HAUSA NOVELNa Baki Rayuwa Ta

Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

 

Adnan ya shigo cikin gidan cikin fara’a yana cewa “Inna na dawo, ah kicema bak’uwa kika…………” kasa k’arasa maganarsa yayi sakamakon juyowar da sukayi dukkansu da Inna da Afnan yaga bak’uwar dake zaune a gaban Innarsu.

 

Lokaci d’aya Adnan da Afnan suka zazzaro idanu sakamakon ganin juna, mik’ewa tayi cikin sauri, a yayin da shi kuma Adnan ya zubar da kayan dake hannunshi saboda tsabar mamakin wadda yake gani a gabanshi.

 

Afnan kuwa gabanta ne keta fad’uwa zuciyarta na tabbatar mata da yau kashinta ya bushe, wai ina Affan ne to, duk a zuciyarta take wannan zancen.

 

Adnan ya taho a fusace yana magana, “ke dan ubanki me ya kawoki gidan nan, kin kashe mata d’a shine kikazo itama ki kasheta, to wallahi yau gawarki zata fita daga gidan nan.”

 

Yana zuwa ya shak’eta, Inna duk ta rud’e tayi-tayi ta b’amb’are hannun Adnan daga wuyan Afnan amma ta kasa, gashi har Afnan idanunta ya fara k’walalowa alamun shan wahala sosai, saboda rik’on da yai mata ba na wasa bane, hakan yasa Inna ta fita waje da sauri domin neman agajin gaggawa karya kashe musu ‘ya.

 

Cikin sa’a kuwa Inna ta samo wasu samari su biyar, duk da haka an kasa b’anb’areshi saida aka k’aro wasu matasan aka taru da k’arfin tsiya aka janyeshi.

 

Inna ta rik’e Afnan wadda take ta maida numfashi dak’yar, zaunar da ita tayi a gefe, Adnan ya sake zaburowa “au zama kikai dan ubanki duk da Allah ya k’waceki ko,” rik’eshi suka k’arayi gam, Adnan fad’i yake wallahi Allah sai ta bar gidan nan tunda ba gidan ubanta bane, in kuwa har tak’i tafiya wallahi sai na kasheta, ta fita tabar gidan kawai.”

 

Inna ta kalleshi tace “haba Adnan ka dawo cikin hankalinka mana, ka daina fad’in irin wannan maganganun, karka jawo mana fitina mana,” Adnan yana kuka yace “Inna kinsan wacece a gabanki kuwa? to in baki sani ba ki sani itace ta kashe miki Affan, ita tai sanadin mutuwarshi.”

 

Inna cikin sauri ta zaro idanu tare da maida kallonta kan Afnan, sai a yanzu ta gane inda ta santa, hotunanta dake manne a d’akin Affan.

 

Afnan itama zaro idanu tayi jin ana fad’in Affan ya mutu, da k’arfi kuma razane ta sake maimaitawa, ” na shiga uku Affan d’ina ya mutu!!!” durk’ushewa tayi a k’asa ta saki wani irin kuka, kuka take kamar ranta zai fita, Adnan yace “a gidan uwar wa ya zama naki, ai murna zakiyi tunda burinki ya cika kin kasheshi”.

 

Wannan kukan shi ya k’ara harzuk’a Adnan ya sake zaburowa yana fad’in kukan ubanme kike munafuka mayaudariya, aka sake rirrik’eshi, ya kalli wad’anda suka rirrik’eshi yace wallahi idan bata bar gidan nan ba sai na kasheta, cikin wani irin k’arfin hali ya ture duk mutanen dake rik’e dashi ya rarimo tab’arya ta daka ya wurgo kanta, be sameta ba, sai wani dutse ne ya sameta a gefen goshi, Inna ta kama hannunta cikin sauri tai hanyar waje da ita tana fad’in “kiy sauri kibar unguwar nan.”

 

Adnan kuwa biyosu yayi yana fad’in makira kawai, bakisan kina k’aunarshi ba wato saida kika kasheshi, to kema insha Allahu sonshi shi zaiyi ajalinki, bakiga komai ba wallahi sai sakamakon Affan yai sanadin barinki duniya.”

 

Da k’yar aka fitar da Afnan daga unguwar saboda wasu abokanan Adnan suma sun fara taruwa zasu tayashi kasheta, wani mak’wabcin su Inna ne aka samu ya d’auketa ya kaita har bakin ti-ti sannan yai mata sallama tare da kashedin in tana son ranta karta sake zuwa.

 

A bakin titin ta sami wani d’an dandamali ta zauna taita rusa kuka, surutu ta fara yi kamar tab’ab’b’iya, “yanzu Affan ya rasu, kuma ta dalilina, ashe duk abubuwan da yake fad’amin har zuciyarshi ne, meyasa zakaimin haka Affan, meyasa zaka tafi ka barni a lokacin d nai mugun kamuwa da k’aunarka, ya zanyi na nemi gafararka, wayyo Allah nayi rashi.”

