Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

Haka suka kai k’arshen maganarsu cikin raha da barkwanci.
Bayan sun gama waya har ya ajiye sai yaji haka kawai yanaso ya lek’a yaga wainar da ake toyawa a ciki, jawo wayar ya sake yi tare da kunna data, sedai cikin rashin sa’a yaga datan nashi ta k’are, to da yake yanada kud’i hakan yasa ya siya data.
Cikin k’ank’anin lokaci sak’onni sukaita shigowa ba adadi sakamakon dad’ewa da yayi be hau ba, amma group d’in da Adnan ya sakashi mai suna sada zumunci shi yafi tarin sak’onni da yawa, hakan yasa yaketa faman jan tsaki.
Bayan sun gama shigowa duka sai ya fara duba Adnan yaga ai ya dad’e da sauka, shima har zai sauka sai yaji yana so ya lek’a cikin group d’in domin yaga wainar da ake toyawa.
Yatsanshi yakai ya danna ya shiga ciki a daidai lokacin wata yarinya ta turo hotonta tare da bayanin sunanta da garinda take, tsaki yaja tare da fad’in salon cinyewa mutane data akan shirme, a daidai yakai hannunshi zai goge hoton a daidai lokacin hoton ya bud’e, dakatawa da goge hoton yayi tare da k’urawa yarinyar idanu had’e da jin matsanancin bugun zuciya, mik’ewa zaune yayi, tare da dafe k’irjinshi da hannu d’aya, d’ayan hannun kuma ya d’ago wayarshi tare da cigaba da kallon halittar Allah mai cike da kyau da annuri.
A lokacin ne ya koma baya kad’an yaga dalilin turo hoton nata, ashe wai kowa yana gabatar da kanshi ne domin asan juna, ita kam wannan yarinyarma saida akaita damunta da magiya sannan ta turo da nata.
Affan ya sake duba wajen da ta gabatar da sunanta yaga sunanta Afnan, a bayyane ya nanata sunan a bakinsa “Afnan Affan,” ya sake k’urawa hotonta idanu, sai kuma yai murmushi.
Ganin anata yaba kyawun da hoton nata yayi yasa haka kawai yaji ranshi ya b’aci, lambarta ya lalibo tare da doka mata sallama ya taki sa’a tana online bata sauka ba, ta amsa mishi sallamarshi, sannan yace “kafin nace miki komai ina rok’on alfarma a gareki dan girman Allah ki cire hotonki da kika tura group d’in sada zumunta yanzu,” tace inason sanin dalili?” Affan yace “ki cire tukun zan fad’a miki dalilin daga baya.”
Ba tare da Afnan tace komai ba taje ta goge hoton da ta tura cikin group d’in, sannan ta dawo private tace “na goge, ina jinka meyasa kace inje in cire?”
Affan yace ji nayi raina ya b’aci da ana yaba kyawunki wanda da a fili suka yaba sai na b’atawa kowannensu rai, kema in kika sake d’orawa sai na had’a dake wajen yin hukunci, sai na b’ata miki rai, sai da safe kema ki sauka kuma karki sake ki kula kowa,” yana gama fad’in haka ya kashe datanshi ya kwanta, sedai bacci ya k’auracewa idanunshi, yasha k’aryata samarin dake cewa hoton fuskar budurwarsu yana musu gizo, sai gashi ya faru dashi hotonta kawai idanunshi ke haskowa sam bacci ya k’aurace mishi duk da kuwa yana jin baccin sosai amma yak’i d’aukarshi, in ya rufe idanun ita yake gani, hakama in ya bud’e.
Afnan kuwa saboda tsabar mamaki a kwance take amma tashi tayi ta zauna saboda jin abinda mutumin da ko sanin wanene shi batayi ba amma yake fad’in haka a kanta, karambaninshi ya burgeta, kuma ya bata mamaki, message d’in kawai take sake karantawa na kashedin da yai mata tana ta dariya ita kad’ai cikin d’aki.
_Wanene Affan? Ina mahaifinsa, wacece Afnan? anya Affan be fad’a so ba kuwa, in ya fad’a yaya zaiyi da haushin soyayyar da masoyan kansu da yake ji? to wai zama ta amince kuwa? ku biyo *????k’n mamie* domin jin cigaban labarin had’e da jin caakwakiyar dake cikinsa._
PAGE 5 to 10
Yau ya taki sa’a ya tarar da Adnan a online, da yake abokin nashi gwanin tsokana ne sai yaje cikin group yana cewa bari in gabatar muku da abokina Affan, ya fad’i sunanshi da garinda yake, kawai Affan beyi aune ba sai gani yayi Adnan ya tura hotonsa cikin group.
