Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

Suna ji suna gani haka suka hak’ura suka sa mata idanu, gadai dukiya iya dukiya amma ta kasa yi musu maganin matsalar d’iyar da suka fi so a cikin yaransu.
_To dama wa yace musu matsalar soyayya kud’i na maganinta, musamman ma matsala akan wanda ka cutar a rayuwa saboda soyayyar da ya gwada maka ta gaskiya._
Haka Afnan ta cigaba da zama a cikin gidansu har zuwa wannan lokacin yanzu batada aure, kuma bata da niyyar yi, domin tace ita in ba Affan ba bazata iya rayuwa da kowa ba, kuma koda an matsa mata tayi sai ta kashe auren ta dawo, hakan yasa ta cigaba da zama da iyayenta a cikin gidansu tana mai matuk’ar nadama da abubuwan da ta gudanar cikin rayuwarta musamman abinda taiwa Affan har ya rasa ransa saboda ita.
K’awarta kuwa tuni ta raba jaha da Afnan d’in musamman da ta lura ta zama haka haka, to dama ai haka rayuwa take mugayen kawaye zasu kaika su baro daga k’arshe kuma su gudu su barka, duk da dai ita Lateefa ta k’ok’arta akan bata shawara akan Affan itace tak’i ji tai kunnen uwar shegu.
Duk jijji da kan Afnan yanzu babu shi, son tak’ama da alfahari da dukiya duk babu shi, wayarta kuwa duk tsufanta ta kasa rabuwa da ita saboda hotunan Affan da kuma chat d’inda sukayi dashi, sedai in ta lalace ta gyara amma tak’i rabuwa da ita, tasan zata iya canza wata ta kwashe hotunan gaba d’aya a sabuwar, to amma chat d’insu bataso ta rasashi, kullum cikin yiwa Affan addu’a take da neman gafara wajen Allah.
Kullum tana manne da wayarta in kanaso kaga mugun tashin hankalinta to kai k’ok’arin tab’a wannan wayar.
Haka rayuwar Afnan ta cigaba da kasancewa har zuwa yanzu da nake baku labarin nan batayi aure ba, shekararta Arba’in da watanni har yanzu tana gidansu.
B’angaren su Inna kuwa Adnan ya maye musu gurbin Affan, tabbas ya rik’e amanar da aka bashi hannu bibbiyu, domin saboda su ya dawo da aikinshi garin zaria gabad’aya.
Bayan shekara d’aya shima mahaifinshi ya rasu sakamakon hawan jini, dama tunda ya rasa matarshi wato mahaifiyar Adnan d’in ya kamu da hawan jinin.
Adnan ya rushe gidansu Affan ya gina musu k’erarren gida ya zuba musu rantsatsun kayan more rayuwa masu kyau da tsada.
Daga k’arshe ya auri Yasmeen k’anwar Affan, ya sakata a sabon gidan da ya ginasu lokaci d’aya da na su Inna.
Haka Adnan ya zame musu kamar uba a rayuwa, D.P.O ya dawo zaria inda suka cigaba da zumunci tare da had’a matansu suyi zumuncin suma.
“Assalamu alaikum,” Adnan ne ya kwad’a sallama, Inna ta amsa musu tare da fitowa, sauran yaran suma duk suka fito dukkansu suna yi musu sannu da zuwa.
Shiga cikin falon sukayi dukkansu Yasmeen ta zauna dak’yar saboda tsohon cikin dake jikinta, Adnan yace “yauwa Inna dama inaso in kawo miki k’arar Yasmeen, wallahi kice mata ta daina yimin raki dan taga ina damuwa da lafiyarta, inda muma muna iya yin cikin nan har mu haihu in ana goma to tsaf zan haifosu ina dariya ma, amma ita bama haihuwar ba duk tabi ta dami mutane wai sai na kawota wajenki karta mutu a gida ita kad’ai, sai kace ni ba mutum bane.”
