HAUSA NOVELNa Baki Rayuwa Ta

Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

 

Affan yace “Inna ki kwantar da hankalinki, bakomai fa, kawai kwana biyun nan ne bana jin dad’in jikina, kuma haka kawai naji bana son hayaniya shiyasa, amma yanzu idan nai wanka insha Allah zanje asibiti a dubani.”

 

Inna tace “to Affan Allah yasa gaskiyane abinda ka fad’amin, ka rik’a tunawa da cewa kai kad’ai ne garemu wanda Allah yasa yake tallafamana, kuma kai kad’aine babba a cikin yaran nan, ba zamuso mu rasaka ba kamar yanda muka rasa mahaifinku,” muryarta ce ta fara rawa hawaye ya fara fitowa daga idanunta, hakan ne yasa tai saurin tashi tabar d’akin.

 

Ganin hawaye a idanun mahaifiyarshi ya matuk’ar tayar mishi da hankali, shi kanshi yasan baya jin dad’in yanayin da yake ciki a yanzu, amma ya zaiyi, abun yana damunshi musamman da yanzu damuwar tashi ta fara wuce kanshi ta fara tab’a ‘yan’uwansa.

 

Wayarshi ya jawo ya lalibo lambar Adnan ya kirashi, bayan sun gaisa Adnan ke tambayarshi ya yaji muryarshi wani iri, Affan yace “abokina ina cikin damuwa,” Adnan yace “subhanallah, meke faruwa?”

 

Affan be b’oye mishi komai ba ya sanar dashi cewa tun daga had’uwarshi da yarinyar nan komai nashi ya canza, gashi itama ya daina samunta a waya akan damuwar hakanne har Inna ta gane halinda yake ciki, hatta maganar da sukayi da Inna duk ya fad’a mishi komai.

 

Adnan ya numfasa sannan yace “abokina na tausayawa halinda kake ciki, kuma kusan nine silar shigarka cikin wannan halin tunda nine na kaika group d’inda ka had’u da yarinyar,” Affan yai saurin katseshi, tare da cewa tsaya dan Allah, nifa bance ina danasanin had’uwa da ita bane, na fad’a makane ka bani shawara yanda zan san gidansu inje, kuma ka bani shawarar yanda zan b’ullowa su Inna su daina shiga damuwa in ina cikin damuwa.”

 

Adnan yace “ai kuwa indai akan damuwar su Inna ne akanka to babu mafita se ranar da kaima sukaga d’orewar farin ciki kan fuskarka, dan haka ni shawarata kawai ka rabu da ita,” wata razananniyar k’ara Affan ya saki yana fad’in “what! Adnan, kai kake bani shawarar nan kai da nake kallonka a matsayin masoyina, gaskiya kaci sa’a kaine, wallahi da wani ne sai na zazzageshi,” yana gama fad’in haka ya katse wayarshi yana huci.

 

B’angaren Afnan kuwa fitowarsu kenan daga lecture anyi wanka ana hutawa ta cewa k’awarta “yanzu ne ya kamata in kunna wayata inji halinda gwanina ke ciki,” Lateefa tace “um harda su gwanina kamar wadda take k’aunarshi da gaske,” Afnan tai dariya, sannan tace “ke wallahi ina sonshi, tunaninshi ne fa yasa yau kika ganni wani iri, matsalar kawai talakane shi, amma duk da ina sonshi bazai hanani tatsarshi ba.”

 

Wayarta ta kunna, tana kunnawa taga sak’onninshi nata shigowa bi da bi, Afnan tai murmushi, sannan ta cewa Lateefa “matso kiga sak’onnin da ya tutturo min, nan suka zauna suka karance dukkanin sak’onninshi wajen guda ashirin da biyar da ya turo mata a d’an lokutan nan kawai da ta kashe wayarta.

 

Lateefa duk iya shegenta yau saida ta kalli Afnan tace “gaskiya gayen nan ya fara bani tausayi, Afnan ki sassauta masa, ina jin tsoron ranar da alhakinshi zai bugaki da k’asa fa,” Afnan ta kalleta tana dariya tace “a’a malama Lateefa yau kuma kece da wa’azi,” basu sake cewa juna komai ba Afnan ta danna lambarshi ta kira a yayin da Lateefa ta shiga wanka itama.

