HAUSA NOVELNa Baki Rayuwa Ta

Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

 

Duk yabi ya damu saboda bata tab’a yi mishi haka ba, haka ya kasance a shagon sukuku, kasa hak’uri yayi ya tura mata sak’o a layinta kamar haka.

 

_Na makance a dalilin rashin gani daga kyakkyawar fuskarki mai tsantsar kyau wadda Allah mabuwayi ya azurtaki da ita, na kurmance a dalilin rashin ji daga zazzak’ar sassanyar muryarki mai tsananin sanyi wadda ta nunka busar sarewa zak’i da dad’in sauraro, rayuwa ba tare dake ba tamkar rayuwane a cikin gidan kurkuku, dan Allah tawan kiji tausayina ki kunna wayarki, nine naki AFFAN._

 

Afnan na zaune ita da k’awarta hirar Affan d’in kawai suke tana bawa Lateefa labarin yanda Affan ya mato a kanta, Afnan tace “yanzu ne dai-dai lokacin da ya kamata, ki tsaya ki koma gefe kiy kallo, ba dai na kashe wayata ba, to jira kiga me zai faru,” Lateefa tace “shiyasa kike burgeni k’awata bakya wasa,” suka sa dariya suka tafa.

 

*WANENE AFFAN?*

_Shin wai me Afnan take nufi ne?????????, Allah sarki Affan bawan Allah,???? ya kamata muji wanene Affan a next page, sannan muji wacece Afnan._

 

PAGE 10 to 15

 

 

*WANENE AFNAN?*

Afnan d’ane ga malam Bukar, mahaifiyarsu sunanta Halima, wadda suke kiranta da Inna.

 

Su shida ne a wajen iyayensu maza uku mata uku, Affan shine babba a cikinsu, kuma saida akai shekara da shekaru da haihuwarsa har sun cire rai da tsammanin sake samun wasu yaran sai gashi cikin ikon ubangiji a bayanshi sun haifi yara har biyar, sedai Affan ya basu shekaru da dama.

 

Suna zaune ne a garin Zaria, a wata unguwa dake cikin gyallesu.

 

Mahaifin Affan talaka ne, sedai Alhamdulillah yana samun na rufin asiri, shago gareshi a kasuwa da yake siyarda takalma shadda da atamfofi sedai kayan tsirarru ne bawai sun cika shagon bane, kuma inda Allah ya taimakeshi shagon da kayan ke ciki nashi ne.

 

Daga Affan har kan k’annaenshi duk makarantar kud’i sukayi, duk da kasancewar mahaifinsu ba wani bane a k’asa, amma in kaga yaranshi zakace yaran attajirai ne, domin tun daga kan karatunsu har suturunsu da abincin da sukeci duk na alfarma ne.

 

Mahaifin su Affan ya rasu ne sakamakon typod da yayi fama dashi na lokaci guda, sa’annan ya rasu a lokacin Affan yana tsakiyar karatunshi, a lokacin yana gab da kammala diploma d’inshi.

 

Bayan Affan ya kammala Diploma d’inshi ya dawo gida tare da dakatar da karatunshi, da takardun diploman nashi yaita yawon neman aiki, to mundai san yanda neman aiki ke wahalr samu a k’asa, hakan yasa yaita nema amma ina be samu ba, gashi d’an abinda mahaifinsu yabar musu duk ya k’are, inda Allah ya taimakesu shine shagon da yake siyar da kaya an rufeshi ne, kuma kayan suna nan, hakan yasa ya yanke shawarar cigaba da kulawa da kasuwancin mahaifinshi da kulawa da mahaifiyarsu da kuma k’annenshi, saboda idan ma yace zai cigaba da karatun to waye yake da shi da zai cigaba da biya mishi kud’in makaranta, me biya mishi Allah ya d’auke abinshi, kuma wa zai barwa hidimarsu Inna, wad’annan dalilan yasa ya ajiye karatu gefe guda.

 

Haka Affan ya taso cikin nuna kulawarshi ga Innarsu da kuma k’annenshi, yana matuk’ar k’aunarsu, zamu iya cewa ma duk duniya babu wad’anda yake so da k’auna sama da Innarsa da kuma k’annensa.

 

Affan yana da aboki mai suna Adnan, tun suna yara suke tare, suna k’aunar juna k’auna ta ban mamaki, sun taso tamkar ‘yan uwa ciki d’aya, tare sukayi primary d’insu, kuma tare sukayi secondry d’insu, daga babban makaranta ne sun fara tare Affan be dad’e da shiga ba Babansu ya rasu, mahaifin Adnan yaso ya cigaba da biya musu su duka duk da shima ba wani k’arfine dashi ba sedai rufin asirin Allah, to amma fur Affan yak’i yarda shi ba inda zai tafi yabar Innarshi da ‘yan’uwanshi, hakan yasa dole ya canza makaranta ya dawo zaria da karatunshi yayi diploma, yanzu haka Adnan yana can yana yin digree, Affan beda abokin shawara daya wuce Adnan domin shi kad’ai ne abokinsa.

