HAUSA NOVELNa Baki Rayuwa Ta

Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

 

Afnan tai murmushi tace “ke shaidace akan halina, idan bana k’aunar mutum zanci kud’inshi kuma ya fuskanci wulak’anci kala kala a wajena, amma tunda kikaga ina baiwa Affan lokacina kema kinsan ina k’aunarsa, Affan irin mazan da nake muradin samu ne, sedai ya kwafsa wallahi, da ya tashi zuwa sai yazo a talaka.”

 

Suna cikin magana sai taji k’ara a wayarta, tana dubawa taga ya turo mata da budu d’ari a maimakon dubu tamanin, wani sak’on ne na test message ya shigo, wai ta siya wayar ragowar kuma tasa kati.

 

Nan ta hau murna, ta nunawa k’awarta kud’in da ya turo mata, ta tura mishi da sak’on godiya tare da sanar mishi da cewa idan ta siyo tai caji zata kirashi.

 

Bayan ta gama tura sak’on sai ta kashe wayar, sannan ta kalli Lateefa tace “zuwa anjima sai in kunna wayata in cigaba da amfani da kayata, ga wayata dama tana tare dani, ga kuma kud’ina kwance a account.

 

Tun daga wannan lokacin Afnan ta sakashi yaita yi mata hidima, da kad’an da kad’an ya fara cinye kud’in shago, akwai lokacin da akai mishi waya aka had’a baki da Lateefa suka kirashi a waya Lateefa na kuka ta sanar dashi Afnan bata da lafiya, har an bata gado zatai kwana biyu, kuma ta kasa samun ‘yan gidansu a waya, sunaso ya ranta kud’i kafin su samu iyayensu suzo sai a dawo mishi dashi, Allah sarki bawan Allah a lokacin hankalinshi yai mugun tashi, gashi babu kud’i a hannunshi, kuma bazai tab’a iya bari Afnan d’insa ta cutu ba balle har yakai ga rasata, a lokacin bashida ko sisi amma ya amsa mata yace ta d’an jirashi nan da ‘yan mintuna.

 

Cikin d’aki yake a tsaye yanata kai kawo, yana tunanin mafita, nan da nan ya tuno da mashin d’insa, cikin sauri ya fito daga d’aki ya fice ko Inna be yiwa sallama ba, mashin d’insa dake k’ofar gida yaja ya mik’i hanya, wajen siyarwa yakai mashin d’in nasa aka siya aka bashi kud’in, dubu saba’in aka siya, dama dubu talatin suka nema, ana bashi yaje ya tura musu duka kud’in ko d’ari biyar be cira ba.

 

Bayan Afnan ta fara jin sauk’i ta Affan yayi yayi Afnan ta bari yazo ya dubata tace a’a ya bari taji sauk’i ta kusa kammala karatunta, in ta dawo gida legos sai yazo, dole hakanan ya hak’ura.

 

Affan ne kwance a katifa suna hira da gwanarshi Afnan, godiya take k’ara yi mishi kan yanda yake kulawa da ita.

 

Affan ya tura mata da amsa yace _”kibar godiya Afnan, nine na cancanci godiya a gareki da kika mallakamin zuciyarki duk da kasancewata talaka, ke ‘yar masu kud’i amma kika k’aunaceni tsakani da Allah, kikaimin k’ololuwar so, *na baki rayuwata* kika karb’a kika rik’e hannu bibbiyu, Afnan a duniyar nan babu abinda zaki nema wanda bazan iya yi miki shi ba, nidai fatana kawai ki cigaba da rik’e amana, a kanki nasan so, nasan dad’inta, dan Allah karki bari nasan d’aci da rad’ad’inta, Afnan ina yi miki fiye da son da romeo da juliet sukayi wa junansu, ina miki fiye da k’aunar da laila da majnoon suka gwadawa junansu, ina yi miki fiye da son da jarumin nan na cikin film d’in titanic ya gwadawa budurwarsa, a lokacin da ruwa ya jirkitar dasu cikin jirgi, saurayin ya gwammace ita ta rayu shi ya mutu, haka ya daskare a cikin ruwa matacce ita kuma ta rayu, amma har tsufanta ta kasa mantawa dashi, to ina yi miki fiye da wannan son zan iya mutuwa domin ke ki rayu, kai bama ke ba zan iya bada raina akan wani naki, shine k’ololuwar son da zan nuna miki wanda na tabbatar da ko bana raye sai kin tuna dani, zaiyi wuya ma ki iya mantawa dani, raina fansa ne a gareki Afnan, Afnan wallahi Allah idan na rasaki mutuwa zanyi, dan Allah kiji tausayina ki rik’e amana.”_

 