Inna da sauran yaran dariya suketa yi, Inna tace “kadai maidani kamar ba surukarka ba ko Adnan a gabana kake fad’in haka,” Adnan yace “to ai dama ke uwace ba suruka ba Inna.”
Nan dai sukaita hira cikin raha suna wasa da dariya amma banda Yasmeen, Adnan yana lura da ita yanda tasha kunu ta had’e fuska.
Adnan ya kalli Inna yace “Inna kin gani ko ta had’e rai, ki bata hak’uri in ba haka ba Allah yajin fara’a zataimin, bazan sake ganin fara’arta ba har sai an kwana biyu.”
Inna tai murmushi, sannan tace “ba ruwana kunfi kusa, wa ya isa shiga tsakaninku yaji kunya.”
Adnan ya juyo ya kalli Yasmeen yace “dan Allah kiyi hak’uri ko in miki tusa me warin gaske.”
Gaba d’aya d’akin aka kwashe da dariya harda gimbiya Yasmeen d’in.
Alhamdulillah
*Alhamdulillah ina godiya ga mahaliccina da ya bani ikon kammala wannan littafi lafiya, kuma anan na kawo k’arshen wannan labari me suna NA BAKI RAYUWATA, ina fatan da mazan da matan wannan labari zai zame musu ishara, suji tsoron Allah su dena yaudara, abinda basu saniba shine duk idan kayi yaudara komin daren dad’ewa wallahi Allah sai ya dawo gareka ya tab’a rayuwarka ko yayane, wasu suna ganin wauta ne da shashanci sawa rai damuwa akan dan ka rasa masoyinka, to inaso mu sani cewa shi so ciwone na musamman wanda yakeda wuyar warkewa kuma shi tab’a jiki yake harma da lafiya, idan kai kana ganin zuciyarka dakakkiya ce zaka iya jure yaudara idan anyi maka to wallahi akwai wad’anda zuciyarsu take da rauni cutar dasu a soyayya sai yasa su shiga mawuyacin hali, abinda wani zai jure wani bazai iya jurewa ba, mu daina yin yaudara muna jin farin ciki da kuma jin dad’i a ranmu duk wanda yai yaudara k’arshensa bazaiyi kyau ba, kawai in bakya son saurayi ko kuma in saurayi baya son budurwa tun farko fad’a mata kai tsaye ko ki fada mishi kai tsaye ka fita, inma ta cigaba ko ya cigaba da naci to kaidai ka fad’i gaskiya Allah bazai kamaka da laifi ba, amma yin hakan aso ba abu bane me kyau kayi amfani da masoyinka kawai domin cimma wani buri naka kuma sai ya sawa ranshi cewa ba wani bayan shi, bayan kai ka sani a ranka babu k’aunarshi ko kad’an, sai daga k’arshe bayan yayi nisa ya gane komai, kai mishi asarar cigaban rayuwa da dagula mishi lissafi da kuma b’ata mishi lokaci, ina fatan zamu ji tsoron Allah mu gyara ayyukanmu.*
*Ina k’ara baiwa ‘yan mata da samari shawara akan su daina cutar da wanda ya sosu tsakani da Allah da zuciya d’aya saboda wani k’aramin dalili ko akan abun duniya dukiya fararra kararra, kuma koda suna kaunarka saboda wani dalili mara tushe sun gwammace su cutar da kansu su hana zuciyarsu abinda takeso, to mu sani cewa lokuta da dama bama sanin daraja da kima da kuma muhimmancin masoyanmu sai lokacin da sukai nesa damu muka rasasu a lokacin ne muke gane babban kuskuren da muka tafka, dan haka wallahi muji tsoron Allah mu daina watsar da damarmu akan wani shirmemmen dalili namu, yin hakan yana haifar da nadama da dana sani wanda baka san iyakarsaba, Allah yasa mu gane.*
*Abinda na manta ban sanar ba shine wannan labarin ya faru da gaske ba k’irk’irarre bane.*
[ad_2]