HAUSA NOVELNa Baki Rayuwa Ta

Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

 

Wayarshi ya jawo ya kira Adnan, tunda sukai fad’a sai yau ya tuna dashi duk irin shak’uwar dake tsakaninsu, Adnan na d’agawa ko gaisawa basuyi ba yace “manyan k’asa ya kake?”

 

Affan yace “ka manta dani Adnan,” Adnan yai murmushi, sannan yace “a’a ban manta dakai ba kana raina, kawai dai na barka ne ka huce daga fushin da kayi dani tukun,” Affan yace “dan Allah ka manta da wannan abokina, shawara nakeso ka bani, ina cikin damuwane wallahi.”

 

Adnan yace “meke faruwa kuma?” Affan yace “kaidai ka bari kawai, wallahi komai ya tsayamin cak, ba kud’i ba kayan shago ga karatun yara ya tsaya shima an korosu daga makaranta, na rasa yanda zanyi, babban damuwata budurwata in ta buk’aci wani abu bandashi bansan ya zanyi ba, shiyasa nake neman mafita kafin ta nema.”

 

Adnan yace “yanzu saboda Allah Affan dama bakayi aiki da shawarar da na baka ba akan ka rabu da yarinyar nan, koda yake yanda ka yimin a ranar dama ya nunamin baka d’auki shawarata ba, gashi ankai matakin da nake gudun akai, ita dama dan kud’inka take sonka kenan kome da har zaka damu akan idan ta nema baka bata ba, kamata yayi ace kafi fifita damuwarka akan karatun k’annenka ba akan wata can budurwa ba wadda baka da tabbas akanta” Affan cikin b’acin rai muryarshi na rawa da alamu kuka yake yi, yace “saurara Adnan, wallahi Allah Adnan har cikin raina nake jin rad’ad’in abubuwan da kake fad’a akan yarinyar da nake so, sosai nake jin zafin fa, dan Allah na rok’eka ka daina, ka taimakamin da shawara kawai idan kanada ita, in bakada ita kuma to ka fad’a min.”

 

Adnan yai shiru yana tunani, gaskiya abokinshi yana cikin wani hali, Adnan ya fad’a a fili yace “Affan gaskiya kana buk’atar addu’a ka dage da addu’a nima zan tayaka, bayan haka game da shawarar da ka nema a wajena, akwai kud’i anan wajena amma ba yawa iya na makarantar tasu kawai za’a samu, zan turo maka ka biya musu kud’in makarantar, game da maganar budurwarka kuma karka damu saura sati d’aya in kammala karatuna gabad’aya in dawo gida,” nan dai Affan yai mishi godiya, suna gama waya kuwa Adnan ya turo mishi da kud’in a account d’inshi, ya sake kira yai mishi godiya, sannan ya samu yaje ya ciro washe gari ya tafi tare da yaran ya biya musu kud’in makaranta, bayan ya dawo gida ragowar ya bawa Innarsa ta rik’e a hannunta.

 

Har ya juyo zai fita ya koma d’akinsa sai Inna tace “Affan,” yace “na’am Inna,” Inna tace “dawo ka zauna muyi magana,” Affan ya dawo jiki ba k’wari kuma a sanyaye ya zauna.

 

Inna ta kalleshi tace “Affan meyasa ka daina fita wajen aiki, kuma ina mashin d’inka?”

 

Karo na farko kenan da Affan ya shararawa mahaifiyarshi k’arya, hawaye na fitowa a idanunshi yace “Inna babu kaya a shagon, b’arayi sun yashe shaguna wajen biyar ciki harda namu Inna komai basu bari ba, na b’oye miki ne dan karki shiga damuwa, mashin d’ina kuma na siyar da kud’in ne nake baku kuna cefane.

 

Inna ta shiga tashin hankali amma sam a fuska bata nuna ba, sai ta danne domin kwantar mishi da hankali, tace “yanzu akan wannan ne dama kwana biyu duk ka fita kamanninka ka shiga damuwa Affan, shin ka manta wanda ya bamu wad’anda aka sacen ne, Allah zai sake mayar mana da wad’anda suka fisu, saboda haka in har kana k’aunar farin cikina to karka sake in k’ara ganin damuwa akan fuskarka kaji ko?” Affan yace “naji Inna kuma insha Allah zanyi yanda kikace,” Inna tace “yauwa Allah yai maka albarka, yanzu tunda babu aikin kaje ka kwanta ka huta, kaga wad’annan kud’in da ka bani zasu isa inyi kwana biyu ina manajawa,” Affan yace mata to, sannan ya fice daga d’akin, Inna ta bishi da kallo har ya fita tausayinshi takeji sosai, sai a lokacin ne hawayen da taketa b’oyewa suka zubo kan fuskarta, mutuwa kenan me tonon silili, faruwar wannan lamarin ne yasa ta tuno da mijinta, saida taci kukanta, shigowar yara yasa ta dakata da yin kukan, dawowansu kenan daga makaranta.