*AFNAN* _”Affan ina k’aunarka da zuciya d’aya ne, kuma nai maka alk’awari wallahi duk wuya duk dad’i muna tare, bazan tab’a guje maka ba, kaima shaida ne akan irin k’aunar da nake maka, dan haka karka damu kai kad’aine a raina, akoda yaushe amanarka itace abar tattalina, kuma na tabbatar k’aunar da nake maka ta zarce wadda kakemin._”

 

*AFFAN* _”Haaaaa yarinya kibar wannan tatsuniyar, ko a ma’auni aka auna soyayyata da taki sai anga tawa ta rinjayi taki sau ba adadi ta buga taki da k’asa.”_

 

Afnan tai dariya, tana k’ok’arin tura mishi da amsa taga wani sak’on nashi ya k’ara shigowa.

 

*AFFAN* _”yauwa na tuna, a cikin labarinki kin fad’amin ke ‘yar Legos ce, acan kuke da zama, amma nasha mamaki da kika kasa sanar dani unguwarku, bayan kuma ni hatta sunan da ake gane gidanmu dashi a gyallesu saida na fad’a miki, meyasa kika b’oyemin, kuma meyasa bakyaso inzo wajenki, a tunanina zakifi kowa zumud’in ganinmu a tare kusa da juna, malama ki bani dama wallahi ko ki ganni kwatsam nazo dan ni ina yin zuwa d’aya zan sanar zan turo iyayena a saka mana ranar aure.”_

 

*AFNAN* _”Haba Affan yaushe zargi da rashin yarda ya fara shiga tsakaninmu da kai har haka? wallahi lokacin da na baka labarina kasan dare yayi ina jin bacci, kuma kasan akwai mantuwa, duk a tunanina na fad’a maka, be kamata kayi saurin zargina ba, maganar zuwa wajena kuma nace ne kayi hak’uri har mu k’arasa karatu in dawo gida, kaga a gida zanfi yi maka tarba me kyau, kuma kaga kaima kana so ka gana da mahaifina kuyi magana akan turo da magabatanka, to wad’anan dalilan ne sukasa nace ka bari sai na koma gida, kuma kaima banda abinka saura fa wata d’aya mu koma gida gabad’aya, amma adress d’in gidanmu yanzu zan fad’a maka.”_

 

*AFFAN* _”Eh gaskiya kin fini gaskiya da hujja gwanata, kiyi hak’uri kinji kar ranki ya b’aci.”_

 

Nan ta tura mishi adreshinta, yai mata godiya sannan sukayi sallama domin ta fara jin bacci, shi in dan ta tashi ne be k’i a kwana ana hira ba.

 

Kullum cikin yi masa kalamai take, tareda tura mishi hotunanta rututu, Affan akan screen d’in wayarshi hotonta ne, cikin whatsapp d’inshi hotonta ne, kai ko a ina acikin wayarshi in ka duba hotonta ne, yanda yake b’ata lokaci a wajen kallon hotonta baya b’atawa a kowane waje haka, in sukai chat kuwa sai ya karanta sau ba adadi, shiyasa sau tari in yana zaune ya tuno da wata hirarda sukai sai yahau dariya shi kad’ai, in ka ganshi shi kad’ai, kai ko a cikin mutane ne in yai shiru to tunaninta yake, gashi ya zama masifaffe a wajen k’anninshi, basa shan masifarshi sai ranarda suka samu matsala da Afnan ko kuma bata da lafiya, to a ranar damuwarshi da b’acin ransa sai ya shafi kowa.

 

Haka Afnan ta cigaba da tatsar Affan hatta kati shi yake tura mata kuma baya tura mata na k’asa da na dubu d’aya da d’ari biyar, ta maida shi tamkar wani A.T.M d’inta.

 

*BAYAN WATA BIYAR*

A lokacin watan su Afnan hud’u kenan da dawowa gida, sun gama karatu tare da fito da kyakkyawan result.

 

Kuma har zuwa wannan lokacin tak’i ta bawa Affan dama ya je inda take domin ya ganta.

 

Komai ya canzawa Affan, komai nashi ya k’are, hatta kayan dake cikin shago babu su a yanzu Afnan ta cinye jari da uwar kud’in, duk yabi ya damu, kuma damuwar tashi guda d’ayace, itace taya zai samu kud’inda zai bawa Afnan kafin ta tambaya, be tab’a nadama da danasanin kud’in da yake kashe mata ba.

 

Zaune yake a d’aki ya zuba uban tagumi, tunanin mafita kawai yakeyi, ga k’annenshi an korosu kud’in makaranta, gashi babu kud’i a hanunshi, babu kuma inda yake tunanin samu saboda shago ba kaya kuma baya bin bashi, inda Allah ya taimakeshi ma akwai kayan abinci him daya siya da yawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button