne su tafi da ‘yarshi Afnan domin ta amsa musu wasu tambayoyi, saboda tana k’ok’arin kashe rai ta hanyar yaudara.

 

Daddyn Afnan ya kalli D.P.O yace “yi a hankali k’aramin alhaki, nasan kasan ko ni wanene dan haka ka kiyaye kar ka rasa aikinka, sannan ya koma kan Afnan yace Afnan me kika yi musu?” nan ta fara kuka tana rantse rantse batama sansu ba, nan da nan Adnan ya k’ara yunk’urawa zai kai mata duka aka k’ara rik’eshi, mahaifin Afnan ya kalli Adnan yace “karka sake ka tab’amin ‘ya dan nima bana dukanta, akan haka zan iya shari’a da kowa, nan Adnan ya fara magana yace “banyi mamaki ba dan ka fad’i haka in na tuna cewa wannan dabbar itace ‘yarka, nan Adnan ya fara karanto irin abubuwan da taiwa d’an’uwansa daga farko har k’arshe dan babu abinda ya b’oye mishi sedai se ya aikata yake sanar dashi daga baya, nan da nan wuri ya kaure da salati, daga nan aka fara k’us k’us kowa na tofa albarkacin bakinshi, yawanci suna Allah wadai da abinda tayi ne.

 

Nan fa Afnan ta fara rantse rantse ita bata tab’a sanin me suna Affan ba, da yake Adnan yazo da wayar Affan nan ya binciko hotonshi ya nuna musu yace kun ganshi nan wallahi ta sanshi matsiyaciya k’arya take, Dad d’inta ya karb’a ya duba hoton, sannan ya bawa yayyinta suma suka duba, dukkansu kuma sun yarda kan sharri ake mata dan basu tab’a ganin me irin wannan kamannin yazo k’ofar gidan nan ba, Adnan yace “ai ba’a k’arya kusa da gida bari na binciko muku hotunanta da ta tuttura mishi da kuma chat d’inta na yaudara da message message d’in da taita tura mishi na k’arya, nan yabi duk ya nuna musu, sai a lokacin bakinsu yai shiru, suka hau salati suna jinjina wannan irin hali na Afnan, Dad d’inta ma yafi jin ciwon abun musamman da yaga message d’in abubuwan da taita rok’on Affan, tunaninshi ya tafi akan dame ya ragi yaranshi na jin dad’in duniya da har zata nemi wani abu daga wajen wani, gashi ranar aurenta ta jawa kanta tonon silili gaban mijinta da ‘yan uwanshi da sukazo tafiya da ita, Dad ya kalli D.P.O yace “ku tafi da ita, mijinta ya kalli mahaifin Afnan d’in yace “amma Dad……….” d’aga mishi hannu yayi sannan yace “ku biyoni ciki muyi magana,” ya shige cikin gida ya barsu nan, su Adnan suka tasa k’eyar Afnan suka tafi da ita suka ja motarsu sukai gaba abinsu.

 

A hanya ne Adnan ke cewa “nagode yallab’ai da irin taimakonda kake yimin, bazan tab’a mantawa dakai ba a rayuwa, Allah ya saka maka da alkhairi, ya kamata mu fara biyawa asibiti da ita taga halinda ta jefamin d’an uwa a ciki koh?”

 

D.P.O yace “ai ba komai yiwa kaine, abinda ya kamata nakeyi a matsayina na mutum wanda yake sanye da wannan kakin a jikinshi, zamu wuce da ita asibitin mana dole ita tayi cosin problem nashi, dan haka dole da ita zamuyi amfani wajen dawo da natsuwarshi,” kai tsaye asibiti suka wuce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button