Yana turawa aka hau yabawa saboda tabbas ba karya Affan kyakkyawane sosai.
Affan ya gama yin bambaminshi ya hak’ura, sannan ya sanar da Adnan halinda yake ciki a yanzu, Adnan yai mishi dariya sosai tare da tabbatar mishi da ya fad’a soyayya, kuma yai gaggawar sanar da ita kar a rigashi, share zancen Adnan yayi, har zai sauka sai yaji yana son ya duba yaga ko yarinyar da ta hanashi bacci jiya tana online, yana dubawa kuwa cikin ikon Allah ya ganta, itama hawowarta kenan.
Hotonsa ta bud’e wanda aka turo ta nunawa k’awarta tace “kai! k’awata kinga wani had’ad’d’en gaye a cikin group d’innan kuwa, wallahi ya had’u, nidai yamin, har naji wani abu game dashi a cikin raina.”
K’awarta me suna Lateefa ta d’ago tare da kallon hoton da Afnan ke nuna mata, tace “gaskiya kam ya had’u, amma sedai daga gani wannan talaka ne bakya ganin yadin dake jikinshi d’an dubu biyu ne fa, me zakici dashi?”
Afnan tace “gaskiya yayi min, kuma shima naga alamun yana sona, kai gaskiya ina sonshi,” Lateefa taja tsaki, sannan tace “ai sai kije kiy tayi banza ‘yar wahala, sam bakida class kina ‘yar manyan mutane a babban gida kina kula k’ananan gayu talakawa salon jawa kai raini, me zaki samu a wajensu banda b’ata lokacinki.”
Afnan tai dariya tace “ba zaki gane bane Lateefa, saboda ke sam bakisan menene so ba, kedai kawai a baki, to ni gaskiya gayen nan yayi min, kuma duk da yana talaka ai baza’a rasa abinda za’a tatsaba a wajenshi.”
Afnan takai hannunta kan lambar da yai mata magana da ita jiya ta duba ko yana nan, cikin ikon Allah kuwa ta taki sa’a yana online, sedai tasan ko a haukace take bazata tab’a iya fara yi mishi magana ba balle ya rainata.
Tana cikin wannan tunanin sai ga sak’onshi ya shigo kamar haka
_Aminci a gareki sarauniyar kyawawa, burinki ya cika kin canzamin k’udurina, zuciyata, da kuma rayuwata, wai ke mutum ce kuwa?”_
AFNAN _Na shiga uku, meyasa kace haka?_
_AFFAN _Saboda ina jin abinda da bansanshi ba sai a kanki, duk lokacin da naga koda sunanki ne sai naji zuciyata na bugawa da sauri, gabad’aya na zama wani sha sha sha tun ranar da na fara ganin hotonki, ban tab’a tsintar kaina a irin wannan yanayin ba sai a kanki, wai ance alamun da nakeji so ne, ni kuma na k’aryata hakan, saboda nasan cewa bana soyayya kuma ban tab’a yi ba sedai ko kece kike sona shiyasa nake jin haka a kanki, haaaa yarinya ta fad’a sona, ina tausaya miki wahalar da zakisha a wajena dan ba iya komai ba, ita kanta soyayyar bansan ya take ba”_ sai ya tura mata harda hoton gwalo.
Afnan ta kalli Lateefa da sauri tace “dan Allah taso kiga abinda gayen nan yake cewa,” nan fa sukaita karanta sak’onshi suna tuntsura dariya, Lateefa tace “da alama wannan be tab’a soyayya ba, gashi ya fad’a hannun shu’uma akan so, hhhhhh wai bema san fa abinda yakeji me sunansa ba, ya kamata ki fahimtar dashi domin kuwa wannan irinsu ne ake cewa zare da akala sai inda kika jasu zasuje,” Afnan tai dariya, sannan tace “barshi ai ya shigo hannuna,” sukai dariya sannan suka tafa, daganan kuma ta cigaba da bashi amsa kamar haka.
_AFNAN _Allah sarki, kaga ban sanka ba, bansan koda sunanka ba, amma daga ganin hotona ka fad’a sona._
AFFAN _hum wane ni, ai kinfi k’arfina, talaka ne ni wa ya aikeni yin soyayya dake, daga ganinki ke ‘yar masu kud’i ce._
AFNAN _Eh bakayi k’arya ba ni ‘yar masu kud’i ce, amma ai babu ruwan so da dukiya ko mulki._
AFFAN _”To ke kina sona ne?”_