 

Affan na kwance yaga wayarshi tana ringing, cikin sauri ya d’aga ganin wadda ta kira, yana karawa a kunnenshi muryarshi na rawa yace “Afnan ina kika shiga ne, na shiga damuwa matsananciya, ji nake duniya taimin zafi, dan Allah Afnan na rok’eki karki sake nisanta kanki dani, *NA BAKI RAYUWATA* a yanzu kece kad’ai kike jan akalarta, wallahi a yanzu gani nake kamar dominki kad’ai nake rayuwa, dan girman Allah karki sake yin nesa dani, kece rayuwata, kece walwalata, kece komai nawa, idan kika sake tafiya koda na awa d’aya ne to komai nawa zai sake tsayawa cak, Afnan ina k’aunarki, idan babu ke babu raina, dan Allah kiji tausayina karki sake tafiya ki barni kinji, kuka yakeyi sosai sai kace k’aramin yaro, har gobe Affan mamakin kanshi yakeyi yanda ya sauya wai shine yau ke kuka akan mace macenma da bai tab’a ganinta ido da ido ba sai a hoto.

 

Duk rashin imani irin na Afnan saida jikinta yai matuk’ar sanyi jin halinda tai silar jefa Affan d’inta.

 

Afnan tai k’arfin hali cikin sassanyar murya harda d’an had’awa da kukan k’arya, a daidai Lateefa ta fito taji tana cewa “Affan nayi kewar rashinka, saboda tsabar kewarka da nayi yanzu haka gani a kwance banda lafiya zazzab’i ya rufeni, kayi hak’uri na fika shiga damuwa da shiga matsanancin mayuwacin hali, nima ba asan raina hakan ta faru ba, munje lecture ne bayan an tashi mukaje masallaci yin sallah saboda munada wasu lecture d’in sai nabar jakata a class da wayata a cikk koda na dawo babu wayar an d’auke an cire min layikana,m an tura cikin jakar an tafi da wayar, yanzuma wayar k’awata na ara nasa sim d’ina na kiraka dan in sanar dakai halinda ake ciki, ni dama damuwata kaine, nasan zaka shiga damuwa in baka ganni ba, kuma nima haka,” duk wad’annan bayanin duk a cikin kukan k’arya takeyi, in kukaga yanda Lateefa tai saranda ta k’ame a tsaye sai tafa hannu take tana salati, ita kuwa Afnan sai d’aga mata hannu take alamun tai shiru karta tona mata asiri.

 

Affan ya numfasa sannan yace “to kiyi shiru kinji ai yanzu gamu a tare, kuma mun gode wa Allah da basu tafi da sim d’in ba, kuma kema da tun lokacin da abun ya faru ma kin sanar dani da tuni kina tare da wata wayar, sedai koda irin haka ta faru ki rik’a gaggawa wajen sanar dani kinji.”

 

Afnan tace “to”

 

Affan yace “yanzu ki fad’amin wace kalar waya kikeso a ranki?”

 

Afnan cikin salon yaudara tace “a’a banso in d’ora maka d’awainiya ka barshi, duk da nasan tunda Dad be dad’e da siyamun wannan ba ko na sanar dashi an sace zaice ba ruwanshi sakacinane ya jawo, amma ni insha Allah zanyi k’ok’ari inga na siya wata koda k’arama ce wadda bata kai waccan ba.”

 

Affan yace “ok saboda ni talaka ne kina ganin banda arzik’in da zan iya siya miki waya ko? in bakyason b’acin raina kawai ki fad’amin.”

Afnan tace “akwai wata waya da ake yayi, amma gaskiya tanada tsada,” Affan yace nawane kud’inta? Afnan tace “dubu tamanin ce,” Affan yace “ok yanzu ba kud’i a account d’ina, amma zanje shago ki turomin da account number d’inki, kafin in k’arasa, zanje yanzu in d’auka inje bank in turo miki, kuma ina turowa kije ki cire ki siyo wayar please bazan iya jure rashin jinki ba wallahi,” nan dai sukayi sallama, cikin sauri ya fito ya shiga d’akin Inna yace mata zaije asibiti daga can zai wuce shago akwai wad’anda sukazo suna son kaya, Inna tai mishi fatan alkhairi sannan ya fice cikin sauri.

 

 

Muje zuwa

 

PAGE 15 to 20

 

 

Afnan ta kalli Lateefa wadda har yanzu take k’ame a tsaye tace “malama wannan kallon fa? itadai Lateefa batace komai ba kallonta kawai takeyi, Afnan tai murmushi sannan tai fari da ido, ta cigaba da cewa nan da ‘yan wasu mintuna 80,000 dubu tamanin zasu shigo account d’ina.”

 

Lateefa ta k’araso ta zauna tana goge jikinta da ya kusa bushewa, ta kalli Afnan tace “a’a fa Afnan wallahi ki sassautawa bawan Allahn nan, wai ba kince min kina sonshi ba, to meyasa kike mishi haka kuma?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button