 

Har yanzu Adnan yana can yana karatunshi a waje shiyasa basa had’uwa da Affan sedai suyi waya kawai,

 

Affan kyakkyawan saurayine, domin in ka ganshi zakasha wannan matashin saurayin nan ne na india wanda yai film d’in koyla wato sharokhan, wannan kenan.

 

 

*WACECE AFNAN?*

Afnan ‘yace ga wani attajiri mai suna Alhaji Bukar, yanada tarin dukiya da arzik’i masu tarin yawa, matarshi d’aya yaranshi uku maza biyu mace d’aya, suna zaune a garin Legos, Afnan itace auta, kuma munsan duk auta d’an gaban goshi ne, gashi dama iyayenta suna matuk’ar k’aunarta, yayyinta maza sam basa jin dad’in tara samari da take tun ma kafin ta tafi karatu, sun so a barta tai karatu a gida saboda su sa mata idanu iyayensu sukace sun matsa mata lamba, iyayenta sun bata ilimi na boko da na islama, yanzu haka tana zaune ne a makaranta tana karatu, tana gaf da kammala digree d’inta na biyu, kuma duk wayar nan da suke da Affan a makarantar tasu takeyi.

 

Lateefa k’awar Afnan ce sun dad’e tare saboda halinsu yazo d’aya, hakan yasa ma koda suka gama karatu suka yanke shawarar makaranta d’aya zasu cigaba da yi.

 

Itama Lateefa ‘yar masu kud’ice dama su basa abota da talakawa sai masu kud’i ‘yan’uwansu, hatta samari ma sai manyan yara, sunsha hawa sama su fad’o ita da Afnan akan kula k’ananan samari da take talakawa, a cewarta tana zubar musu da class ne, tasha fad’i cewa da ita Allah ya baiwa shahararren kyawun Afnan da ba haka ba Allah kad’ai yasan me zatayi, yanzu haka suna gaf da kammala karatunsu su koma gaban iyayensu, wannan kenan.

 

 

*CIGABAN LABARIN*

Bawan Allah Affan kasa zaman shagon yayi ya rufo ya dawo gida, yana shigowa Inna tana tsakar gida tana alwala, bayan ta amsa sallamarsa ya gaisheta ya wuce d’aki.

 

Yana zama k’aninshi me suna Hassan ya shiga d’akin Affan d’in da sauri yace “yaya an bamu aikin gida dan Allah ka koyamin ka…… be k’arasa fad’in abinda yakeso ya fad’a ba Affan ya daka mishi tsawa tare da cewa “fita ka bani wuri,” yaron ya fito yana hawaye, dama yara basa k’aunar tsawa musamman ma su da tsawar take bak’uwar abu a wajensu tunda be saba yi musu haka ba, Innace ta kirashi ta tambayeshi dalilin hawayen, Hassan yace “yayane naje ya koyamin aikin da aka bamu a makaranta ya koroni, kuma yana kukama,” Inna tayi jim, sannan tace wa yaron yaje ya ajiye littafin yai alwala yai sallah, idan Ahmad yayansa ya shigo sai ya koya mishi, yaron yace mata to ya wuce d’aki domin ajiye litattafan, tayi alwala ta idar sannan ta taso ta taho d’akin Affan, tai sallama tafi biyar besan tanayi ba, d’aga labulen d’akin tayi ta shiga, kwance ta tarar dashi, kuma abun mamaki ba bacci yakeyi ba, idanunshi k’irrrr a sama ya k’urawa silin ido.

 

Inna ta jijjigashi sannan ne ya dawo cikin hayyacinshi, sedai hawayen da taga suna gangarowa kan fuskarshi ne yai matuk’ar tayar da hankalinta.

 

Zama tayi a kusa dashi sannan tace ya tashi ya zauna zasuyi magana, babu musu yayi yanda tace, Inna ta kalleshi tace Affan ka canza, ba ni kad’ai na fahimci canzawarka ba hatta ‘yan uwanka sun lura da hakan, saboda yanda kake basu kulawa da yanda kake jansu a jiki duk ka dena, komai naka ya canza, hatta wajen aiki yanzu a makare kake zuwa, abinci ka daina maida hankali kaci, sau tari yanda aka ajiyeshi haka za’a zo a fito dashi, bayan haka ga damuwa yau da naketa gani a fuskarka tun safe, sai kuma gaka ka dawo a irin wannan lokacin da tunda ka fara aiki sai ciwo ko d’aya daga cikinmu wata buk’ata tamu ta taso ta gaggawa kake dawowa domin biya mana buk’atunmu, sai gaka ka dawo yau a irin wannan lokacin Affan ni mahaifiyarka ce, duk duniya baka da wadda ta fini, ya kamata ace ka sanar dani abinda ke damunka, fad’amin menene ya canza maka rayuwa haka lokaci guda?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button