Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

Adnan yace “yaushe hakan ta faru?”
D.P.O yace “bayan kwana biyu da tahowarku.”
Adnan yace “ranar da Affan ya rasu kenan, kayi hak’uri dan girman Allah mun zama silar rasa aikinka.”
D.P.O yace “no karka damu wallahi, ko basu koreni ba ni zan ajiye da kaina, domin na tsani goyon bayan rashin gaskiya.”
Adnan yace “wallahi D.P.O bazan k’yale yarinyar nan ba, duk inda take saina nemota na d’auki fansar ran d’an uwana da ta zama silar salwantarsa.
D.P.O ya girgiza kai, sannan yace “Adnan, mahaifin Afnan shahararren me kud’i ne kuma fitacce, duk wanda yace zai ja dashi zaisha k’asane kawai, babban abinda ya kamata ka maida hankali akai shine kula da amanar da Affan ya damk’a a hannunka hakan shi zaifi, ita kuma ka barta da halinta kawai.”
Saida D.P.O yai kwana biyu a garin sannan ya tafi, inda ya tabbatarwa da Adnan cewa insha Allah zai nemi aiki anan zaria ya dawo da iyalensa su cigaba da zumunci.
B’angaren Afnan kuwa washe garin ranar da ta koma gida aka kaita gidan mijinta bayan Daddynta ya nuna mata matuk’ar b’acin ranshi akan abinda tayi, a cewarshi me ta rasa da zata nema a wajen wani talaka k’ask’antacce har ana tozartata gaban jama’a ta dalilinshi.
Tunda take bata tab’a ganin b’acin ran Dad d’inta ba irin na wannan lokacin, hak’uri ta baiwa Dad d’in nata, duk da taji haushin fad’an da yake mata, dan ta tsani fad’a a rayuwarta, bayan ya gama yi mata fad’an ne sannan sukai sallama da ita aka tafi kaita d’akin mijinta.
Da yake tunda ta dawo ta cire tsohon layinta, ta saka wanda mijin nata ya siya mata, shiyasa bataga sak’on da Adnan ya tura mata ba.
Mijin da Afnan ta aura sunanshi Ibrahim, ana yi mishi inkiya da Inyas.
Inyas d’an gwamnan garin legos d’in ne, basu wani dad’e tare ba, ganinshi d’an masu dashi kuma gashi kyakkyawa yasa Afnan tai alaragaf, iyayenta kuwa suka mara mata baya domin abinda takeso shi sukeso, Afnan taita murna ta sami irin mijin da takeso, nan da nan ba b’ata lokaci aka saka rana aka sha biki.
Abinda yasa mijinta inyas be shiga maganar abinda ya faru ba Dad d’in Afnan ya hanashi yin komai yace yabar mishi komai a hannunshi.
Abu na farko da ya fara mata barazana shine tun bayan dawowarta har aka kaita d’akin mijinta babu abinda idanunta suke yawan kawo mata irin hoton fuskar Affan cikin mawuyacin halin da ta ganshi a ciki lokacinda taje asibitin, sai kuma maganganun da ya fad’a mata a wannan ranar sune suketa dawo mata
_Afnan *na baki rayuwata,* dan Allah ki yarda kema ki bani taki rayuwar, zuwa yanzu k’aunar da nake miki ta riga da tai miki ta zama gyambo, wallahi zan iya rasa rayuwata muddin kika k’auracewa cikinta._
Kwance suke ita da angonta suna bacci cikin dare sai ji kawai yayi tana surutai, can kuma sai ta tashi firgigit tare da k’wala k’ara, cikin sauri shima ya tashi yana tambayarta lafiya, tace mishi bakomai wani mummunan mafarki tayi, yace tayi addu’a ta koma ta kwanta, hakan kuwa akayi tai addu’a suka koma a tare sukai kwanciyarsu.
Washe gari sun karya sunci ado sai Inyas ya kalleta yace zai fita, ta kalleshi tace “to Affan sai ka dawo.”
Inyas ya kalleta yace “yau nine kuma na koma Affan, anya lafiyarki lau kuwa?”
Afnan tace “kayi hak’uri mantuwa ne,” nan sukai sallama ya fita, tunda ya fita ba wani aiki da take sai tunanin Affan.
Haka dai rayuwarta ta cigaba da kasancewa ko menene takeyi tunanin Affan takeyi, musamman idan tana ita kad’ai, sannan maganganunshi suita dawowa cikin kunnenta, cikin k’ank’anin lokaci ta rame, sam batada natsuwa, ga wani irin mugun tausayin Affan da takeji yanzu, da matsananciyar k’aunarshi wanda ada bata san da ita ba, ga kewarshi da takeji musamman idan ta tuno da yanda rayuwarsu ta kasance da yanda ya damu da ita.