 

Ta dad’e anan bakin titin duk wanda yazo wucewa ta gefenta sai ya kalleta, wasu suyi mata magana, batama san sunayi ba tunda bata a hayyacinta, wasu kuma su kalleta kawai su wuce.

 

Wayarta ce taketa k’ara tun lokacin da take cikin gidansu Affan taji wayar na k’ara amma firgici ya hanata d’agawa

 

Cikin k’arfin hali ta ciro wayarta daga jaka, ta d’aga ba tare da ta duba ba, muryar Dad d’inta taji yana fad’in “Afnan kina inane?”

 

Afnan ta sake sakin wani irin kuka me matuk’ar k’ara tace “Daddy na kashe shi Daddy, na rasa masoyi na k’warai, na rasa masoyi na hak’ik’a Daddy, ashe da gaske yake fad’i da yake cewa in ya rasani mutuwa zaiyi, Dad ina sonshi, wallahi ina sonshi, bazan tab’a samun masoyi kamarshi ba Dad, nima mutuwa zanyi in har babu shi bazan iya rayuwa da wani ba idan ba shi ba.”

 

Dad d’in Afnan ya saki salati, yace “yanzu kina inane?”

 

Afnan tace “ina zaria nazo gidansu Affan in bashi hak’uri na tarar wai ya mutu,” ta sake fashewa da kuka.

 

Dad yace “to kije ki samu hotel da yake kusa ki zauna a ciki, zamu taho mu d’aukeki kar kije ko ina kinji ki jiramu kiyi hak’uri kinji idan munzo zamu tattauna maganar.”

 

Afnan tace “to,” sukayi sallama da ita ya katse kiran.

 

Dad ya kalli mahaifiyar Afnan yace “kinji wai tana zaria, ga dukkan alamu Afnan ba daidai take ba wallahi sai mun had’a da addu’a da kuma rok’on Allah.”

 

Nan mahaifinta ya shirya shi da tawagarsa sukabi jirgin yamma sai zaria.

 

 

 

_Ayi hakuri da wannan saboda yanayin lafiyata_

 

 

Muje zuwa

Page 55 to 60

LAST PAGE

 

 

Abinda Dad d’inta ya fad’a mata haka tayi, sedai duk wanda ya kalli Afnan yasan tabbas bata cikin hankalinta.

 

Ba’a wani d’auki lokaci ba Dad d’inta suka k’araso suka d’auketa suka juya zuwa Legos.

 

Sai dare suka k’arasa gida inda suka tarar da mahaifiyar Afnan d’in da kuma yayyinta zazzaune suna jiran dawowarsu.

 

Suna shigowa da gudu Afnan taje ta rungume mahaifiyarta tana runtuma kuka tana fad’in “na rasashi Mummy, idan babu Affan nima mutuwa zanyi, bazan iya rayuwa da wani ba idan ba shi ba.”

 

Mummynta ta d’agota suna fuskantar juna tace “to kiyi shiru kar wani abu ya sameki kinji, ba zaki rasashi ba, zamu tabbatar da kin sameshi a matsayin miji indai yana raye,” nan dai sukaita rarrashinta tare da kwantar mata da hankali har suka samu ta d’an natsu.

 

Da k’yar suka samu tasha tea daga nan sukasa tai wanka sannan ta kwanta, nan da nan kuwa bacci yai awon gaba da ita.

 

falo suka dawo dukkaninsu suka barta tayi baccin, Mummy ta kalli Dad tace “Alhaji ya kamata fa kai wani abu akan lamarin nan, kana ganin yanda yarinya ta koma, ni ina ganin saboda abinda tai mishi ne yake mata asiri take irin wad’annan abubuwan.”

 

Dad yace “ko kad’an Hajiya abinda kike tunani ba haka bane, seda nai bincike na gano dagaske ne yaron ya rasu, ni ina ganin kawai wulak’ancin da tai mishi ne alhakin yake bibiyarta, kuma wannan laifinmu ne tunda bama kwab’a mata akan haka.”

 

Hajiya ta numfasa, sannan tace “hakane, duk da haka ya dace mu dage wajen ganin ta dawo daidai, ina ganin me zai hana mu nemo malamai suyi mata addu’a?

 

Dad yace “hakan za’ai insha Allah.”

 

Haka kuwa akayi babu irin malaman da ba’a kira sunyi mata addu’o’i da kuma bata magunguna ba amma ina.

 

Haka iyayen Afnan sukaita yin iya yinsu suna kashe dukiyarsu, har fita da ita asibitin k’asara akayi amma har yanzu ba nasara, sedai ta dangana ta hak’ura tunda ta tabbatar ta rasa Affan kuma bazai tab’a dawowa ba, amma har abada bazata tab’a iya cireshi daga ranta ba, don kuwa daga lokacin zuwa yanzu tayi aure har sau bakwai amma da tayi take kasheshi ta fito domin dama ta fad’awa iyayenta babu wanda zata iya zama dashi bayan Affan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button