HAUSA NOVELNa Baki Rayuwa Ta

Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

 

AFNAN _”Eh ina sonka mana, saboda na dad’e da gane kaima kana sona, kaga kenan mun fad’a k’aunar juna a lokaci d’aya kenan.”_

 

AFFAN _”Bantab’a sanin menene so ba sai a kanki, kin shiga cikin zuciyata ta yadda bazan iya mantawa dake ba har abada, har yanzu mamakin kaina nakeyi wai ni Affan nine na fad’a soyayya, ina fatan zaki bani damar shiga zuciyarki domin yad’a soyayyata a ko’ina na cikinta, tare da kafa sansanin yak’ar duk wanda yai k’ok’arin kawo farmaki cikin wajen da ya zama fadar mutum d’aya tilo wato ni.”_

 

AFNAN _”Tunda ka samu damar na baka lokacina hakan ya isa tabbatar maka da ka samu zuciyata, kasan shi so a ko’ina yake shine sanadin dake rik’e mutum, to nima hakan ce ta faru dani, ka rik’eni da soyayyarka, dare yayi ya kamata mu kwanta ko?”_

 

AFFAN _”Nagode gwanata, ji nake kamar munyi shekaru a tare da juna, kuma ji nake kamar karmu rabu, amma ya zama dole in barki ki kwanta dan banaso in hanaki bacci kiyi ciwon kai.”_

 

AFNAN _”Nima banason na rabu da kai, amma karka damu bamu rabu ba, muna tare da juna a cikin zuciya, ka kulamin da kanka, kuma kayi bacci banaso ka bari tunanina ya hanaka bacci kaji?”_

 

AFFAN _”Angama gimbiyata abinda kikace shi za’ayi, sai da safe nima ki kulamin da kanki.”_

 

Nan sukayi sallama suka sauka a tare, Afnan tana duba wayarta ba tare da ta juyoba tace “gaskiya k’awata gayen nan ya fad’a da yawa, har ya d’an bani tausayi, kuma wallahi ya iya tsara kalami kamar ba sabon kamu ba.”

 

Shirun da taji ba’a bata amsa bane yasa ta juyo, tana juyowa taga ashe har tayi bacci, agogo ta kalla taga d’aya da rabi, tayi murmushi sannan ta girgiza kai, a fili tace “gaskiya Affan kazo da sa’a da har ka iya samun lokacina har haka kuma cikin k’ank’anin lokaci ba tareda kasha wahala ba, kaine irin namijinda zai nakeso, wanda zai rik’a rik’eni tsawon lokaci da dad’ad’an zantukansa, amma sedai ka kwafsa da kazo a talaka.”

 

Kwanciya tayi, nan da nan bacci yai awon gaba da ita, sab’anin Affan, duk yanda yaso yai baccin domin cika umurnin masoyiyarsa ya kasa, amma duk da haka yana kwance ya runtse idaunshi, sedai ba baccin yakeyi ba.

 

Tun daga ranar so da shak’uwa me k’arfi ya shiga tsakaninsu, kuma tun daga lokacin Affan ya daina samun wadataccen bacci da lokacin kanshi, domin hatta koyar da yara karatu da yake ya ragu, gabad’aya dai al’amuransa duk sun canza.

 

Yauma chat suke ta zubawa, ya bata tarihinsa da garinsu hatta sana’arshi, itama ta fad’a mishi nata tarihin, suna cikin magana sai wani saurayi yai magana a cikin group yace Afnan ta bashi lambarta yana so yai muhimmiyar magana da ita, nan da nan kamannin Affan suka canza cikin sauri ya bashi amsa da cewa “malam matar aure ce, in ta baka lambarta ubanme zakai mata?”

 

Wannan saurayin yace “yi hak’uri ai bansan matar aure bace saboda naga basa zama cikin group d’in da yake had’e da na maza.”

 

A ranar haka Afnan ta wuni tana rarrashi saboda kawai ance ta bada lambarta, da k’yar ta samu ya hak’ura.

 

Washe gari ma hakance ta sake faruwa dama shi Affan be cika ma lek’a kowane group ba, shi burinshi kawai yayi chat da Afnan, in har tana online bashida lokacin kowa sai nata, to saboda ganin an fara kula mishi budurwa yasa yafara shiga cikin group d’in da duk take ciki har yana magana ana hira dashi domin asan yananan fa duk wanda ya kulata zaiji ba dad’i.

 

To yauma yana shiga yaga ta gaisa da wani har yana turo mata da hoton heart, dawowa private yayi ya sameta yace “Afnan, ta amsa, yace indai kina k’aunata kamar yanda kike fad’i to ki fita daga group d’incan, kuma wallahi karna sake ganin kin kula wani k’ato.”