 

Page 20 to 25

Bayan kwana biyu da yin wayar su Adnan da Affan, ya kama saura kwana biyar kenan Adnan ya dawo gida.

 

Kuma tun daga ranar be sake samun wayar Afnan ba

 

A cikin kwanaki biyun nan kuwa Affan ya rame ya fita hayyacinshi gabad’aya sakamakon wayar Afnan da ya daina samu duk idan ya kirata abu d’ayane kunnuwansa suke sauraro shine wayarta tana kashe.

 

Duk yabi ya damu, tunaninshi kawai a wane hali take ciki, yasan Afnan bata tab’a yi mishi haka ba sai lokacin da aka sace wayarta, sai kuma wannan lokacin da yanzu yake nemanta baya samu.

 

_So kenan me maida jarumi ya zama rago, a duk lokacin da k’auna ta kama zuciyar bawa beda wani zab’i nashi sai abinda zuciyarshi ta zab’ar mishi me kyau ko mara kyau, kuma duk yanda yaso ya kaucewa faruwar hakan baya iyawa dole sai ya aikata koda zai cutar dashi a gaba, so makantar da zuciya takeyi ta yanda baka iya gane daidai da rashinsa, sedai in Allah yasa kayi dace da masoyi na gari shine zai rik’a d’oraka akan hanya idan kayi abu wanda ba daidai ba, fatanmu shine Allah ya had’amu da nagartattun masoya, wanda zasu k’aunacemu domin Allah kuma soyayyar tasu tayi sanadin samar mana da cigaba me kyau a rayuwa ameen._

 

Affan fa ya shiga damuwa matsananci bashida wani aiki sai kallon hotunanta a waya, sai kuma bitar chat d’insu, babu abinda ke tayar dashi daga aikata abu biyun nan sai sallah kad’ai.

 

Abu fa yai k’amari har takai ga fara tab’a lafiyarshi, ciwon kai matsananci ga kuma zazzab’i.

 

Wasa wasa yau kusan kwana hud’u kenan baya samun wayar Afnan, ta kama saura kwana uku Adnan ya dawo A lokacin kuma zazzab’in yayi sauk’i sedai damuwa da kuma rashin k’arfin jiki.

 

Ganin wannan tunanin nashi ba shine mafita ba yasa ya fara tunanin mafita cikin ranshi.

 

Shawarar da ya yanke itace ta sashi cikin farin ciki mara misaltuwa a cikin k’ank’anin lokaci, ya yanke shawara ne akan zai bi Afnan garinsu kawai tunda yasan gidan.

 

Sedai yasan Inna bazata barshi ba idan tasan gaskiyar lamari, shi yama fara ya fad’a mata gaskiya, tunanin k’aryar da zai shirgowa Inna ta yarda da tafiyar nan yake.

 

Yana cikin wannan tunanin ne ya tuna ashema bashida kud’i tayaya zaiyi tafiya bashida ko nera biyar.

 

A tak’aice saida ya wuni yana tunanin mafita, har ya fara sarewa can sai Allah ya kawo mishi mafita, tashi yayi cikin sauri ya nufi d’akin Inna, tarar da ita yayi tana sallar magrib, sai a lokacin ne ma ya tuna cewa ko sallar la’asar beyi ba.

 

Fita yayi daga d’akin yaje ya d’auki buta yai alwala ya tafi masallaci yai sallah.

 

Bayan ya idar yana dawowa kai tsaye d’akin Innarsa ya shiga bakinshi d’auke da sallama, Inna ta amsa mishi, bayan ya gaisheta tace “ya jikin naka Affan?” Affan yace “da sauk’i Inna,” Inna tace “to Allah ya d’orar maka da lafiya,” Affan yace “ameen ya rabbi Inna.”

 

Shiru ne ya biyo baya na ‘yan wasu mintuna sannan Inna ta kalleshi tace “Affan ya akai me kake son fad’ane kuma kayi shiru?”

 

Affan yace “Inna wata shawara na yanke shine nazo mu tattauna akanta, in tayi kin amince da ita to, inma batayi ba shikenan sai a barta.”

 

Inna ta gyara zama sosai tare da k’ara maida hankalinta gareshi, tace “to ina saurarenka Affan.”

 

Affan yace “dama wani abokina ne wanda mukai karatu tare a makaranta ya bani shawarar inje garinsu muyi kasuwanci tare, shine naga da inta zama a gida gwara inje d’in, amma sai abinda kikace.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button