Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

Sun shafe wajen sati biyu a garin, duk kiran da Inna tayi da irin k’aryar da Adnan ke shirga mata.
Yau lahadi, kuma yau aka basu sallama sakamakon sauk’i da Affan ya samu sosai, sun shirya tsaf domin tafiya, D. P. O kawai suke jira yazo suyi sallama.
Suna cikin jiranshi kuwa sai gashi ya shigo, bayan sun gaisa suka yi mishi godiya akan irin taimakon da yai musu da kuma irin dukkanin kulawar da ya basu, har bakin mota ya rakasu inda sukai sallama Adnan yaja suka d’auki hanyar zaria.
Haka suka taho hanya suna hira jefi jefi, duk da hirarma Adnan ne yaketa janshi da ita, saboda sam baya k’aunar yaga Affan d’in yai shiru yana tunani yanzu sai kamanninshi su canza, kuma an gargad’esu da hanashi shiga damuwa da tunanin.
Tun suna hanya Adnan yaiwa Inna albishir cewa suna hanya shida Affan, har tana fad’in ho d’an nema ashe can ka tafi kaketa yimin hanya hanya a waya, hakan yasa ita da k’annen Affan wato su Yasmeen aka shiga shiryawa babban yaya da Adnan girki me rai da lafiya, sedai kash
Suna shigowa cikin unguwarsu ciwo ya dawo sabo, Adnan duk ya rud’e, sam baya k’aunar Inna taga Affan a irin wannan yanayin, yana k’ok’arin juya motar suje asibiti ne kawai ya gansu sun fito daga gida cikin sauri kowannensu fuskarshi d’auke da murmushi suna jiran fitowarsu domin suga yayansu.
Sedai ganin Adnan ya fito shi kad’ai ga tari matsananci suna ji a cikin motar yasa sukayi saurin k’arasowa inda motar take.
Halinda suka tarar da Affan a ciki shi ya tsayar da dukkanin fara’ar fuskarsu, a yayinda cikin k’ank’anin lokaci kuka ya maye gurbin dukkanin walwalarsu.
Inna ce cikin kuka take fad’in “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un me zan gani haka!!! Affan menene ya sameka haka, juyawa tayi b’angaren da Adnan yake wanda yaketa kuka yama kasa cewa komai, saboda a yanzu bayan ciwon Affan d’in dake damunshi harda tausayin mahaifiyarshi da kuma k’annenshi.
Inna tace “Adnan me ya sami Affan d’ina ka sanar dani dan Allah, aman jini fa yake, yanzu halinda yake ciki kenan dama shiyasa kaketa b’oyemin Adnan, ” duk ta rikice ta cukuikuye Affan d’in tana kuka, a yayinda suma k’annenshi suke kusa da Innar tasu suna kallon halinda d’an uwan nasu yake ciki suna kuka.
Adnan ne cikin k’arfin hali da wata irin muryar kuka yace “Inna ku shiga mota mu kaishi asibiti, daga baya na sanar dake komai. ”
Cikin sauri Adnan da Inna suka maidashi baya Inna ta zauna kusa dashi, kanshi yana Kafad’arta, ‘yan uwanshi ma dukkansu suka shiga, Adnan yaja motar cikin sauri suka tafi asibitin kud’i saboda Adnan bayaso a b’ata lokaci wajen dubashi, yana tuk’i yana kuka tare da waigowa yana kallon halinda Affan d’in ke ciki, gudu yake sosai amma duk rashin son gudu da inna take a mota a yau gani take kamar baya wani gudu, ji take kamar ta karb’i motar taja.
Allah ne kawai ya kaisu bakin asibitin lafiya, cikin sauri ba b’ata lokaci aka shiga dashi emergency likitoci suka duk’ufa a kanshi.
A wannan lokacin ne Adnan ya sanar da Inna komai, kuka Inna take kamar zata shid’e, tana fad’in “meyasa baka fad’amin ba Adnan, meyasa Affan zai mana haka, akan mace zai salwantar mana da rayuwarshi, bayan yana sane da cewa tafi komai muhimmanci a garemu, ” Adnan ya kasa cewa komai domin kuka yake shima.
Likitoci suna kanshi har wajen awa shida da rabi sannan suka fito, d’aya daga cikinsu ya nufo su Inna, suma su Inna kanshi sukayo cikin sauri suna tambayarshi lafiyar Affan d’in.
Doctor yace “to munyi iya yinmu sauran sai mu barwa Allah, amma kun rigada kun bari jikinshi yai tsananin da har zuciyarshi tayi mugun ciwo, zamu cigaba da dubashi mu ga abinda Allah zaiyi, wasu kayan aiki zan d’auko mu cigaba da dubashi, ” yana gama fad’in haka ya wuce, a yayin da jin haka ya k’ara tayar da hankalin su Inna sosai.
