HAUSA NOVELNa Baki Rayuwa Ta

Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

 

Inna tace “to shi abokin naka a wane gari yake, kuma da wane kud’in zakai kasuwanci Affan?”

 

Affan yace “a garin legos yake, kuma………..” Inna ta katse mishi maganarshi cikin hanzari tace “legos Affan, yanzu duk fad’in garin nan da sauran garuruwa ka rasa inda zaka tafi neman kud’i sai legos, garinda akace ana yawan kashe kashe.”

 

Affan yai murmushi, sannan yace “Inna wallahi wasu abubuwan duk canfin mutane ne, wasu abubuwan da kikeji ana fad’i akan wasu garuruwan duk ba gaskiya bane, lafiya lau suke zaune a ciki.”

 

Da Inna taga taja Affan yaja sai tace “to idan na amince maka ka tafi da wane kud’in zakaje yin kasuwancin?”

 

Affan yace “shine ai nace me zai hana mu bada hayan shagonmu ga wani tunda ba amfani mukeyi dashi ba da yaita zama ba komai a ciki, in yaso kud’in dama ba ni zan tafi dasu ba, ku zan bar mawa na mota kad’ai zan d’auka sai in bar muku sauran kud’in kiyi amfani dasu kafin in dawo.”

 

Inna tace “yanzu kai bayani yanda zan fahimta, cemin zakai aiki zakaje nema bawai kasuwanci ba”

 

Affan yai murmushi sannan yace “akwai aikin ma wanda abokina sukeyi, nima shi zanyi,” Inna tace “to wane irin aikine, Affan yace “ban tambayeshi ba Inna, amma in har naje naga aikin beyi ba zan dawo kawai,” Inna tace “to Affan tunda ka dage ni bazan hanaka tafiya ba nasan duk inda kake addu’ata tana tare dakai, amma zamuji kad’aici tunda mun saba ganinka koda yaushe, yanzu yaushe ne tafiyar?”

 

Affan yace “dama akwai wani wanda ya nuna yana son hayar shagonmu to na bari ne sai nayi magana dake in tuntub’eshi, kuma idan na tafi bawai zan dad’e bane, zanje inga irin yanayin aikin ne idan yayimin sai in dawo inyi shirin tafiya, to idan ya bada kud’i a gobe to a goben nakeso in tafi.”

 

Inna tace “haba dai, ai ka bari sai nan da jibi ko nan da kwana uku ma, kaga lokacin ka k’ara samun sauk’i, kuma wai kama manta ne saura kwana uku Adnan ya dawo?”

 

Affan yai shiru yana tunani, baya son ya dage a gobe zai tafi ta ganoshi amma shi da da hali bayaso ya wuce gobe ya tafi wajen masoyiyarsa, hakan yasa yace mata “to Inna idan yaban kud’in gobe sai in bari sai nan da kwana ukun na ma fi shiryawa a tsanake, maganar zuwan Adnan kuma na sani ban manta ba, kuma shima ya san da tafiyata.”

 

A wannan ranar bayan Affan ya gama samun amincewar Inna, a ranar yaje ya bada hayar shagonsu, kuma a ranar ya zab’o had’ad’d’un kayan da zaisa ya tafi dasu, a ranar ya gama duk wani shiri nashi, zagayowar ranar tafiyar kawai yake jira.”

 

A safiyar ranar da Adnan zai dawo a ranar Affan ya d’auki hanyar legos bayan sunyi kyakkyawar sallama da k’annensa da kuma Innarsa ta yi mishi addu’o’i.

 

A cikin kud’in nan na mota kad’ai ya d’auka wanda zai isheshi zuwa da dawowa, saboda halin rayuwa.

 

Yana zuwa tasha cikin ikon Allah ya sami mota ta kusa cika, yana shiga saura mutum d’aya, kuma be dad’e da zama ba aka samu wani shima zaije legos d’in, kuma saurayine shima kamarshi, a gaba suka zauna shi da wannan saurayin, cikin k’ank’anin lokaci aka had’a kud’i mota ta tashi.

 

Tunda wannan saurayin ya shiga cikin wannan motar ya damesu da surutu, Affan kuwa sai faman neman lambar Afnan yake amma har zuwa lokacin bata tafiya.

 

Wannan saurayin ya kalli Affan yace “kaima cikin garin legos d’in zaka sauka?”

 

Affan yace “eh” ya sake ce mishi wace unguwa zakaje a legos?” Affan ya fad’a mishi sunan unguwar a tak’aice, ga dukkan alamu yanda Affan ya nuna ya dameshi, shi kuma a yanzu sam ya tsani hayaniya ko yaya take, saurayin nan yace shikenan fad’uwa tazo daidai da zama ai unguwar da zaka nima can na nufa kaga kenan tafiyarmu d’aya dakai, Affan ya sauke wani numfashi na jin dad’i, a cikin zuciyarshi yake cewa ashe kulaka yai amfani har da ina shirin in shareka.