 

Afnan ta dawo mishi da amsa tace “haba gwanina, menene na tayar da hankalin har haka, menene na b’ata ran, karka manta kaine fa me jan ragamar zuciyata, kaga kuwa dole ne inbi duk wani umurni naka, ka kwantarmin da hankalinka please, kafa san duk duniya babu abinda nake adawa dashi wanda ya wuce b’acin ranka, bari inje in fita,” tana gama fad’in haka taje ta fice daga cikin group d’in, sai a lokacin hankalin Affan ya fara dawowa jikinshi.

 

Shima Affan washe gari wata ta biyoshi private tai mishi magana, ya kwashe komai ya fad’awa Afnan, ya fad’a mata amma yai blocking d’in yarinyar, nan da nan Afnan ta haukace mishi, kuma ta tayar da rigima akan sai ya fita daga cikin group d’in, kuma sai yasa an sakata duk wasu group da yake ciki, hakan kuwa akayi, amma duk da haka yayi dana sanin fad’a mata domin yaga fushinta, kuma yasha wahala kafin ta sauko.

 

A tak’aice dai kowane group sai da aka san suna matuk’ar k’aunar juna, saboda tsabar shak’uwarsu wata da zahra ake kiransu, amma saboda tsabar kishin da suke gwadawa juna saida takai duk sun fice daga kowane group ya zamto basuda group ko d’aya, su babban tashin hankalinsu a kula d’aya daga cikinsu, kuma dan sun rabu da dukkanin group d’insu ko a jikinsu, hakanma sai yafi musu dad’i da kwanciyar hankali, duk da dad’ewar da sukai a groups d’in da kuma irin shak’uwar da sukai da mutanen ciki amma wallahi ko d’ar basuji ba, sufa basuk’i su cigaba da rayuwarsu ba su kad’ai.

 

Tunda Affan yafara soyayya komai nashi ya canza, idan yana chat da Afnan ko zuwa kusa dashi baya son anayi balle ayi mishi magana, k’annenshi da yake matuk’ar so da kulawa dasu da karatunsu ya daina, in kuwa su sukazo ya koya musu sai ya koresu yace su tafi ba yanzu ba, gabad’aya yanayin Affan ya canza in kanaso kaga b’acin ranshi to ka katseshi yana chat, har fuskarshi sai ta bayyanar da b’acin rai, hatta wajen sana’arshi sunga canji, baya k’aunar su tayar dashi saboda kawai wata siyayya tasu in yana chat da afnan, a tak’aice a ko’ina ya tsani ana kulashi idan yana magana da ita, yafi buk’atar a barshi ya kad’aice, abinci kanshi baya son ci yanzu, saboda gani yake zai tab’a musu lokaci shi da abar k’aunarsa, shifa in yana magana da ita to kowane irin abune baya son katse maganarsu ya aikatashi, sedai a jira har ya gama, kai ko baya chat ko magana da ita a waya to yafi buk’atar a barshi ya kad’aice yaita kallon hoton Afnan yana tunaninta, ko kuma yana karanta chat d’insu yana d’ebemai kewarta.

 

Kullum tare suke hawa whatsapp, kuma tare suke sauka, d’aya baya yarda ya tafi yabar d’aya.

 

Soyayya suke gwadawa juna bil’hak’k’i da gaskiya, basa k’aunar b’acin ran junansu, koda yaushe kowannensu burinsu su farantawa junansu rai, idan Affan bashida lafiya Afnan har kuka take, sai ta kirashi yafi a k’irga tana bashi kulawa kuma kullum tana fad’in ya kula mata da kanshi, dan Allah kar yai ciwo, ta damu dashi fiye da yanda yake tunanin samu daga gareta.

 

Yau Lahadi, hakanan yau Affan ya tashi sukuku, ga bacci yanaji, ba yau bane rana ta farko da ya tashi a makare, ko wajen aikinshi yanzu a makare yake zuwa, to yaushe ma ya kwanta balle har ya samu ya tashi da wuri, yana tashi wayarshi ya fara laliba ya duba ko zaiga kiranta be gani ba, sai ya bud’e data domin sak’onni su shigo ko akwai nata a ciki, kafin su gama shigowa sai ya tashi domin zuwa ya gabatar da abubuwan da ya saba gabatarwa, bayan ya gama ya karya ya sallami Inna da k’annensa ya tafi kasuwa, har zuwa lokacin bega sak’on Afnan ba kuma bata online, kuma ya kira wayarta a kashe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button