Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

Inna tace “na yafe maka Affan, ba laifinka bane, ” Affan ya juya ya kalli k’annenshi yace su k’araso wajenshi, suna zuwa ya kallesu d’aya bayan d’aya, yace ” ‘yan’uwana kada ku manta dani acikin dukkanin addu’arku, kuma ko bayan babu ni karkuyi kuka kunji Adnan zai maye muku gurbina, ” maganganunda sukeyi ne yasa duk d’akin kuka.
Affan ya sake kai kallonshi kan Adnan yace “abokina sai yanzu na gane dalilin da yasa na tsani soyayya, kuma nake jin haushin masu yinta, ashe dalilin kenan saboda itace sanadin tsayar da rayuwata, dan Allah ko bayan raina ka kulamin da Innata da kuma k’annena, banda d’an’uwan da ya rage wanda zan damk’awa amanarsu da ya wuce kai, basu da kowa sai Allah sai kuma kai, ka kulamin dasu dan Allah.”
Adnan ya k’araso kusa dashi cikin kuka ya rik’e hannunshi tamau yace “haba abokina ya kake mana magana kamar me bankwana ko me barin wasiyya, ka daina tsoratar damu mana, karka manta tare muka tashi mukai komai tare, yanzuma insha Allah tare dakai zamu cigaba da kulawa dasu.
Gabad’aya d’akin ya kaure da kuka, Affan kallonsu yake d’aya bayan d’aya yana jin kukan har cikin ranshi, tausayinsu yakeji, gani yake be kyauta musu ba, tunda shine sanadin kukansu da damuwar da suka tsinci kansu a ciki, yana matuk’ar jin k’aunar ‘yan uwanshi, da Innarshi, yana matuk’ar tausayinsu, yanaso yaga ya cigaba da rayuwa tare dasu, amma jikinshi yana bashi bazai dad’e a raye ba, saboda bazai tab’a daina jin rad’ad’in da yake ji a zuciyarshi ba.
Affan yace “to banda abinku menene na kukan ba sai ku godewa Allah ba jikin nawa yayi kyau har ina cin abinci da yin hira me tsawo haka, duk wanda beyi shiru ba sai nayi mishi tusa me d’an karen wari a baki,” nan da nan dukkansu ya basu dariya, haka yake musu har Inna muddin ya gansu cikin damuwa in yai rarrashin suka k’i yin shiru sai yace zai musu tusa.
Dariya yaita basu har suna tuntsurawa, sunji dad’i sosai ganin ya fara samuwa, shi kuwa Affan ba k’aramin namijin k’ok’ari yayi ba wajen danne abinda yake ji a jikinshi, da yaji ciwon yana gaba gaba ne ya fara lumshe idanu kamar yana jin bacci, Inna ce ta lura da hakan tace “yadai Affan bacci kakeji ne? ”
Affan yace “eh Inna bacci nakeji wallahi, a daidai lokacin likita ya shigo ya dubashi, sannan aka bashi maganin da zaisha a daidai lokacin, kuma a lokacin doctor d’in ya bada umurni akan su bashi waje ya d’an kwanta dan maganin da yasha akwai na bacci kuma anfi so yayi baccin karsu hanashi yi, hakan kuwa akayi dukkansu suka fita suka bashi waje.
Daga wannan baccin ne Affan yai bankwana da duniya, ya tafi bacci me dogon zango, ma’ana daga wannan baccin nashi ne Allah ya d’auki ranshi.
Su kansu basu san ya rasu ba, domin jefi jefi sunayi suna lek’owa d’akin su duba ko ya tashi sai suga stil dai baccin yake, har dare tayi be tashi ba, su kuma basu tasheshi ba saboda cika umurnin likita karsu tasheshi wani abun ya biyo baya.