Sunan tana gidan mai naira amma sam babu kwanciyar hankalin cin dukiyar, watansu befi uku tak ba da aure amma Inyas yakai k’ararta wajen sau uku akan tana kiranshi da sunan tsohon saurayinta, sannan tana yawan tunaninshi harda kuka, sam batada lokacinshi yanzu sai na tunani.
Bata b’oyewa iyayen ba ta fad’a musu itafa yanzu bata k’aunarshi ita Affan takeso, nan fa iyayen sukai mata caaaaa, daga baya suka rarrasheta.
Anyi haka da sati d’aya ta saka Inyas a gaba ya saketa ita bata k’aunarshi ita Affan takeso, duk bai kulata sedai kullum cikin rigima suke, bayan kwana biyu da inyas yazo yaga tana kallon hotunan Affan a wayarta, a ranar ne kishi ya turnuk’eshi ya saketa tai murna kamar me, fad’i take “Allah na gode maka, zanje ga masoyina na gaskiya wanda naso naiwa kaina asara,” Inyas yace “oho dai kin zama bazawara ba lallai bane wanda kika kashe auren saboda shi ya yarda ya aureki, ni kuwa in hudu naso duka yanmata ko ‘ya’yan waye zan aura.”
Bayan sati d’aya da mutuwar aurenta ta d’akko wayarta ta kira lambar Affan a kashe, yanke shawarar zuwa garinsu tayi dan taje ta bashi hak’uri dan a yanzu a duniya kaf babu wanda take jin matuk’ar k’aunarshi irin Affan, kuma bata jin zata iya rayuwa da wani d’a namiji a yanzu idan ba Affan ba, duba adreshin da Affan ya tab’a bata tayi ta shirya ta tafi zaria ba tare da ansan can d’in ta tafi ba.
Abinka da masu naira jirgi ta biyo hakan yasa ba b’ata lokaci ta iso zaria, bata wani sha wahala ba wajen gane unguwar saboda tambaya da taita yi, har Allah ya kawota har k’ofar gidan.
_Tabd’ijam, Afnan kin mutu, waya aikeki, masu karatu kuji fa irin katob’arar da Afnan ta tafko.????_
Muje zuwa
Page 50 to 55
Afnan na zuwa k’ofar gidan taji gabanta ya fara fad’uwa, amma haka nan ta dake tayi k’arfin hali ta shige cikin gidan.
“Assalamu alaikum,” Afnan ta kwad’a sallama tare da shigowa cikin tsakar gidan ta tsaya k’ik’am.
Inna ce ta fito daga cikin d’aki tare da amsawa “wa alaikumussalam sannu da zuwa.”
Afnan da fara’arta tace “yauwa Mama, dan Allah nan ne gidansu Affan?”
Inna tace “eh nan ne, bismillah shigo daga ciki, bari in d’auko mana tabarma mu zauna a tsakar gida, d’akin akwai zafi gashi ba wuta.”
Inna ta shiga d’aki ta d’auko tabarma ta shimfid’a musu a gefen k’ofar d’aki tacewa Afnan ta zauna, komawa ciki Inna tayi ta kawo mata abinci da ruwa me sanyi ta ajiye a gabanta, sannan tace “baiwar Allah bismillah.”
Afnan ta d’auki ruwa kawak tasha kad’an, sannan ta kalli Inna tace “Mama ina yini, mun sameku lafiya?”
Inna tace “lafiya lau ‘yarnan, sedai ban ganeki ba.”
Afnan tai shiru tana sunkuyar da kai, can sai ta d’ago ta kalli Inna tace “eh Mama baki sanni ba, dama wajen Affan nazo kuma naga kamar bayanan.”
Inna tai jim tare da k’urawa yarinyar idanu, gani take kamar ta santa, amma ta kasa gano inda ta santa, Inna ta numfasa, sannan tace “hala ba’a garin nan kike ba, kuma kun dad’e rabonki da had’uwa da Affan koh?”
Afnan ita burinta kawai taga Affan, tafiso idan ta ganshi sai shi ya gabatar da ita ga Maman tashi, amma taga sai tsareta da tambayoyi kawai takeyi, ta kalli Inna tace “makaranta d’aya mukayi, to tunda muka gama karatu bamu sake had’uwa ba sedai muyi magana a whatsapp, to kwana biyu bana ganinshi a whatsapp ne shiyasa nace bari nazo in duba ko lafiya.”
Kafin Inna tace komai sai sukaji sallamar Adnan ya shigo cikin gidan d’auke da kaji a cikin leda da kuma kayan miya da sauran kayan cefane.