Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

Daga wannan baccin ne Affan yai bankwana da duniya, ya tafi bacci me dogon zango, ma’ana daga wannan baccin nashi ne Allah ya d’auki ranshi.
Su kansu basu san ya rasu ba, domin jefi jefi sunayi suna lek’owa d’akin su duba ko ya tashi sai suga stil dai baccin yake, har dare tayi be tashi ba, su kuma basu tasheshi ba saboda cika umurnin likita karsu tasheshi wani abun ya biyo baya.
Doctor ne suka shigo d’akin da norses, doctor yace “har yanzu baccin yake kenan? ” Inna tace “eh wallahi tunda ka shigo d’azu kace a barshi yai bacci yaketa bacci,” doctor yace “ko abinci ma be ci ba kenan, ah to gaskiya a tasheshi lokacin shan maganinsa yayi,” hannu doctor yasa yana k’ok’arin tashinsa shiru baya motsawa, ya d’aga hannunsa hannun ya fad’i yaraf, nan fa doctor yasha jinin jikinsa, haka suma su Inna, nan ya fara gwaje gwajensa amma ina, babu alamun numfashi a jikinsa, doctor ya girgiza kai tare da d’agowa ya kalli su Inna yace “Allah yai mishi cikawa, ashe baccin ba na tashi bane. ”
Innalillahi wa inna ilaihir raji’un!!! itace kalmar da suketa maimaitawa, k’anninshi kanshi sukai harda Adnan, k’anninshi kuka suke suna jijjigashi suna fad’in “yaya ka tashi karka tafi ka barmu kamar yanda abbanmu ya tafi ya barmu, yaya dan Allah ka tashi, ” Adnan shima fad’i yake “abokina ya zakaimin haka, karka manta da yarintarmu, karka manta da alk’awarin da mukaiwa juna na gina gida d’aya komai iri d’aya mu zauna tare da matanmu, duk’ar da kanshi yayi a jikinshi ya sake fashewa da kuka, Inna kuwa a tsaye take, amma jin jiri yana neman kwasheta ta fad’i yasa ta nemi kujera ta zauna, ta cigaba da maimaita salati a bakinta, sannan tace “shikenan shima ya tafi ya barmu, wannan yarinya baki kyauta mana ba, muna zaune lafiya da yaronmu kikayi sanadin da kika rabamu dashi, tsakaninmu dake……..” tunawa tayi da rok’on da yai musu akan ko bayan ba ranshi kada suyi mummunan furuci a kanta, su yafe mata kamar yanda shima ya yafe mata, tunowa da hakan ne yasa Inna ta sake fashewa da kuka tare da binshi da kyawawan addu’o’i.
Muje zuwa
Page 45 to 50
Haka suka tarkata suka koma gida da gawar Affan, anyi mishi wanka aka buk’aci Inna da ‘yan’uwansa suzo su yi mishi addu’o’i, haka sukazo kan gawar harda Adnan suka duk’a suna mishi addu’a suna kuka gwanin ban tausayi.
Saida suka sa mutane da dama kuka a wajen, tausayinsu ya cika zuciyar kowanne, tausaya musu suke akan mahaifinsu ya rasu, gashi wanda ya zame musu madadin uba shima yau babu shi ya tafi ya barsu, gaskiya rashi akwai ciwo musamman wanda ka shak’u dashi, wanda kuma besan komai ba sai kyautatawa.
Da akazo fita dashi daga gidane fa zance yasha bamban, domin Adnan da k’annenshi rik’e makarar da aka d’orashi a cikinta sukayi gam, k’annenshi fad’i suke ” ina zaku kaishi, dan Allah karku tafi dashi,” Adnan kuwa kallon wad’anda suke rik’e da makarar yake yana fad’in “wai da gaske yanzu Affan ya rasu ya tafi ya barmu? ku d’an k’ara jinkirtawa dan Allah ina ganin doguwar suma yayi.”
Haka yaita surutu kowa saida ya tausaya domin ansan irin muguwar shak’uwar dake tsakanin Adnan da Affan.
Mahaifin Adnan ne yazo ya dafashi, Adnan yai sauri ya kallin babanshi yace “baba kace su tsaya ba mutuwa yayi ba zai farfad’o,” Baba yace “Adnan ka sawa zuciyarka hak’uri dan Allah, wanda ya mutu bazai tab’a dawowa ba,” yaja hannunshi suka fita suka zauna a k’ofar gida inda dubbannin jama’a ke jiran a fito dashi su sallaci gawarshi.
Anyi mishi sallah, sannan akai yunk’urin kaishi makwancinsa, Allah sarki inna ita da k’annensa su Yasmeen sunata lek’e har aka tafi dashi ba yanda suka iya, ji sukeyi kamar su bishi.