Doctor ne suka shigo d’akin da norses, doctor yace “har yanzu baccin yake kenan? ” Inna tace “eh wallahi tunda ka shigo d’azu kace a barshi yai bacci yaketa bacci,” doctor yace “ko abinci ma be ci ba kenan, ah to gaskiya a tasheshi lokacin shan maganinsa yayi,” hannu doctor yasa yana k’ok’arin tashinsa shiru baya motsawa, ya d’aga hannunsa hannun ya fad’i yaraf, nan fa doctor yasha jinin jikinsa, haka suma su Inna, nan ya fara gwaje gwajensa amma ina, babu alamun numfashi a jikinsa, doctor ya girgiza kai tare da d’agowa ya kalli su Inna yace “Allah yai mishi cikawa, ashe baccin ba na tashi bane. ”
Innalillahi wa inna ilaihir raji’un!!! itace kalmar da suketa maimaitawa, k’anninshi kanshi sukai harda Adnan, k’anninshi kuka suke suna jijjigashi suna fad’in “yaya ka tashi karka tafi ka barmu kamar yanda abbanmu ya tafi ya barmu, yaya dan Allah ka tashi, ” Adnan shima fad’i yake “abokina ya zakaimin haka, karka manta da yarintarmu, karka manta da alk’awarin da mukaiwa juna na gina gida d’aya komai iri d’aya mu zauna tare da matanmu, duk’ar da kanshi yayi a jikinshi ya sake fashewa da kuka, Inna kuwa a tsaye take, amma jin jiri yana neman kwasheta ta fad’i yasa ta nemi kujera ta zauna, ta cigaba da maimaita salati a bakinta, sannan tace “shikenan shima ya tafi ya barmu, wannan yarinya baki kyauta mana ba, muna zaune lafiya da yaronmu kikayi sanadin da kika rabamu dashi, tsakaninmu dake……..” tunawa tayi da rok’on da yai musu akan ko bayan ba ranshi kada suyi mummunan furuci a kanta, su yafe mata kamar yanda shima ya yafe mata, tunowa da hakan ne yasa Inna ta sake fashewa da kuka tare da binshi da kyawawan addu’o’i.
Muje zuwa
Page 40 to 45
Suna shiga d’akin suka tarar da Affan yana aman jini, hannunshi na dafe da saitin zuciyarshi.
Adnan ya kalli Afnan wadda ta mak’ale bakin k’ofa ta kasa k’arasowa ciki, kanta na k’asa tunda ta d’ago sau d’aya taga halinda Affan yake ciki ta duk’ar dashi, bata sake d’agowa ba, Adnan ya daka mata tsawa yace “wuce ki shige ciki ko in tattakaki, muguwa shed’aniya mara tausayi da imani kawai.”
Suf suf suf ta shige ciki, kuma ya dage sai taje bakin gadon taga halinda ta jefa Affan aciki, yanda ta iya kanta yana duk’e ta k’arasa bakin gadon, ta tsaya a tsaye k’ik’am.
Affan kuwa tarin da yake ya lafa mishi, d’agowa yayi ya k’ura mata idanu, sannan cikin murya ta jinya yace “ga kujera nan ki zauna. ”
Ba musu ta samu waje ta zauna, idon Affan yana kanta, yace “Afnan kiyi hak’uri da d’aukoki da d’an uwana yaje yayi, wallahi banda masaniya akan haka, har abada ina k’aunarki kuma bazan tab’a bari aci zarafinki ba, duk abinda kikaimin wallahi na yafe miki, Afnan *na baki rayuwata* dan Allah ki yarda nima ki bani taki rayuwar dan Allah Afnan. kuma auren da zakiy in har an riga da an d’aura to ina muku fatan alkhairi Allah ya sanya alkhairi, idan kuma ba’a d’aura ba to ina rok’onki da ki dubi girman Allah, ki kalli halinda nake ciki ki hak’ura da auren wancan mutumin kizo ki aureni, Afnan k’aunar da nake miki ta rigada taimin tabo me girma wanda in har ba mallakarki nayi a matsayin matar aureba to tabbas zan rasa rayuwata, baki fad’amin ba dagaske kike sona ba da tun farko na hak’ura, amma yanzu lokaci ya k’ure, domin kuwa k’aunarki itace ke sarrafa tunanina ban isa na gujewa faruwar hakan ba, saboda sonda nake miki ya rigada yai miki har ya zama gyambon da be tab’a warkewa, amma kije kiyi tunani, tashi ki tafi abinki,” duk wad’annan maganganun cikin zubarda hawaye yake yinsu.
Afnan batace komai ba, amma ga dukkan alamu jikinta yai matuk’ar sanyi, haka ta tashi ta doshi hanyar fita, Adnan ya tare k’ofa tare da fad’in babu inda zataje.
Affan ya kalli Adnan yace “Adnan,” Adnan yace “na’am,” Affan yace “kaf duniya babu abinda na tsana irin naga ana cin zarafin Afnan, dan Allah in kana k’aunar farin cikina ka k’yaleta ta tafi, bana k’aunar duk wani abu da za’ayi domin tirsasa mata ko yi mata barazana, ka k’yaleta ta tafi in baka bartaba zan iya shiga wani mawuyacin hali sanadin haka, kaga fa hawaye takeyi saboda takurawarku, wallahi in ka bari ta cigaba da kuka sanadinka bazan tab’a yafe maka ba. ”
Adnan ya matsa Afnan ta wuce ta fita daga d’akin.
Abinda Affan be saniba shine tana fita D. P. O yaiwa jami’an dake waje message akan da ta fito su kamata su wuce da ita station su kulleta zaizo daga baya.