 

Affan yai murmushi sannan yace “naji dad’in haka wallahi domin ni ban tab’a zuwa legos ba tunda nake, kaga sai ka taimakamin.”

Saurayin nan yace “ya sunan gidan da zakaje?”

Affan yace “gidan su Afnan zanje tace gidansu fitacce ne ba b’oyayye bane,” caraf saurayin nan yace kar dai d’iyar Alhaji Bukar?”

 

Affan cikin sauri da jin dad’i matsananci yace “itace wallahi, gidan zanje,” wannan saurayin yace ai unguwarmu d’aya dasu,” nan fa ya fara kallonshi tun daga sama har k’asa tareda jero mishi tambayoyi na ba gaira ba dalili, tun Affan na amsawa har yayi kamar yana bacci sannan ya samu lafiya sai ya koma kan driver da surutunsa, da yake drivern irinshi ne ya biye mishi sunata hira Affan yana jinsu.

 

*BAYAN AWANNI*

Adnan ne ya kwad’a sallama cikin gidan su Affan, bayanshi almajirai ne suna rik’e da kaya nik’i nik’i, Inna ta fito tana fad’in “lale marhabin da bak’in ‘yan makaranta, yanzu kake tafe kenan?”

 

Adnan yace “a’a Inna, wallahi tun jiya na dawo nace zan yi muku zuwan bazata, musamman mutumina dan munyi dashi sai yaune zan dawo, nan ta shimfid’a mishi tabarma tare da kawo mishi abinci da ruwa, Adnan ya sallami almajiran da suka shigo da kayayyakin nan, ruwa kawai Adnan yasha yace ya k’oshi, bayan sun gaisa Adnan yace ina abokina ne banji motsinshi ba?”

 

Inna tace “abokinka ai ya dad’e da d’aukar hanyar legos, sedai mu bishi da addu’ar Allah ya saukesu lafiya.

 

To da yake Adnan yanada labarin Afnan, kuma har garinda take Affan be b’oye mishi ba hakan yasa Adnan ya mik’e tsaye cikin sauri tare da zabga wani uban salati yace “Inna meyasa kika barshi ya tafi?”

 

Page 25 to 30

Inna tabi Adnan da kallon mamaki tace “meyasa kace haka Affan, ko dama baka san da tafiyar bane, ko akwai wani abu da ya sanar dakai ne wanda ni ya b’oyemin naga ka tashi hankalinka akan tafiyar ne har kana cewa meyasa na barshi, kuma ya fad’amin ya sanar dakai komai game da tafiyar, zauna ka sanar dani gaskiyar lamari, meke faruwa?”

 

Adnan yai shiru yana tuno lokacin da Affan ke fad’a mishi cewa ya yi budurwa, yasan Adnan da surutun tsiya shiyasa ya sake tuno lokacin da ya rok’eshi kar ya sanar da Inna sai yaje sun gana da yarinyar sannan shi yasan yanda zai b’ullo mata da maganar, dan idan yace mata ga a inda suka had’u to akwai matsala.

 

Tuno maganganun da sukayi da Affan ne yasa yaga lallai be kamata ya sanar da Inna gaskiyar maganar ba, saboda yanzu yana fad’a mata cewa Affan wajen budurwarshi ya tafi to hankalinta bazai tab’a kwanciya ba.

 

Adnan a sanyaye ya koma ya zauna tare da yin k’ok’ari wajen daidaita natsuwarshi, sannan ya kalli Inna yace “haba Inna wannan tambayoyi haka wacce zan fara amsawa.”

 

Inna tace “to ai kai na fara ganin tashin hankali a wajenka daga cewa abokinka ya tafi legos, kuma naji kace wai meyasa na barshi ya tafi, kodai akwai abinda kuke shiryawa ne wanda ban saniba?”

 

Adnan yai murmushi, sannan yace “eh abinda yasa nace haka saboda naso idan nazo mu tafi tare ne, nafi so muje tare hankalina zaifi kwanciya shiyasa kikaji nace haka, bawai ina nufin wani abu bane.”

 

Inna tai dariya, sannan tace “wo d’an nema wato k’afarka k’afarshi ko, wato duk tsawon shekarunda kuka d’auka bakwa tare shak’uwar tana nan, kar kaji komai, ai ko yanzu kamar kuna tare ne muddin kana yi mishi addu’ar yaje lafiya ya dawo lafiya, Allah ya bar muku zumuncinku har ‘ya’ya da jikoki kai harma k’arshen rayuwa.”

 

Adnan yace “hakane Inna, barima in kirashi inji suna daidai ina yanzu,” Inna tace “yauwa kirawo mana shi.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button