Adnan kuwa k’arshe a wani d’aki aka kulleshi, dan yanata surutai yana zabura shi sedai a barshi yaje ya kasheta kamar yanda ta kashe mishi d’an uwa Shiyasa sam be samu an kaishi dashi ba yana kulle, Inna kuwa jininta ne ya hau, sedai saboda masu zuwa gaisuwa yasa ba’a kaita asibiti ba, likita aka kira har gida ya dubata, saida Adnan yai sati a kulle komai sedai a kawo mishi, sannan daga baya aka fito dashi aka yi mishi nasihohi tare da nunar mishi da cewa duk wad’annan abubuwan bazasu tab’a amfanar Affan da komai ba, babu abinda Affan yafi buk’ata a yanzu daya wuce addu’a, itace soyayyar da ta rage yanzu a tsakaninsu dashi, sai a lokacin ya dawo hayyacinshi.
Su Inna duk sun rame saboda jimami, kullum cikin kuka, sedai duk wanda yazo gaisuwa ta ko’ina yabon kyawawan halayenshi akeyi, tabbas Affan ya samu shaidar k’warai,
_Ya Allah kasa muyi kyakkyawan k’arshe, ya Allah ka bamu ikon aikata kyawawan aiyukan da zakai alfahari damu_
Bayan sati d’aya wato ranar da aka fara zaman makoki da Adnan, ranar da aka yi mishi nasiha kenan, suna zaune anata yabon halayen Affan tare da yi mishi addu’a, Adnan dai yana zaune shiru ya zuba uban tagumi yana tunani hawaye na biyo fuskarshi sai ga wayarshi tai k’ara, ita ta dawo dashi daga tunanin da ya lula, yana dubawa yaga D.P.O ne, tashi yayi yabar wajen ya koma d’an nesa kad’an da inda mutane suke zaune zaman makoki, bayan sun gaisa D.P.O yake tambayarshi ya jikin Affan, Adnan cikin kuka yace “ai Affan jiki ya warke, Allah yai mishi rasuwa, yau sati d’aya kenan da rasuwarshi.”
D.p.o ya saki salati, sannan yace “Affan ya rasu!!!, Allahu akbar, Allah sarki Affan, to Allah ya jik’anshi, insha Allah nima inanan tafe,” sukai sallama Adnan ya koma wajen zamanshi, wayar Affan ya ciro a aljihunshi, ya shiga whatsapp ba tare da ya kunna data ba, chat d’insu da Afnan yaketa dubawa, yana mamakin irin tarin yaudararrun kalaman da yaga Afnan na turowa Affan, a zuciyarshi yace lallai ko wanene koda kuwa nine zan iya fad’awa tarkon wannan shed’aniyar yarinyar, saboda irin yaudararrun kalaman da take amfani dasu dole taja ra’ayin kowa fad’awa tarkonta ba tare da ya ganota ba.
Kasa hak’uri yayi ya d’auko wayarshi ya rubuta message kamar haka:
_”Burinki ya cika, kin raba Affan da duniyar kin huta, amma ki sani ki jira naki sakamakon, yanda kikai sanadin mutuwarshi insha Allah naki k’arshen ba zaiyi kyau ba.”_
Yana gama rubutawa ya kwafi lambarta a wayar Affan d’in ya tura mata.
Washe gari kuwa kamar yanda D.P.O ya fad’i sai gashi ya diro garin zaria, ya kira Adnan, Adnan yai mishi kwatance, yana k’arasowa bayan yayi gaisuwa, ya kaishi har d’akin Inna yai musu gaisuwa sai ya saukeshi a d’akin marigayi Affan.
Sedai yayi danasanin shiga, domin suna shiga manya manyan hotunan Afnan suka gani a d’akin, ga dukkan alamu na cikin wayane da take turo mishi yaje aka wanke mishi.
Adnan ya sake fashewa da kuka matsananci, yace “ka gani ko, ya sota tsakani da Allah kuma da zuciya d’aya, ita kuma ta saka mishi da. d’aukar ranshi.”
D.P.O yace “Adnan kar kayi sab’o, babu wanda yake da ikon d’aukar ran wani sai Allah, sedai mutum ya zama sanadi, ta zama sanadi dai na mutuwarshi bawai ta d’auki ranshi ba.”
Adnan yace “har yanzu tana hannunku ne ko kun bada belinta?”
D.P.O yace “mahaifinta ya turo a bada belinta muka k’i bayarwa, yazo da kanshi nan ma bamu saurareshi ba, munce su jira aje kotu, ashe yasan kwamishina, shine ya buga mishi waya ya fad’a mishi k’arya da gaskiya, kwamishina yaita bashi hak’uri kuma harda tambayarshi ya yakeso ayi dani, nidai a ranar ina zaune a office kawai naji kiran gaggawa, ina zuwa aka bani takardar sallama daga aiki, a ranar ne itama aka saketa ta koma gida, tunda dama an d’aura mata aure nasan yanzu tuni ta tare a gidan mijinta.