A tak’aice saida yai kwana biyu rak yana kwance besan ma inda kanshi yake ba, a kwana na uku ne Allah yasa ya farfad’o, yana farfadowa ikon Allah kuma sai jikin yai sauk’i, su Inna sukaji dad’i sosai, abinci yakeci, yana ci yana kallon Inna da taketa kuka har yanzu.
Affan ya kalli Inna yace “haba Inna menene kike kuka kuma bayan gashi na warke? ”
Inna tace “meyasa ka b’oyemin abinda ke faruwa Affan, dama duk halinda ka shiga a baya saboda watace wadda bata damu da ka rayu ko ka mutu ba, wallahi abinda tai maka da kuma halinda ta jefaka a ciki insha Allah sai……..” Affan yai wuf ya rufe bakin Inna yana kuka yace “Inna dan girman Allah kar kiywa Afnan baki, ki yafe mata, karki manta yafiya sifface daga cikin siffofin ‘yan aljanna, duk da abinda taimin har yanzu ina k’aunarta Inna, kuma bazanji dad’i ba idan naji kinyi mummunan kalami a kanta, ki yafe mata, nima ina rok’on afuwarki akan irin k’aryar da naita yi miki Inna. ”
Inna tace “na yafe maka Affan, ba laifinka bane, ” Affan ya juya ya kalli k’annenshi yace su k’araso wajenshi, suna zuwa ya kallesu d’aya bayan d’aya, yace ” ‘yan’uwana kada ku manta dani acikin dukkanin addu’arku, kuma ko bayan babu ni karkuyi kuka kunji Adnan zai maye muku gurbina, ” maganganunda sukeyi ne yasa duk d’akin kuka.
Affan ya sake kai kallonshi kan Adnan yace “abokina sai yanzu na gane dalilin da yasa na tsani soyayya, kuma nake jin haushin masu yinta, ashe dalilin kenan saboda itace sanadin tsayar da rayuwata, dan Allah ko bayan raina ka kulamin da Innata da kuma k’annena, banda d’an’uwan da ya rage wanda zan damk’awa amanarsu da ya wuce kai, basu da kowa sai Allah sai kuma kai, ka kulamin dasu dan Allah.”
Adnan ya k’araso kusa dashi cikin kuka ya rik’e hannunshi tamau yace “haba abokina ya kake mana magana kamar me bankwana ko me barin wasiyya, ka daina tsoratar damu mana, karka manta tare muka tashi mukai komai tare, yanzuma insha Allah tare dakai zamu cigaba da kulawa dasu.
Gabad’aya d’akin ya kaure da kuka, Affan kallonsu yake d’aya bayan d’aya yana jin kukan har cikin ranshi, tausayinsu yakeji, gani yake be kyauta musu ba, tunda shine sanadin kukansu da damuwar da suka tsinci kansu a ciki, yana matuk’ar jin k’aunar ‘yan uwanshi, da Innarshi, yana matuk’ar tausayinsu, yanaso yaga ya cigaba da rayuwa tare dasu, amma jikinshi yana bashi bazai dad’e a raye ba, saboda bazai tab’a daina jin rad’ad’in da yake ji a zuciyarshi ba.
Affan yace “to banda abinku menene na kukan ba sai ku godewa Allah ba jikin nawa yayi kyau har ina cin abinci da yin hira me tsawo haka, duk wanda beyi shiru ba sai nayi mishi tusa me d’an karen wari a baki,” nan da nan dukkansu ya basu dariya, haka yake musu har Inna muddin ya gansu cikin damuwa in yai rarrashin suka k’i yin shiru sai yace zai musu tusa.
Dariya yaita basu har suna tuntsurawa, sunji dad’i sosai ganin ya fara samuwa, shi kuwa Affan ba k’aramin namijin k’ok’ari yayi ba wajen danne abinda yake ji a jikinshi, da yaji ciwon yana gaba gaba ne ya fara lumshe idanu kamar yana jin bacci, Inna ce ta lura da hakan tace “yadai Affan bacci kakeji ne? ”
Affan yace “eh Inna bacci nakeji wallahi, a daidai lokacin likita ya shigo ya dubashi, sannan aka bashi maganin da zaisha a daidai lokacin, kuma a lokacin doctor d’in ya bada umurni akan su bashi waje ya d’an kwanta dan maganin da yasha akwai na bacci kuma anfi so yayi baccin karsu hanashi yi, hakan kuwa akayi dukkansu suka fita suka bashi waje.